81. TAMABAYA
SHIN AMAI NA KARYA AZUMI?
Assalamu alaykum'm Malam Dan Allah inada
tambaya,nice ina azumi se nayi irin Dan aman nan wanda ake ce masa aman
kaji,Dan kadanne ba wae amai da yawaba,to malam ya matsayin azumi na naji ance
amai yana karya azumi.Allah y qarawa malam Lpy.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Duk aman da akayi kadan ko mai yawa ba da gangan ba toh baya karya azumi amma idan
an kakaro shi ne to azumi ya karye, Don fadar manzon Allah cikin hadisin Abu huraira wanda ke cikin sunan na imam tirmizi 720.Don haka dai babu sabani tsakanin malamai cewa duk
wanda amai ya rinjaye shi toh azumin sa na nan amma wanda ya kago amai da kansa
to azumin sa ya baci, aduba:
Al'Mugni 4/368
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
29/05/2017
82. TAMABAYA
SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU
Assalamu alaikum,
Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan
"KUDRA da kuma SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa, Wannan yana daga cikin mas'aloli masu
mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwka game da haka :
Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi
kamar ruwan ciwo, ya fito daga gabanta.
Kudra kuwa na nufin : ruwa ya ringa fitowa daga
farjin mace, wanda kalarsa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da baki wato
kamar ruwa gurbatacce,
Dangane da hukuncinsu kuwa : idan daya daga
cikinsu ya kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila kafin ta sami
tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan kuma bayan tsarki ne to ba
haila ba ne saboda fadin Ummu adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra
bayan tsarki a cikin haila) Abudawud ya rawaito shi da sanadi mai inganci,
A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin
da suke sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan da yake
kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa
ya fito, ta yadda za mu yi amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki,
ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila ba, hadisin
A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana cikin haila ta yadda za ta kirga
da su.
ALLAH ne mafi sani.
5/12/2014
Dr Jamilu Zarewa
83. TAMABAYA
YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YA YI
KAFFARA?
Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne
ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani
auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.
Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga Malam.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Auransa na biyun ya inganta
saboda ba su da alaka da juna.
Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku
ne, to wancan ziharin ya warware, amma in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai
halatta ya taba ta har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah
ya fada a cikin Al-Mugni.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2017.
84. TAMABAYA
TANA AZUMI SAI MIJINTA YA SUMBACETA?
Malam macece tayi kitso alhalin tana azumi sai
mijinta yaga kitson ya basa sha'awa saiya sumbacesa ita kuma take sha'awa tazo
mata harta jika pant dinta
Wa akaikumus salamTo yar uwa da farko dai anyi
wasa da azumi kwarai da gaske kuma ba daidai bane kina azumi ki bari mijinki ya
sumbaceki ta yadda har zaki fitar da wani abu dazai bata miki azumi' wannan
akwai ganganci a ciki.
Amma shi azumin nafila dama mai shi yanada yan'cin
ya karyashi koya cigaba Annabi S.A.W ya fada cikin hadisi sahihi mai azumin
nafila shine sarkin kansa idan yaga dama ya karya manzon Allah s.a.w. ya bada
wannan damar.
Malamai suna cewa fitar maziyyi idan har maziyyine
ya fita karamar sha'awa kenan zance mafi inganci baya karya azumi amma idan
maniyyi ne ya fita to azumi ya karye shikenan idan na nafila ne bakida lada
idan kuma farilla ne akwai kaffara akansu bisa kaulin malamai amma wasu malaman
sukace sai anyi jama'i kaffara take wajabta idan nafilane shikenan idan kuma na
farillah ne saiki rama guda daya wannan shine zance mafi inganci.
Allah shine mafi sani.
Amsawa
DR. ABDALLAH GADON KAYA
85. TAMABAYA
INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADHANA SAI ALFIJIR
YA KETO!
Assalamu alaikum Malam muna cikin saduwa da mijina
a cikin wannan wata, sai muka ji kiran sallar asalatu, me ye hukuncin azuminmu?
Amsa
Wa alàikum To 'yar'uwa mutukar kuna jin kiran
sallar, kun maza da sauri, kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan,
amma in har kuka ci gaba, da yi ko da na second daya ne, to azuminku ya karye,
kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki ya
yi, to zai yi kaffara shi kadai.
Duba Almugni: 3\65.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
18/06/2015
86. TAMABAYA
SHIN ME NENE ZIHARI?
