GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Sunday 20 May 2012

TAMBAYA TA DARI BIYU DA ARBA'IN DA DAYA (241) ZUWA TA DARI BIYU DA SITTIN (260)

241. TAMBAYA

YAUSHE AKE FITA DAGA I'ITIKAFI

 

Assalamu Alaikum. Malam inaso a fada min mafi rinjayan zance game da lokacin fita daga I'itikafi?

Amsa

Wa'alaikumus salam,

To dan'uwa malamai suna da ra'ayoyi biyu akan wannan mas'alar :

1. Fita  daga I'iitikafi daga zarar an ga watan Ramadhna,  wato bayan rana ta fadi a daren  Idi, saboda  I'itikafi ana  yinsa ne a Ramadhana kuma idan  an ga wata Ramadhana ya  kare.

2. Mai I'itikafi zai iya zama har zuwa lokacin sallar Idi, ta yadda zai fita bayan kammala sallar, Imamu  Asshafi'i yana cewa: "Duk wanda ya yi niyyar koyi da Annabi S.A.W. to  ya  fita daga I'itikafi bayan rana ta fadi in an ga wata, watan ya yi nusan ko ya cika, amma in ya zauna zuwa sallar idi, hakan shi ne yafi"  Imamu Malik yana cewa: "Na samu labarin wasu daga cikin mutanan kirki suna fita daga I'itikafi bayan sallar idi"

Zance mafi inganci shi  ne fita daga I'itikafi bayan ranar daren idi ta fadi, saboda Annabi S. A. W. yana I'itikafin dararen goman karshe ne, su kuma suna fita idan daren IDI ya shiga.

Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy 6/323 da kuma FaTaawa Allajnah Adda'imah 15/411

Allah ne mafi  sani

24/06/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

242. TAMBAYA

YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU!

 

 Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Ta  saku mana,  saboda rubutu

yana  daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. w.  yana cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya  a zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata.

Hadisin da ya  gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa rubutu aiki NE,  shi kuma  ya yi aiki.

Yana daga cikin Ka'idojin Shariar da malamai fada a littattafan fiqhu:الكتاب كا الخطاب Rubutu kamar magana NE.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

24/06/2017

 

243. TAMBAYA

WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN  DA SUKA SHAFI RANAR  IDI

 

Assalamu Alaikum,

Malam ina so sanin hukunce-hukuncen idi

 

Amsa

Wa'alaikumus salam.

Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga ciki:

1. Azumtar  ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry,  -Allah ya yarda da shi -  cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi  ya hana azumtar  ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito

2. Siffar sallar idi- An karbo daga  Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa : "Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya kasance yana fita ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana farawa da sallah"  Bukari ne ya rawaito

Ana yin ta ne raka'o'i  biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud

Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na kabbarori, saboda  sunnoni ne ba  wajibai ba.

Dr. Jamilu Zarewa

7/8/2013

 

244. TAMBAYA

SHIN ZAN IYA SAKIN AMARYATA DOMIN NA TARA DA ITA SAI NA GANE BABU BUDURCI A TARE DA ITA?

 

Assalamu alaikum malam amincin Allah ya kara tabbata ga malam tareda karin kariya har abada amin.

Tambayata itace: Shin mutum nada hakkin sakin matarsa (Amarya) wacce ya aura ya tara da ita yagane cewa ba budurwabace akwai wani abu daya faru kafin tashigo gidansa. Zai iya sakinta?

 

Amsa

Wa'alaykumussalam

Wannan na daga cikin shubuhohin aure wanda zargi ke kawo haka baya da tabbacin wani abu ya faru kafin ya aure ta, kuma koma wani abun ya faru ai tuba na kankare komai don haka yayi hakuri a cigaba da zama da matar sa, domin bincike ya nuna akwai hanyoyin da mace ka iya saryantar da budurcin ta koda bata sadu da wani da namiji ba...

Don haka ya zauna da matar sa ya rike ta bisa amana.

Wallahu A'alam

Amsawa

Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed

28/06/2017

 

245. TAMBAYA

NA HAIHU JINI YA WUCE KWANA 40, YAUSHE NE HAILA ZA TA IYA ZUWA MUN?

