161. TAMBAYA
YAYI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YAYI
KAFFARA
Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne
ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani
auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.
Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga
Malam.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Auransa na
biyun ya inganta saboda ba su da alaka da juna.
Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware, amma
in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai halatta ya taba ta har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah ya fada a cikin Al-Mugni.Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2017
162. TAMBAYA
HUKUNCIN DILLANCIN AURE
Assalamu Alaikum,
Malam
menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu
mijin aure?
AMSA
Wa'alaykumussalam,
Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar
da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan
kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake
cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da
zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun yi
sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da yaje neman
aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin
hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a
kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya
baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai
san yanayin matar da zai aura. Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya
fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki
:
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar,
bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta
yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta
ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda
yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton
na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya
wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure,
saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta
auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne mafi sani_
Amsawa
Dr. jamilu zarewa
22/11/2016
163. TAMBAYA
HUKUNCIN JININ BARI
Assalamualaikum,
malam ina da tambaya, Dan Allah idan
mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin
ya zaka na ciwo ko zata daina azumi sallah
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan’uwa wannan jini ba zai hana
sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa bane,
malamai suna cewa : duk cikin da ya zube
kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana
sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne
daga 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka
duk cikin daya zube kafin haka, to jininsa ba
zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma
mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa
ta fara bayyana, to za’a bar sallah da azumi.
Allah ne mafi sani.
30/11/2016
Dr Jamilu Zarewa
164. TAMBAYA
ALAMOMIN KARBAR TUBA
Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da
mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai alamomin da
malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga
ciki
1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai
kusantar da shi zuwa ga Allah.
2.Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya ga
Allah.
3.Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba
daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .
4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba,
a matsayin ni'ima daga Allah.
5.Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da
kafin ya tuba.
6. Yawan istigfari.
7. Son kusantar salihan bayi.
Allah ne ma fi sani .
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
5/6/2014
165. TAMBAYA
TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE?
Assalamu alaikum malam Mace taba da jikinta ga
mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din
nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga
ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba?
Jazakallahu khairaljazaaa.
Amsa :
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da
tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai
halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba
bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska
da wuya da makamacin haka.
Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi
akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya
zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli
sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai
sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don
haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada
garin neman gira a rasa ido.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR.JAMILU YUSUF ZAREWA
4/4/2014
166. TAMBAYA
TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE?
Assalamu alaikum malam Mace taba da jikinta ga
mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din
nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga
ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba?
Jazakallahu khairaljazaaa.
Amsa:
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da
tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai
halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba
bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska
da wuya da makamacin haka.
Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi
akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya
zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli
sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai
sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don
haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada
garin neman gira a rasa ido.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR.JAMILU YUSUF ZAREWA
4/4/2014
167. TAMBAYA
BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?
Assalamu Alaikum.
Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina
hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah
madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo.
Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga
tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata
sabo".
Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida suka
siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.
Allah Ne
mafi Sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
16/08/2016
168. TAMBAYA
HUKUNCIN KARBAR LOAN
Assalamu Alaikum, Malam menene hukunchin karbar
bashi amma na kaya ma'ana kamar (Car loan,) ko nau'insu kamar abinchi, wanda
mutum zai amsa ya biya zuwa wani lokaci, amma kuma farashin yana bambamta da
wanda zai je kasuwa ya bayar da kudinsa ya siya. Shin akwai RIBA a cikin irin
wannan loan din? Koko babu. Allah ya saka da alkhairi.
Amsa:
Wa alaikum assalam
To dan'uwa Mutukar an bayyana masa kudin tun da
farko, to ba riba ba ne ko da ya sabawa farashin kasuwa, domin lokaci yakan yi
tasiri wajan ciniki, saboda in har an biya 'yan kasuwa kudin su cikin lokaci to
za su iya amfana da su, wajan sayo wasu kayan da za su ci riba, don haka
malamai suka yi bayyani cewa hakan ya halatta, idan har an yi sharadi da farko
.