Assalamu alaykum Warahmatullahi wabarakatuh. Don
Allah Mallam menene ZIHARI? Allah yaqara ilimi mai amfani.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Zihari shi ne mutum ya kamanta matan shi da wata
wanda take muharrama a gare Shi kamar Mahaifiyan sa, kanwar shi ko 'Yar shi da
ya haifa.
Wallahu A'alam
Malam Umar Shehu Zaria
03/03/2017
87. TAMABAYA
Mata ta mutu ta bar:
1- miji
2- 'Ya'ya mata biyu
3- 'yan-uwa li'abbai Maza da mata
4- 'yan-uwa li'ummai Maza da mata.
menene kason kowa
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Za'a raba abin da ta bari gida 12, a bawa mijinta
kashi uku, ' ya'yanta mata kashi takwas,
ragowar kashi dayan sai a bawa'
yan'uwa li'abbai su raba.
Allah ne mafi sani
4/6/2017
Dr Jamilu Zarewa
88. TAMABAYA
ALAMOMIN KARBAR TUBA
Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da
mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya?
Amsa
Wa alaikum assalam.To dan'uwa akwai alamomin da
malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga
ciki :
1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai
kusantar da shi zuwa ga Allah.
2. Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya
ga Allah.
3. Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba
daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .
4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba,
a matsayin ni'ima daga Allah.
5. Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da
kafin ya tuba.
6. Yawan istigfari.
7. Son kusantar salihan bayi.
Allah ne ma fi sani .
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 5/6/2014
89. TAMABAYA
ZAN IYA CIN BASHIN BANKI SABODA ZUWA HAJJI?
Assalamu alaikum, malam don Allah ina da tambaya
kamar haka - ko zan iya cin bashin banki wato loan domin cika kudin kujerar
maka,? Nabiya ma mahaifiyata sabida karin kudin da akayi ya wuce abinda muke
zaton cikawa kuma ni ma'aikaciyar gwamnati ce. Na gode Allah yabada ikon
amsawa. via UMMUHATUL MUMININ.
Amsa
Wa alaikum assalam,
mutukar ba ki da hali to barin zuwa aikin hajjin
shi ne daidai,, saboda Allah ya kwashewa kudin ruwa albarka a cikin suratul
Bakara kuma ya yi shirin fito-na-fiton yaƙi da wanda ya ci riba,, sannan Allah
bai wajabta miki hajji ba ta hanyar bashi,, balle kuma ki biyawa wani.
Hajji yana wajaba ne ga wanda yake da iko da kuma isasheshen guzirin da zai
wadatar da shi daga rokon mutane.
Allah ne mafi sani
5/6/2017
Dr. Jamilu Zarewa
90. TAMABAYA
AL'ADATA TA
RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI ?
Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya,
don Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci. Malam matsala
ta haihuwa greni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar
tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan
sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na
nkeyi nacigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan
Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi
wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yamin
wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama
wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin tawa take.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a cikin
alqur'ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin
ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai
dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi yawan
kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta
yadda ba zai hana sallah da azumi ba.
Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin
Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje
yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a
hadisi mai lamba ta: 4911, saidai
yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al'ada, wannan yasa barin
su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka
gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa.
Allah ne mafi sa ni
Dr. Jamilu Zarewa
22\1\2016
91. TAMABAYA
BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA?
Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji
wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai
idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi
da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Annabi S.
A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi
siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon
shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare. Amma
abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka
sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata
raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai
sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin
Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare
wutiri".
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
07/06/2017.
92. TAMABAYA
AURAN KAFURAI BAYAN SUN MUSULUNTA INGANTACCE NE!!
Assalamu alaykum, Don Allah ina son a tambaya min
malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalansa ta dalili
na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka
tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar
Musulunci ta tsara, sai yace min to yaya matsayin 'ya'yansu? To gaskiya wannan
ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah
yataimaka ameen.
Amsa
Wa alaikum assalam,
To ɗan
uwa, auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi
shi akan ƙa'idoji
da sharuɗan da suka yarda da su na
auratayyarsu, saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka musulunta
ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta
hanyar wancan aure.
Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta
hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu
zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan
da kafurai suka haifa ta hanyar aure za
mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.
In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za a danganta
shi zuwa babansa ba bayan ya musulunta.
Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma
sharhul Mumti'i 12/239.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
07/06/2017.