 

Assalamu Alykum malam tambayata anan itace don Allah malam tsawon kwana kin jinin biki ance kwana 40 ne to jini bai dauke ba sainayi wanka a 40 din abin tambaya ta anan shine bayan kwana 40 kwana nawane haila zata iya zuwa ma mutum don saboda bayan kwana 2 da arba'in wani jnin ya zo Wanda nidai ba kalar jinin haila bane kuma Yana.zuba sosai kamar.jini idan mutum ya.yanke yaji ciwo to Sai naci gaba da sallah da sauran ibada shin yaya matsayin haka.da nayi  don Allah malam a amsa min tambayarnan don insan miye nagode.

 

Amsa:

Wa rahmatullahi wa barakaatuhu, To, Lallai 'Yar'uwa, duk da cewa Malamai sunyi sabani game da adadin yawan kwanakin jinin Biki, amma dai magana mafi karfin da ladili itace jinin Biki baya wuce kwana arba'in (40), kuma itace maganar mafi yawancin Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka biyo bayansu, sai dai idan jinin Biki ya wuce kwana arba'in (40) bai daukeba to, sai ki lura idan lokacin yayi dai-dai da lokacin da kika saba yin Haila ne to, Hailarki ce ta dawo, domin mafi yawanci jinin Haila yakan dawoma macen da ta haihu ne a karshen sati na shida bayan haihuwa, idan kuma baiyi dai-dai da lokacin Hailarkiba, to, ya zama jinin ciwo (Istihadah), sai kiyi wanka kicigaba da Sallah da sauran aiyukan Ibada, sai dai duk lokacin da zakiyi Sallah sai kinyi tsarki kin sake alwala.

A duba littafin Almugnee na Ibn Qudaamah, ko Tadauwurul Janeen, ko Diraasah anil Haidi wan Nifaas, ko fatawar Al-Lajnah Al- Daa'imah, mai lamba ta 3923 dan samun karin bayani.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Malam Ibrahim Jushi, Zamfara

08/06/2017.

 

246. TAMBAYA

Assalamu alaikum, dafatan Dr. Yana lafiya. Dan Allah ya rabo gadon nan yake? Mace ce ta mutu bata da miji bata da dan uwa bata da uba, sai yar ta mace guda daya, sai kuma jikoki guda hudu mata, sai kannen ta maza su hudu wanda suke uba daya, da kuma kanne maza uku da suke uwa daya. Shin jikokin ta da kannen suna da gado?

 

Amsa

Wa alaikum assalamu,

 Za'a raba abin da ta bari kashi shida, a bawa 'yarta kashi uku, 'yan'uwanta da suka hada uwa kashi biyu, wadanda suka hada uba sai a ba su ragowar kashi Dayan.

Jikokin da suka fito ta bangaren mace ba za su yi gado a nan ba.

Allah ne mafi sani

1/07/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

247. TAMBAYA

HUKUNCIN ZUBAN JINI KO DAUKEWAN SHI SANADIYAR SHAN MAGANI

 

Assalamu alaikum, Menene hukuncin jinin da ya samu mace ta hanyar rashin shan maganin planing da ake sha wadda da zata tsallake kwana biyu bata sha ba jini zai zo mata amma data ci gaba da sha zai dauke shi ne nike son in san hukuncin shi.

 

Amsa:

Wa alaikumus Salaam, Lallai jinin da yake zo ma  Mace sanadiyyar amfani da hanyoyin kayyade Iyali (Planning) shi ne asalin jinin Haila, dan haka a duk lokacin da mace ta yi amfani da wata hanya ta kayyade Iyali  (planing) ta hanyar fitar da jini ko hana jinin fita, to babban abin da za ta lura da shi, shi ne, duk lokacin da jinin ya fito, hukuncin Haila ya hau kanta, ko da ba lokacin da ta saba haila ba ne in dai jinin ya zo to, hukuncin Haila ya tabbata a kanta.

Amma idan maganin ya hana jinin fita ne to, hukuncinta hukuncin mace mai tsarki ko da lokacin da ta saba Haila ne in dai jini bai zo ba to, babu hukuncin Jini a kanta domin hukuncin jini ba ya tabbata sai lokacin da jinin ya fito.

 Allah Ya bamu ikon ganewa da gyarawa.

Amsawa:

Malam Ibrahim Jushi, Zamfara

01/07/2017.