Saidai abin da sharia ta hana shi ne : ayi kari
akan sharadin farko, kamar ya sayar masa da abu naira (10,0000) sai ya zama ya
kasa biya a lokacin da suka yi alkawari,, sai ya kara masa 3,000, akai, wannan
shi ne abin da ya haramta , saboda Annabi s.a.w. ya hana yin ciniki byu cikin
ciniki daya. kamar yadda ya zo a hadisin da Malik ya rawaito a Muwada'a a lamba
ta : 2640
Don neman Karin bayani : duba : Fiqhul muyassar :
shafi na : 219.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
7/4/2014
169. TAMBAYA
HUKUNCIN KARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA
ASSALAMU ALAIKUM, da fatan mallam yana cikin koshi
lfy,. dan ALLAH mal ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi
to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma
wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba
shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin
haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce
iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to
mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba
da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin
haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take
cewa : "Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila.
Bukhari 1\426
ALLAH NE MAFI SANI
Dr. Jamil Zarewa
16/8/2014
170. TAMBAYA
IYA AURAN JIKAR YAYATA?
Assalamu Alaikum, Allah yasa Malam yana cikin
koshin lafiya. Malam Ina neman a warwaremun wata matsala ne, Akwai aure
tsakanina da jikar yayata? Wato dani da kakar yarinyan mahaifinmu daya.
Amsa
Wa alaikum assalam, Babu aure a tsakaninku mutukar mahaifiyarku
daya da kakarta, saboda aya ta (23) a
suratun Nisa'i ta haramta auran 'yar 'yar'uwa wacce kuke uwa daya ko uba daya ko kuma shakikai.
'Yar 'yar'uwa a wannan ayar ta hada da Jikarta da
jikar jikarta har zuwa can kasa kamar yadda malaman Fiqhu su ka yi karin
bayani.
Don neman karin bayani duba babun NIKAH a Fiqhul
Muyassar da tafsiran malamai ga aya ta (23) a Suratun Nisa'i.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
19/08/2017
171. TAMBAYA
NA JONA SALLATA DA TA MAMU,BAYAN AN GAMA
SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?
Assalamu alaikum malam. Shin ya halatta abi wanda
bai samu cikakken jam'i
ba sallah? Misali, na zo masallaci na taradda
jam'i na sallar
asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don
karasa raka'a
2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada
jam'i da ni.
Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya
halatta, tare da
hujjoji.
Amsa
Wa alaikum assalam.To dan'uwa malamai sun yi
sabani akan wannan mas'alar
zuwa zantuka guda biyu:
1. Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan
haramcin
hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba,
sannan kuma
shi masabuki ba liman ba ne, Annabi S.A.W kuma ya
yi umarni
da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa
sallah ta
ki karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in
ya gama
yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka
sai ya
haramta . Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma
Mawahibul-jalil
4\489.
2. Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi
ingancin
zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda
hadisin Ibnu
Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da
daddare sai ya
bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba
ta:666, A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya
halatta
mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa
bai yi
niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi
S.A.W bai hana
Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa
ba su fara da
shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya
rabu da
liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai
ne, don
haka sai ya halatta a bi shi.
Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.
Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu
saboda abin da ya
gabata da kuma hadisan da suke nuna falalar sallar
jam'i.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07/12/2014
172. TAMBAYA
HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN
SALLAR NAFILA
Assalamu alaikum. malam Menene asali ko dalili
idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya dan matsa baya ko gaba
daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?
AMSA:
Wa alaikum assalam To dan'uwa Akwai hadisin da
yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a
sahihinsa, a hadisi mai lamba : 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan
hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178
Saidai malamai suna cewa : ana so ayi hakan saboda
gurare da yawa su yi ma mutum shaida,
Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri,
saboda abin da aka rawaito daga Aliyu - Allah ya kara masa yarda- yana cewa :
"Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar
nafila" wannan yasa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya
yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335
ALLAH NE MAFI SANI
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
22/8/2014
173. TAMBAYA
NA JONA SALLATA DA TA MAMU,BAYAN AN GAMA
SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?
Assalamu alaikum malam. Shin ya halatta abi wanda
bai samu cikakken jam'i
ba sallah? Misali, na zo masallaci na taradda
jam'i na sallar
asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don
karasa raka'a
2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada
jam'i da ni.
Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya
halatta, tare da
hujjoji.
Amsa
Wa alaikum assalam
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan
mas'alar
zuwa zantuka guda biyu:
1. Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan
haramcin
hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba,
sannan kuma
shi masabuki ba liman ba ne, Annabi S.A.W kuma ya
yi umarni
da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa
sallah ta
ki karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in
ya gama
yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka
sai ya
haramta. Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma
Mawahibul-jalil
4\489.
2. Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi
ingancin
zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda
hadisin Ibnu
Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da
daddare sai ya
bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba
ta:666, A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya
halatta
mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa
bai yi
niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi
S.A.W bai hana
Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa
ba su fara da
shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya
rabu da
liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai
ne, don
haka sai ya halatta a bi shi.
Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.
Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu
saboda abin da ya
gabata da kuma hadisan da suke nuna falalar sallar
jam'i.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07/12/2014
174. TAMBAYA
SHIN ZA'A IYA YIWA DAN SHI'A SALLAMA?
Assalamu'alaikum.
warahaamatullahi wabarakatuhu : Malam shin zan iya yiwa dan Shi'a
sallama?
Amsa:
Wa alaikum assalam. To dan'uwa Allah da manzonsa
sun kwadaitar akan sallama saboda kasancewarta tana sanya soyayya a tsakanin
mutane, tana kawo hadin kai tana gusar da kewa, wannan yasa Annabi s.aw. ya yi
umarni da sallama, saboda tana kaiwa zuwa Aljanna, kamar yadda hadisin Tirmizi
mai lamba ta: 599 ya tabbatar da hakan.
Tabbas 'yan shi'a suna da akidu wadanda suke
warware musulunci, Daga ciki akwai zagin sahabban da Allah ya yarda da su, da
riya tawayar qur'anin da Allah ya yi alqawarin kiyaye shi, da siffanta Nana
A'isha da mazinaciya duk da Allah ya kubutar da ita daga can saman saman
bakwai.
Saidai ba
duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za'a kira shi da kafiri ,
dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha
wacce ta kasa warwaruwa.
Yana daga
cikin ka'idoji a wajan malaman Tauhidi ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa
kafiri ba, don haka jahilai a cikin 'yan shi'a da gama-gari wadanda suka shiga
shi'a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirta su
ba,kuma ba za mu ki yi musu sallama ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa
da suka gabata, saboda akwai hadisai da yawa da suke bada uzuri ga wanda ya
aikata kafirci bisa kuskure ko jahilci.
Don haka
duk musulmin da ka san an shigar da shi SHI'A a ba-bai saboda jahilcinsa kana
iya masa sallama, kyakykyawar mu'amala tana iya sanyawa mutum ya gane gaskiya,
kamar yadda hakan ya faru ga mutane da yawa a zamanin annabi S.a.w. da
sahabbansa.
Allah nai mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
17/1/2016
175. TAMBAYA
IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR BAKWAI,
MENENE MAFITA?
Assalamu alaikum.
yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala ya bashi
karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna
Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa
abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu
malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin
bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.
Duk wanda bai samu damar yiwa dansa Akika ba a
kwanakin da aka ambata a sama, to
babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi
duk lokacin da ya samu dama.
AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa
a lokacin da Annabi S. a. w ya ambata,
in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha
1/615.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/08/2017
176. TAMBAYA
AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI?
Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba
mai a motar ma'aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa
na yau da kullum, a ciki?
Amsa:
Wa alaikum assalam
To dan'uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya
ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan
harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta b\a, kamar
yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.
Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: "Ko da
shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da b a huruminsa ba
ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika'u babil maftuh: 238.
Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da
aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da
hakan.
An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul'aziz ba ya
amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi
bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka
shafi jama'a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar
office yana daga cikin tsentseni.
Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi,
wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
25\2\2016
177. TAMBAYA
SANA'A DA WUTAR LANTARKI A GIDAJAN GWAMNATI?
Assalamu alaikum malam. Tare da fatan Allah Ya
karbi ibadun mu da ku Alhazai baki daya.
Malam ina hukunchin wanda suke zaune a gidan
hukuma, kudin wuta da ruwa duk hukuma ke biya. Ya halatta suyi harkan kasuwanchi
da ruwa da wuta, kamar niqa gari, ko yin qanqara suna chin kudin da suka samu.
Ina matsayin wannan a Shari'a?
Amsa
Wa alaikum assalam,
In har a
cikin albashinsa ake dauka babu laifi in ya yi sana'a kamar yadda hakan yake
faruwa a cikin albashinmu na malaman jami'o'i, tun da hakkinsa ne kuma in da ba
ya shan wutar da ba'a cira a albashinsa.
Misali a A. B. U. Zaria hukuma tana cirar min
dubunanai daga Albashina duk wata, saboda wutar lantarkin GIDANA, kin ga babu
laifi in na yi Sana'a da wutar saboda na riga na biya.