93. TAMABAYA
SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA, MENENE
SHAWARA
Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu
dace. Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara daya mijina be
kusanceniba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Nagode
Amsa
Wa alaikum assalam
Auranku
ingantacce ne, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da
saduwar ma'aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai
ma'aurata zuwa saɓon Allah. In har ba
ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku
hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da
wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka.
Allah ne mafi sani
08/06/2017
Dr Jamilu Zarewa
94. TAMABAYA
BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI DA MAZIYYI DA KUMA
WADIYYI
1. Maniyyi
Maniyyin
namiji : ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar sha'awa kamar
saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma
warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe kuma
yana yin kamshin kwai.
Maniyyin
mace : ruwa ne tsinkakke, MAI FATSI-FATSI, WANI LOKACIN KUMA YANA ZUWA FARI,
wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan
yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji tsananin sha'awa da
kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko
damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshin kwai, kuma za ta ji
sha'awarta ta yanke bayan fitowarsa.
HUKUNCINSA SHI NE : YANA WAJABTA WANKA
2 Maziyyi :
Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko
kuma tuna wacce kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike
sha'awa, haka nan yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba
ya sa sha'awa ta tafi, kuma wani lokacin ba'a sanin ya fito.
Malamai
suna cewa : Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da maziyyi zai
fitowa namiji azzakarinsa zai mike.
HUKUNCINSA
SHI NE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA
3 Wadiyyi
wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya
ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wadanda suke fama da gwauranci ko
wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.
YANA DAUKAR
DUKA HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI
Allah ne mafi sani.
31/05/2013
Dr. Jamilu Zarewa.
95. TAMABAYA
DAN ACABA ZAI IYA KAI KIRISTA COCI?
Assalamu alaikum, Akramakallahu, Shin ya halatta
MUSULMI DAN ACABA ya dauki KIRISTA ya kai Shi COCI, ko ya dauko Shi daga Coci
zuwa gida? Domin Suna cewa: Mu Sana'a kawai Mu ke yi, haka abin ya ke a
bangaren MAGINA, TELOLI, KAFINTOCI da MA SU WAYARIN da sauran su.
Amsa
To dan uwa Allah Madaukakin Sarki Ya hana
taimakekeniya wajan aikata sabo, kamar yadda aya ta biyu a suratul Ma'ida ta
tabbatar da hakan.
Yana daga cikin sharuddan cinikayya ya zama ta
hanyar da shari'a ta yarda, wannan ya sa kafinta da magini ba za su taimaka
wajan gina inda za a saba wa Allah ba, ko da kuwa za su samu kudi, kamar yadda
bai halatta Tela ya dinka kayan da za a
sanya a coci a kira wanda ba Allah ba.
Duk wanda ya wadatu Allah Zai wadatar da shi,
wanda ya kame Allah Zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da bata karewa.
Don neman Karin bayani duba: Al'umm 4\213. Da kuma
Iktidha'u siradil mustakim 2\41.
Allah ne mafi Sani
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
12\2\2016.
96. TAMABAYA
DAN ACABA ZAI IYA KAI KIRISTA COCI?
Assalamu alaikum, Akramakallahu, Shin ya halatta
MUSULMI DAN ACABA ya dauki KIRISTA ya kai Shi COCI, ko ya dauko Shi daga Coci
zuwa gida? Domin Suna cewa: Mu Sana'a kawai Mu ke yi, haka abin ya ke a
bangaren MAGINA, TELOLI, KAFINTOCI da MA SU WAYARIN da sauran su.
Amsa
To dan uwa Allah Madaukakin Sarki Ya hana
taimakekeniya wajan aikata sabo, kamar yadda aya ta biyu a suratul Ma'ida ta
tabbatar da hakan.
Yana daga cikin sharuddan cinikayya ya zama ta
hanyar da shari'a ta yarda, wannan ya sa kafinta da magini ba za su taimaka
wajan gina inda za a saba wa Allah ba, ko da kuwa za su samu kudi, kamar yadda
bai halatta Tela ya dinka kayan da za a
sanya a coci a kira wanda ba Allah ba.
Duk wanda ya wadatu Allah Zai wadatar da shi,
wanda ya kame Allah Zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da bata karewa.
Don neman Karin bayani duba: Al'umm 4\213. Da kuma
Iktidha'u siradil mustakim 2\41.
Allah ne mafi Sani
Amsawa
D.r Jamilu Yusuf Zarewa
12\2\2016.
97. TAMABAYA
ZAN IYA DORA RIBA, IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU?