 

 

248. TAMBAYA

HAILA YA ZO MATA GA SHI BATA DA LAFIYA BA ZA TA IYA TABA RUWA BA; YA ZA TA YI

 

Assalamu alaikum, Mal. Mace ce ta gama haila amma a lokacin bata da lafiya kuma in har ta sa ruwa akanta akwai matsala, Yaya ya kamata ta yi?.

 

Amsa:

Wa rahmatullahi wa barakaatuhu,  Idan jinin Haila ko na Biki ya dauke ma mace a lokacin da take cikin uzurin da ya hana ta amfani da ruwa to, za ta jinkirta wanka sai uzurin da ya hana ta wanka ya gushe, sai dai kafin ta yi wankan sai ta rika yin taimama madadin Alwala.

A duba littafin Majmu'ul fatawah na Shaikhul Islam Ibn Taimiya mujalladi na 19, dan samun karin bayani.

 Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Malam Ibrahim Jushi, Zamfara

01/07/2017.

 

249. TAMBAYA

KWANAKI NAWA NE TSAKANIN HAILA ZUWA WATA HAILAR?

 

Assalamu alayk wa Rahmatullah wa Barakatuh. Don Allah kwanaki nawa ne tsakanin haila da wata hailar don yau kwana 13 da na fara haila sai na yi kwana 5 na yi tsarki sai kuma yau gashi ta zo. Allah Ya sa mu dace.

Don Allah ina jiran answer don in san hukuncin da ke kai na. Its urgent pls.

Amsa:

To, 'Yar uwa, Malaman Musulunci sun hadu akan cewa shari'ar Musulunci ba ta kayyade wasu kwanakin tsawon tazarar Haila zuwa wata Haila ba, amma sun yi sabani game da karancin tazarar kwanakin Haila zuwa wata Hailar. Wasu Malaman sun ce: karancin kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Hailar, sai ya kai kwana goma shabiyar (15), wasu suka ce: kwana goma sha uku (13), wasu sukace kwana goma (10), wasu suka ce: kwana takwas (8) zuwa goma (10), wasu suka ce kwana takwas (8).

Amma magana tabbatacciya ita ce Shari'ar Musulunci ba ta kayyade karanci ko yawan tazarar kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Haila ba, Mace tana iya yin Haila uku (3) cikin wata guda musamman masu amfani da magani ko allurar tazarar haihuwa, nan da nan sai Haila ta ta zo musu. Sai dai idan Mace ta yi da'awar ta gama idda kasa da lokacin da aka saba gama idda, to sai ta zo da wanda zai shedeta cikin danginta makusanta akan cewa haka hailarta take.

A duba Majmu'ul fatawah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyya Mujalladi na 19, ko littafin Al-Haidu wal Hamdu wannifaas bainal fiqhu waddibu na Umar Sulaimanu Al- Ashqar, dan samun karin bayani.

 Allah ya taimake mu.

Amsawa:

Malam Ibrahim Jushi, Zamfara

04/07/2017.

 

250. TAMBAYA

KWANAKI NAWA NE TSAKANIN HAILA ZUWA WATA HAILAR?

 

Assalamu alayk wa Rahmatullah wa Barakatuh. Don Allah kwanaki nawa ne tsakanin haila da wata hailar don yau kwana 13 da na fara haila sai na yi kwana 5 na yi tsarki sai kuma yau gashi ta zo. Allah Ya sa mu dace.

Don Allah ina jiran answer don in san hukuncin da ke kai na. Its urgent pls.

 

Amsa:

To, 'Yar uwa, Malaman Musulunci sun hadu akan cewa shari'ar Musulunci ba ta kayyade wasu kwanakin tsawon tazarar Haila zuwa wata Haila ba, amma sun yi sabani game da karancin tazarar kwanakin Haila zuwa wata Hailar. Wasu Malaman sun ce: karancin kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Hailar, sai ya kai kwana goma shabiyar (15), wasu suka ce: kwana goma sha uku (13), wasu sukace kwana goma (10), wasu suka ce: kwana takwas (8) zuwa goma (10), wasu suka ce kwana takwas (8).