Amma idan akwai sharadin da hukuma ta sanya na hana amfani da wutar a wasu
halaye da kuma lokuta ko wasu kayan lantarki saboda kar asha ta wuce ka'ida ko
gudun fadawa hadari ya wajaba a kula da su, mutukar bai sabawa sharia ba, tun
da musulamai suna kan sharudansu ne kamar yadda hadisi ya tabbatar.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/08/2017
178. TAMBAYA
INA SON KARIN BAYANI AKAN 'YAN TABLIG?
Assalamu alaikum . Da fatan Malam yana lafiya .
Dan Allah ina son bayani akan tabligh da mutanen pakistan suka assasa kuma suke
yawon da awa suna kiran mutane su fita da'awa na wasu kwanaki ko watanni.
Mijina ya shiga kuma zai tafi kwana 40 amma ni hankali na ya ki kwanciya da
hakan . Jazakallah . Ina binku ne a whatsapp.
Amsa:
Wa alaikum assalamu.To 'yar'uwa 'yan tablig wasu
jama'a ne wadanda suka sanya da'awa i zuwa ga Allah babban aikinsu, kuma mutane ne masu gudun duniya, in sun je
gari da'awa ba sa sauka wajan kowa,
saidai şu shiga masallaci, suna dagewa sosai wajan da'awa duk alhamis
a wasu kasashen, Muhammed Yûsuf
Al-kandahlawy Ba'indiye wanda ya mutu a shekara ta:1364 bayan hijira shi ne ya kafata.
Saidai akwai kura-kurai da yawa a tafiyarsu, daga cikin akwai :
1. Karancin ilimi,
ba şu damu şu yi ilimi mai zurfi ba, ko dan yaya şu ka Samu sai şu
tsunduma çıkın da'awa.
2. Ba şu
damu da hana aikata mummuna ba, şuna karfafa da'awarsu ne wajan umarni da
ayyukan da Allah ya ke so.
3. Suna da karancin
ilimin tauhidi, sun fi damuwa da bayanin
falalolin ayyuka
4. Suna kafa hujja da hadithai raunana da na
karya.
5. Wasu daga cikinsu suna sakaci da hakkokin
iyalansu, saboda shagalarsu da da'awa.
6. Sukan aibanta malaman da ba sa cikinsu, da rashin damuwa da Şakacı da da'awa.
7.Karancin
iliminsu yana jawo musu fadawa kura-kurai wajan fassara Al'qur'ani. In har kin
san mijinki yana da karancin ilimi zai
fi kyau ki sanya a tsawatar masa, game da bin su don kar ya fito kafin ya nuna, duk wanda ya zamar da kansa malami kafin ya
isa, barnarsa za ta fi gyaransa yawa.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
5/3/2016
179. TAMBAYA
DAGA YANZU MAHAJJATAN NIGERIA BA ZA SU SAKE
HALARTAR JIFAN SHAIDAN BA!
Dr. muna so ayi mana bincike akan wannan : Daga Yanzu Mahajjatan Nijeriya
Ba za Su Sake Halartar Jifan Shedan Ba, Inji Sarkin Kano Alhaji Muhammadu
Sanusi II kuma Amirul Hajji na bara, a hajjin da ya gabata ya bayyana cewa daga
yanzu mahajjatan Nijeriya ba za su sake halartar jifan Shedan ba, saidai idan
an sama musu masauki a kusa da Jamrat inda a nan ne za a gudanar da jifan, Ya
kuma kara da cewa bakaken fata irin al'ummar Nijeriya bai zama wajibi sai sun
gudanar da jifan Shedan ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne bayan yawan mace-macen
da aka samu a wurin turmutsitsin jifan Shedan a hajjin bara, wanda ciki har da
mahajjatan Nijeriya kimanin saba'in suka rasa ransu. Ya kuma kawo hujjoji da
dama daga ayoyin Kur'ani, wadanda suka nuna cewa rashin halartar jifan Shedan
ba zai kawo rauni a hajjin mahajjaci baa .
Amsa:
Ina rokon Allah ya ba mu dacewa, ya kuma sanya
rayuwarmu kamar yadda yake so, tabbas
wannan Magana ta mai martaba ta girmama, amma ga amsoshin da zan iya
bayarwa a takaice:
1. Farko dai abin da bincikena ya tabbatar min shi
ne:
Daga cikin manyan dalilan da suka sanya shemomin
Nigeria su ka yi nisa da wajan jifa shi ne saboda kasancewar su sun fi sauki,
sannan ba Nigeria ce kawai take da shemomi ba a Muzdalifa, daga cikin kasashen
da suke zaune a Muzdalifa akwai:
FARANSA, INGILA, MURITANIYA, BANGALADESH, CHAINA,
PAKISTAN, INDIA, KARLA, AFGNISTAN,
TURKISTAN,
da wasu daga cikin Agencies na cikin Saudiyya masu araha.
2. Samawa alhazan Nigeria wuri kusa da wajan Jifa,
zai jawo kudin hajji ya kara tsada, ta yadda zai gagari talaka, saboda duk shemar
da ta fi kusa da wajan Jifa to tafi tsada.
3. Akwai
Agencies da yawa na bakaken fata
wadanda suke zaune a kusa da wajan jifa, amma suna da tsada, wannan sai ya nuna ba kasancewarsu 'yan Afrika ba
ne yasa ake ba su wuri mai nisa ba, mas'ala ce ta kudi kawai.
4. Jifan Shaidan ibada ce tabbatacciya daga manzon
Allah s.aw, wacce ya yita kuma ya umarci
mutane su koya a wajansa, kamar yadda ya tabbata a hadisin da Muslim ya
rawaito a lamba ta: 3197, wannan sai ya
nuna hana bakaken fata zuwa jifan Shaidan sabawa nassi ne karara.
5. Dukkan ayyukan da shari'a ta yi umarni da su ba sa rabuwa da wahala, wacce za'a iya
jurewa, wannan ya sa aka siffanta
su da TAKLIF, kamar yadda ya tabbata a
ilimin Usulul-fiqh, Hana Alhazan Nigeria jifan Shaidan saboda wahalarsa, rashin
kulawa ne da ka'idojin ilimin
MAKASIDUSHSHARIA.
6. Jifan Shaidan wajibi ne a wajan malamai da
yawa, saboda Manzon Allah ya yi shi kuma ya umarci mutane su yi koyi da shi, In
da ace zai kai zuwa ga halaka, tabbas ana iya barinsa saboda ka'aidar: لا
واجب مع العجز, duk sanda aka samu kasawa wajan aikata
wajibi to yana faduwa, saidai har yanzu ba'a samu ba, tun da Shari'a ta ba da
damar yin jifa tun daga safe a ranar sallah har zuwa dare, tun daga zawalin
rana a ranakun 11-13, har zuwa dare, yana
daga cikin ka'aidojin sharia: Hukuncin sharia yana zagayawa ne da sababinsa.
7. Hukunce-hukuncen sharia ba sa bambanta daga
baki zuwa fari, saboda Annabi s.a.w. an
aiko shi ne zuwa dukkan mutane kamar yadda
aya ta: 28 a suratu Assaba'i ta tabbatar da hakan.
8. Ayoyin alqur'ani da hadisan za'a iya jawowa
akan faduwar jifa saboda tirmitsitsi, suna magana ne akan wahalar da ta wuce
wacce aka saba da ita,ko kuma wani uziri da sharia ta yadda da shi, amma ba
wahalar da aka saba da ita ba a yawancin hukunce-hukunce.
9. Hajji ginshiki ne daga cikin turakun addinin
musulunci, wanda yake da bangarori da yawa, barin wani sashe daga cikinsa ba
tare da uzuri ba yana iya gurgunta shi, babu mamaki kuma ba za ka sake samun
damar yin wani ba.
10. Allah ya sanya ibadoji da yawa a cikin aikin
hajji saboda mutane su samu lada cikin sauki, ya kamata ka dage wajan yin kowacce ibada ba tare da nakasu ba, in har ka samu
ikon hakan.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
8 Zul-hijja 1437
10\9/2016
180. TAMBAYA
IDAN KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR
IDI, MENENE HUKUNCIN?
Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka.
Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan.
Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da
ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin
shi. Allah ya bada ikon amsawa.
Amsa
Wa'alaikum assalam,
Amin Allah ya amsa adduarka.
Malamai sun yi sabani game azumin kaffara idan ya
ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu :
1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba
da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar
Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce
maganar mafi yawan malamai.
2. Ya
wajaba ya sha azumi a ranar
idi, saboda yin AZUMI haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin
Umar dan khaddabi ya tabbatar, wannan
yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da Sharia ta yi masa izni.
Zance mafi inganci shi ne na Biyu, saboda idan hani da umarni suka ci karo da
juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda Idi ko tafiya ko haila.
Don neman Karin bayani duba: Al-Muntaka min
Fataawa Alfauzaan 1/152
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
31/08/2017
No comments:
Post a Comment