Assalamu Alaikum Mallam, dan Allah ina da tmby,
kaman misalin mutum yana baka kudi ka sayo mishi abu, wataran ya baka kudin ka
sayo, wataran kuma sai ka sayo ka kai zai baka kudin, shin koya halasta inci
riba a wanda yaban kudinshi in sayo mai, ko kuwa a wanda na sayo da kudina ne
kawai zan iyacin riba, banda Wanda ya bada kudinshi? Nagode Allah ya kara basira.
Amsa
Allah ya amsa addu'arki 'yar'uwa, idan mutum ya
wakilta ki, ya baki kudi ki sayo masa wani abu, bai halatta ki ci riba da shi
ba, sai da izininsa, saboda hadisin Urwatu Al-ja'ady lokacin da Annabi s.a.w.
ya ba shi dinare (1) don ya sayo masa dabbar layya, sai ya sayo akuyoyi guda
biyu, ya sayar da daya akan dinare daya, ya zo ma da Annabi s.a.w. da akuya
daya da kuma dinaran da ya aike shi, sai Manzon Allah ya amshe ya yi masa
addu'a, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 3642.
Kasancewar Annabi S.a.w. ya tabbatar da shi akan
aikinsa, sai ya nuna hakan shi ne shari'a, don haka idan wakili ya samu ragi ko
ya ci riba a cinikayyar da aka wakilta shi ya wajaba ya dawo da ita zuwa wanda
ya aike shi.
Idan ya wakilta bai bayar da kudi ba, to mutukar
kuna kasuwanci a tsakaninku ya halatta a dora riba, amma in ba kwa yin
kasuwanci ba za ki dora riba ba, za ki kawo masa abin a kudin da ake siyarwa a
kasuwa, saidai in ya bada iznin cin riba, saboda wakili amintacce ne a shari'a,
wasu malaman suna ganin za ki iya dora gwargwadon wahalarki, in bai bada kudi
ba.
Don neman Karin bayani duba Al-mugni na Ibnu
khudaamah 5\86.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
20\1\2016
98. TAMABAYA
ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA MIJINA?
Assalamu'alaikum, Malam don Allah wata ce mijinta
ya ce hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a
musulunci. Shin Malam ya abun yake? Haramun ne, ko kuwa tana iya hudawa tasa
dankunne ta yi kwalliya da shi?.
Amsa
Wa alaikumus Salaam, An tambayi Sheikh Ibnu
Uthaimin akan wannan mas' alar ta huda Hancı sai yake cewa: Huda Hancı zai iya
zama canza halittar Allah, amma idan Garin da matar da ta huda hancin take ana
yın ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi a yi hakan.
Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.
Haka nan an tambayi Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad
akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan
haka.
Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE
ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce, saboda ya
tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye
Kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
4\1\2016.
99. TAMABAYA
ZAN IYA JAN
CARBI, KO KO BIDI'A NE ?
Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa
Malam Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen
ambaton Allah a kowane lokaci. Ina matsayin haka a sharia?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk
da cewa babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da
shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya
kiyaye adadin zikirinsa.
Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda
hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar
yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta:
3486, don haka za su yi maka shaidar
abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.
Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi
amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.
Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda
wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne.
Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama
kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya
inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa
yi da dama shi ne yafi.
Saidai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai
iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya
zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi
da hannu shi ne yafi.
Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul
fataawa 22\187. da Lika'ul maftuh na
Ibnu-uthaimin 3\30.
Allah ne
mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
24\3\2015
100. TAMABAYA
Ya ya wannan rabon gadon yake?
Assalamu alaikum. Allah ya karama dr lafiya.mlm
dan Allah yaya rabin gadon mutumin da ya rasu ya bar 'ya'ya 24 maza 14 amman
daya arnene. Mata 10. da matanshi biyu. dr yaya rabon gadon su yake?? kuma dr
rabon gado dole ne a musulunci
Amsa
Wa alaikum
assalam,
za'a
raba abin da ya bari gida:8, a bawa matansa kashi
daya su raba, ragowar kashi
bakwan Sai a bawa 'ya'yansa (23) su raba, duk
namiji ya dau rabon
mata biyu.
Ba za'a
bawa dansa kafuri ba, Domin Arne ba ya
gadon musulmi saboda hadisin
Annabi S. A. W da ya tabbata
akan haka.
Allah ne
mafi Sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
16/06/2017
No comments:
Post a Comment