Amma magana tabbatacciya ita ce Shari'ar Musulunci ba ta kayyade karanci ko yawan tazarar kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Haila ba, Mace tana iya yin Haila uku (3) cikin wata guda musamman masu amfani da magani ko allurar tazarar haihuwa, nan da nan sai Haila ta ta zo musu. Sai dai idan Mace ta yi da'awar ta gama idda kasa da lokacin da aka saba gama idda, to sai ta zo da wanda zai shedeta cikin danginta makusanta akan cewa haka hailarta take.

A duba Majmu'ul fatawah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyya Mujalladi na 19, ko littafin Al-Haidu wal Hamdu wannifaas bainal fiqhu waddibu na Umar Sulaimanu Al- Ashqar, dan samun karin bayani.

 Allah ya taimake mu.

Amsawa:

Malam Ibrahim Jushi, Zamfara

04/07/2017.

 

251. TAMBAYA

HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)?

 

Assalmu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da imani, malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a musulunci

 

Amsa:

Wa alaikum assalam,

To 'yar'uwa  Babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da al'aura har maniyyi ya fito, duk hadisan da suka zo ba su inganta ba.

Saidai wasu malaman sun haramta auran hannu saboda aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan bukatar sha'awa ta hanyar matar aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan bukata ta hanyar su.

 Yin wasa da al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin ka'idojin shari'a ; idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda za'a yi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka  halatta auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.

Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai barnar dake cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi 'ya'ya gantalallu, marasa asali, wannan ya sa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu sharudan da suka gabata.

Don  neman Karin bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu'ul fataawaa 34\146>

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

23\1\2016

 

252. TAMBAYA

HUKUNCIN MIJIN DA MATARSA TA NEME SHI DA JIMA'I BAI AMSA MATA BA?

 

Assalamu alaikum, malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijin ta shi kuma yaki, shi ma ya aikata zunubi ne ko ko?

 

Amsa

Wa'alaikumussalam,

To dan'uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa 

"Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala'iku za su tsine mata har ta wayi gari"

 kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1436. Saidai abin da malamai suke cewa shi ne :

 Namiji ba shi da laifi, idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za'a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha'awa, namiji kuwa sai yana da sha'awa, zai iya saduwa, don haka akwai bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima'i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya, sannan sha'awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji ne yake neman matarsa ba akasin haka ba.

 Allah ne ma fi sani. 

Dr. Jamilu Zarewa

19\3\2014

 

253. TAMBAYA

NA TUBA DAGA  ZINA, YAYA IDDATA?

 

Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa ne ISTIBRAI din ta?

 

Amsa

Wa'alaikumus salam,

To 'yar'uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi sabani game da iddarta.

1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka.

2. Za ta yi jini daya kawai, saboda fadin Annabi S.a.w. "Ba'a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila daya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.

Don neman Karin bayani duba Almausu'a Alfikhiyya Alkuwaitiyya 30/341.

Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana tabbata da jini daya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina.

Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa

22\2\2016

 

254. TAMBAYA

BA'A YIN GATSE A SAKI!

 

Assalamu Alaiku Tambaya: Dr, mutum ne sukayi fada da kawun matarshi sai kawun matar yace dashi iyakaci dai kace ka saki 'yata, sai shi kuma mijin yace na saketa saki uku, amma matar bata gurin ma'ana bata jiba, sai daga baya ta samu labari, don Allah Dr. Menene matsayin Aurensu? Nagode Allah ya karawa Dr. Lafiya da Imani.

 

Amsa

Wa alaikum assalam, ta saku mana tun da ba'a wasa a saki, mutukar an furta ai kalmar ta zartu

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

11/12/2016

 

255. TAMBAYA

MENENE MATSAYIN ADDU'AR MAWAKA A CIKIN WAKENSU..?        

 

Assslam alaika Allah ya karawa Dr lafiya mallam mene matsayin addu'ar da mawaka suke a cikin wakensu shin za'a iya amsawa

 

Amsa

Wa'alaikimus salam. To dan uwa da farko dai ita addu'a tana da ladabi da ka'idoji wanda shari'a ta shimfida ayi addu'oin ba dai dai bane mutum yana rokon Allah yana  waka yana kida wannan izgilancine, ya kamata mutane suji tsoron Allah su kiyaye.

Dangane da amsawa kuma Allah madaukakin sarki shine yake amsa addu'a a duk yadda bawa yayi' dayawa akan samu mutum yana cikin sakoma ya roki Allah kuma ya amsa idan yaga dama amma baya daga cikin abinda malamai magada Annabawa suka rubuta a litattafi cewa mutum' yayi addu'a a cikin waka kuma Allah ya karba ya kamata komai mutum zaiyi yayi abinda shari'a ta amince dashi sai dai idanya cika sharudan karbar addu'ar da malamai suka shimfida idan yayi Allah zai karba sai dai kawai za'a kamasa da yayi izgilanci yayi abin bata hanyar daya kamata yayi ba

Allah shine mafi sani

Amsawa

Dr. ABDALLAH GADON KAYA

18/04/2017

 

256. TAMBAYA

WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU!

 

 Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,  ta  saku mana,  saboda rubutu yana  daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W.  yana cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya  a zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata.

Hadisin da ya  gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa rubutu aiki NE,  shi kuma  ya yi aiki.

Yana daga cikin Ka'idojin Shariar da malamai fada a littattafan fiqhu:الكتاب كا الخطاب Rubutu kamar magana NE.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

24/06/2017

 

257. TAMBAYA

ZAN IYA YIN AZUMI UKU KAWAI A MATSAYIN SITTA SHAWWAL?

 

Assalamu alaikum, malam Tambayata shine don Allah Malan mutun ze'iyayin azumin sitta shauwal guda uku?

 

Amsa

Wa'alaikumus salam,

Ba za'a iya a zumtar kwana uku a matsayin sitta shawwal ba, domin manzon Allah cewa yayi kwana shida(6) don haka dole sai kwana shida din.

Wallahu A'alam.

Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

12/07/2017

 

258. TAMBAYA

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE

SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI

DAMAR KOME?

 

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware

mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta,

mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1 ya

koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata

shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan

sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake

rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu

akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren

wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya

kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa

ne yake kanta nagode Allah yakara imani da

basira sai naji daga gareka

 

Amsa :

Wa alaikum assalam  To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke

tsakaninku sun yanke gaba dayansu.

Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a

baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da

ka mata, kafin ka sake auranta, da ba'a kirga da

saki biyun baya ba, amma tun da ba ta aura ba,

ya wajaba ku hakurewa juna .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na

Ibnu-Khudaamah 7\388 .

Allah ne mafi sani.

 Amsawa

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

3\5\2015

 

259. TAMBAYA

NA YI AURE KAFIN NA YI ISTIBRA’I

 

Assalamu alaikum

Ya kamata a ce na yi istibra’i kafin na yi aure,

amma ban yi ba, har na yi aure, yanzu haka ina

jini na farko ban yi tsarki ba, amma ba da wanda

na aikata laifin na yi aure ba. Ya ingancin aure

na? Gani nake kamar babu auren.

 

Amsa

Wa'alaikumus salam,

Toh

farko dai ina miki wasici da tsoron Allah saboda

zunubin da kika aikata, amma game da aure, to

aurenki ya yi, saidai yinsa bayan istibra’i shi ne

ya fi, sannan ya wajaba mutukar kin san kina da

ciki to bai halatta ki bawa sabon mijinki dama ya

take ki ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya yi

imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar

da ruwansa ga shukar waninsa” Abu- dawud :

1847. Don haka ya wajaba a gare ki ki yi stibra’i

kafin mijinki ya sadu da ke, sannan istibra’i jini

daya ne , idan kuma har kin dauki ciki, kafin ki yi

istibra’i, in kin haihu kafin wata shida to ba

dansa ba ne, amma in har kin haihu bayan wata

shida daga fara saduwarku, to dansa ne, mutukar

ba’a samu shaidar da take nuna kina da ciki ba,

tun kafin ku fara saduwa . Don neman Karin

bayani duba : Al-mugni na Ibnu kudaamah 8\79

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

1/12/2016

 

260. TAMBAYA

YAUSHE AKE FITARWA DA GOLD ZAKKA?

 

Assalama Alaikum Warrahmatullah. Malam ya

kokari, Allah ya saka da Alkhairi. Don Allah

Malam ina so in san nisabin zakka na gwal (gold)

nawa yake kaiwa idan za’a cire?.

AMSA

Wa alaikum assalam,

 Ana fitarwa da Goal zakka idan ya kai gram tamanin da biyar (85).

Allah ne mafi sani.

1/08/2017

Dr. Jamilu Zarewa


No comments: