101. TAMABAYA
Shin Malam mene ne matsayin direban motar da ayayi
hadari aka mutu?,
Assalamu Alaikum Sheikh!!!; Mutum ne suka yi
accident a cikin mota sai aka kai su asibiti, bayan wasu kwanaki wasu daga
cikin wanda suka yi accident din suka mutu. Shin Malam mene ne matsayin direban
motan?, zai yi azumi ne?; kuma idan zai yi guda nawa zai yi?, saboda ba mutun
daya ne ya mutu ba.
Ina fata Sheikh zai amsa don ma amfanin ragowar
musulmai masu damuwa da irin wannan. Na
gode Allah ya kara ilimi da imani.
Amsa:
To dan uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda
biyu:
1. Diyya wacce dangin wanda
ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.2. Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu
ba sai ya yi azumi sittin (60), kamar yadda aya ta 92 a Suratun Nisa'i take
nuni zuwa hakan.
Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya
wajaba ga Direban motar ya yi wa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya,
mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi
gudun da ya zarce ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu
makamancin haka wanda yake nuna sakacin Direba, ko wuce ka'idarsa.
Idan hatsari ya faru wasu suka ji ciwo saboda
sakacin Direba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya
diyyarsu kuma zai yi wa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da
faruwar hatsarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dadidai da
abun.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Al'inaya 1\116,
Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
29\12\2015.
102 Tambaya
NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO!
Assalamu Alaikum Malam jiya bayan na gama cin
abinci, sai na samu
ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai
Allah ya
sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ?
Amsa
Wa'alaikumusalam,
To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to
azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai
azumi
ya yi kokwanton huduwar alfijir, to ya halatta a
gare
shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne
asali,
kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : "Allah ya
halatta
mana cin abinci - a Ramadhana- mutukar mun yi
kokwanton hudowar alfijir", saidai in da zai
yi
kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi
ya ci
abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr Jamilu Zarewa
20/6/2015
103 TAMBAYA
TAFIYA TA KAMA NI A TSAKIYAR YINI, KO ZAN IYA
KARYA AZUMINA?
assalamu alaikum. akramakallahu barka DA warhaka
tambaya gareni, mutum ne zaije umara cikin azumi sai yazamana jirginsu zai
tashi karfe biyu na ranan, shin kame bakine daga safe zuwa lokacin tashin KO
kuwa bazaiyi azumi ba kwata kwata aranar?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Zancen mafi
yawan malaman Hanafiyya da Malikiyya da Shafi'iyya shi ne : idan mutum ya yi
tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci ba, saidai idan ya shiga wahalar da
ba zai iya jurewa ba, amma a wajan malaman Hanabila ya halatta, saboda Allah ya
halattawa matafiyi cin abinci a suratul Bakara kuma bai banbanta tsakanin wanda
ya yi tafiya a farkon yini ba, da wanda ya yi a tsakiya.
Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba : Al'insaf 3/205
Amsawa
Dr Jamilu Zarewa
21/6/2015
104 TAMBAYA
IDAN NA KUSANCI MIJINA, YANA KYAMATATA, MENENE
MAFITA?
Assalamu alaikum MALAM nice ina da miji a duk
lokacin da zan zo kusa da shi sai yace min barci yake ji, ai shari a ta hana na
dameshi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina da shi, Allah
taimaki MALAM menene mafita?
Amsa
Wa'alaikum assalam,
Ki tambaye
shi dalılin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma
akwai Wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya
fitowa fili.
Sharia ba ta halattawa namiji ya ki saduwa da
matarsa ba da gangan, saboda nau'i ne na cutarwa, yana dağa cikin manufofin
aure katange ma'aurata daga kallon haram.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
27/3/2016
105 TAMBAYA
MACE ZATA IYA ASKE GASHIN KANTA?
Assalamu alaikum. Malam gashin matata ne yake
karyewa, musamman in tazo tajewa dayawa yana fita. Shi ne tace tana son ta aske
don sabo yafito
Amsa
Wa alaikum assalam,
ya haramta ga mace ta aske gashin kanta saboda
hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa: "Annabi S.A.W. ya hana Mace ta aske
gashin kanta".
Idan Mace ta aske
gashin kanta zai zama ta Yi kama da Maza, Allah kuma ya La'anci macen da take kamaceceniya
da maza kamar yadda ya zo a cikin
hadisi.
Wasu
malaman sun halattawa Mace ta aske
gashin kanta don wani sabon
gashin ya fito, idan wata lalura ta same
ta kamar KORA ko kwakuyewar Kai, Ibnu
Uthaimin ya ambata hakan a Fataawaa
Nurun aladdarb 10/13 sannan Athram ya hakaito kwatankwacin wannan
fatawar daga Imamu Ahmad.
Allah NE mafi
sani
24/06/2017
Dr. Jamilu Zarewa
106 TAMBAYA
BA A BATA AURAN KAFURAI BAYAN SUN MUSULUNTA ! !!
Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min
malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalan sa ta
dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai
suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda
shariar musuluncinta tsara, sai yace min to yaya matsayin yayan su? To gaskiya
wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah
yataimaka ameen
Amsa
Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa
auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi
akan ƙa'idoji
da sharuɗan da suka yarda da su na
auratayyarsu, saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka musulunta
ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta
hanyar wancan aure.
Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar
zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu,
wannan ya sa duk ɗan da kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi
zuwa iyayansa bayan sun musulunta.
In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za'a danganta
shi zuwa baban sa ba bayan ya musulunta.
Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma
sharhul Mumti'i 12/239.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23-06-2017
107 TAMBAYA
YAUSHE AKE FITA DAGA I'ITIKAFI ?
Assalamu Alaikum. Malam inaso a fada min mafi
rinjayan zance game da lokacin fita daga I'itikafi?
Amsa
Wa'alaikumus salam,
To dan'uwa malamai suna da ra'ayoyi biyu akan
wannan mas'alar :
1. Fita
daga I'iitikafi daga zarar an ga watan Ramadhna, wato bayan rana ta fadi a daren Idi, saboda
I'itikafi ana yinsa ne a Ramadhana
kuma idan an ga wata Ramadhana ya kare.
2. Mai I'itikafi zai iya zama har zuwa lokacin
sallar Idi, ta yadda zai fita bayan kammala sallar, Imamu Asshafi'i yana cewa: "Duk wanda ya yi
niyyar koyi da Annabi S.A.W. to ya fita daga I'itikafi bayan rana ta fadi in an
ga wata, watan ya yi nusan ko ya cika, amma in ya zauna zuwa sallar idi, hakan
shi ne yafi" Imamu Malik yana cewa:
"Na samu labarin wasu daga cikin mutanan kirki suna fita daga I'itikafi
bayan sallar idi"
Zance mafi inganci shi ne fita daga I'itikafi bayan ranar daren idi
ta fadi, saboda Annabi S. A. W. yana I'itikafin dararen goman karshe ne, su
kuma suna fita idan daren IDI ya shiga.
Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy
6/323 da kuma FaTaawa Allajnah Adda'imah 15/411
Allah ne mafi
sani
24/06/2017
Dr. Jamilu Zarewa
108 TAMBAYA
WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU !!!*
Assalamu
alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba
kawai ya rubuta ne shin tasa ku?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ta saku mana,
saboda rubutu yana daidai da
furuci a musulunci, Annabi s. a. w. yana
cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya a zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta
aikata.
Hadisin da ya
gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta saku, saboda duk
masu hankali sun cimma daidaiton cewa rubutu aiki NE, shi kuma
ya yi aiki.
Yana daga cikin Ka'idojin Shariar da malamai fada
a littattafan fiqhu:الكتاب كا الخطاب
Rubutu
kamar magana NE.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
24/06/2017
109 TAMBAYA
WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR IDI
Assalamu Alaikum,
Malam ina so sanin hukunce-hukuncen idi
Amsa
Wa'alaikumus salam.
Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga
ciki:
1. Azumtar
ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin
Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da
shi - cewa : "Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da
ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito
2. Siffar sallar idi- An karbo daga Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa :
"Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya kasance yana fita
ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana
farawa da sallah" Bukari ne ya
rawaito
Ana yin ta ne raka'o'i biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko,
a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud
Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori,
to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na
kabbarori, saboda sunnoni ne ba wajibai ba.
Dr. Jamilu Zarewa
7/8/2013
110 TAMBAYA
SHIN ZAN IYA SAKIN AMARYATA DOMIN NA TARA DA ITA
SAI NA GANE BABU BUDURCI A TARE DA ITA ???
Assalamu alaikum malam amincin Allah ya kara
tabbata ga malam tareda karin kariya har abada amin.
Tambayata itace: Shin mutum nada hakkin sakin
matarsa (Amarya) wacce ya aura ya tara da ita yagane cewa ba budurwabace akwai
wani abu daya faru kafin tashigo gidansa. Zai iya sakinta?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Wannan na daga cikin shubuhohin aure wanda zargi
ke kawo haka baya da tabbacin wani abu ya faru kafin ya aure ta, kuma koma wani
abun ya faru ai tuba na kankare komai don haka yayi hakuri a cigaba da zama da
matar sa, domin bincike ya nuna akwai hanyoyin da mace ka iya saryantar da
budurcin ta koda bata sadu da wani da namiji ba...
Don haka ya zauna da matar sa ya rike ta bisa
amana.
Wallahu A'alam
Amsawa
Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
28/06/2017
111. TAMBAYA
NA HAIHU JINI YA WUCE KWANA 40, YAUSHE NE HAILA ZA
TA IYA ZUWA MUN?
Assalamu Alykum malam tambayata anan itace don
Allah malam tsawon kwana kin jinin biki ance kwana 40 ne to jini bai dauke ba
sainayi wanka a 40 din abin tambaya ta anan shine bayan kwana 40 kwana nawane
haila zata iya zuwa ma mutum don saboda bayan kwana 2 da arba'in wani jnin ya
zo Wanda nidai ba kalar jinin haila bane kuma Yana.zuba sosai kamar.jini idan
mutum ya.yanke yaji ciwo to Sai naci gaba da sallah da sauran ibada shin yaya
matsayin haka.da nayi don Allah malam a
amsa min tambayarnan don insan miye nagode.
Amsa:
Wa rahmatullahi wa barakaatuhu, To, Lallai
'Yar'uwa, duk da cewa Malamai sunyi sabani game da adadin yawan kwanakin jinin
Biki, amma dai magana mafi karfin da ladili itace jinin Biki baya wuce kwana
arba'in (40), kuma itace maganar mafi yawancin Sahabbai da Tabi'ai da wadanda
suka biyo bayansu, sai dai idan jinin Biki ya wuce kwana arba'in (40) bai
daukeba to, sai ki lura idan lokacin yayi dai-dai da lokacin da kika saba yin
Haila ne to, Hailarki ce ta dawo, domin mafi yawanci jinin Haila yakan dawoma
macen da ta haihu ne a karshen sati na shida bayan haihuwa, idan kuma baiyi
dai-dai da lokacin Hailarkiba, to, ya zama jinin ciwo (Istihadah), sai kiyi
wanka kicigaba da Sallah da sauran aiyukan Ibada, sai dai duk lokacin da zakiyi
Sallah sai kinyi tsarki kin sake alwala.
A duba littafin Almugnee na Ibn Qudaamah, ko
Tadauwurul Janeen, ko Diraasah anil Haidi wan Nifaas, ko fatawar Al-Lajnah Al-
Daa'imah, mai lamba ta 3923 dan samun karin bayani.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
08/06/2017.
112. TAMBAYA HUKUNCIN ZUBAN JINI KO DAUKEWAN SHI
SANADIYAR SHAN MAGANI
Assalamu alaikum, Menene hukuncin jinin da ya samu
mace ta hanyar rashin shan maganin planing da ake sha wadda da zata tsallake
kwana biyu bata sha ba jini zai zo mata amma data ci gaba da sha zai dauke shi
ne nike son in san hukuncin shi.
Amsa:
Wa alaikumus Salaam, Lallai jinin da yake zo
ma Mace sanadiyyar amfani da hanyoyin
kayyade Iyali (Planning) shi ne asalin jinin Haila, dan haka a duk lokacin da
mace ta yi amfani da wata hanya ta kayyade Iyali (planing) ta hanyar fitar da jini ko hana
jinin fita, to babban abin da za ta lura da shi, shi ne, duk lokacin da jinin
ya fito, hukuncin Haila ya hau kanta, ko da ba lokacin da ta saba haila ba ne
in dai jinin ya zo to, hukuncin Haila ya tabbata a kanta.
Amma idan maganin ya hana jinin fita ne to,
hukuncinta hukuncin mace mai tsarki ko da lokacin da ta saba Haila ne in dai
jini bai zo ba to, babu hukuncin Jini a kanta domin hukuncin jini ba ya tabbata
sai lokacin da jinin ya fito.
Allah Ya
bamu ikon ganewa da gyarawa.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
01/07/2017.
113. TAMBAYA TSARKIN HAILA YA ZO MATA GA SHI BATA
DA LAFIYA BA ZA TA IYA TABA RUWA BA; YA ZA TA YI?
Assalamu alaikum, Mal. Mace ce ta gama haila amma
a lokacin bata da lafiya kuma in har ta sa ruwa akanta akwai matsala, Yaya ya
kamata ta yi?.
Amsa:
Wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Idan jinin Haila ko na Biki ya dauke ma mace
a lokacin da take cikin uzurin da ya hana ta amfani da ruwa to, za ta jinkirta
wanka sai uzurin da ya hana ta wanka ya gushe, sai dai kafin ta yi wankan sai
ta rika yin taimama madadin Alwala.
A duba littafin Majmu'ul fatawah na Shaikhul Islam
Ibn Taimiya mujalladi na 19, dan samun karin bayani.
Allah ne
mafi sani.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
01/07/2017.
114. TAMBAYA KWANAKI NAWA NE TSAKANIN HAILA ZUWA
WATA HAILAR?
Assalamu alayk wa Rahmatullah wa Barakatuh. Don
Allah kwanaki nawa ne tsakanin haila da wata hailar don yau kwana 13 da na fara
haila sai na yi kwana 5 na yi tsarki sai kuma yau gashi ta zo. Allah Ya sa mu
dace.
Don Allah ina jiran answer don in san hukuncin da
ke kai na. Its urgent pls.
Amsa:
To, 'Yar uwa, Malaman Musulunci sun hadu akan cewa
shari'ar Musulunci ba ta kayyade wasu kwanakin tsawon tazarar Haila zuwa wata
Haila ba, amma sun yi sabani game da karancin tazarar kwanakin Haila zuwa wata
Hailar. Wasu Malaman sun ce: karancin kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Hailar,
sai ya kai kwana goma shabiyar (15), wasu suka ce: kwana goma sha uku (13),
wasu sukace kwana goma (10), wasu suka ce: kwana takwas (8) zuwa goma (10),
wasu suka ce kwana takwas (8).
Amma magana tabbatacciya ita ce Shari'ar Musulunci
ba ta kayyade karanci ko yawan tazarar kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Haila
ba, Mace tana iya yin Haila uku (3) cikin wata guda musamman masu amfani da
magani ko allurar tazarar haihuwa, nan da nan sai Haila ta ta zo musu. Sai dai
idan Mace ta yi da'awar ta gama idda kasa da lokacin da aka saba gama idda, to
sai ta zo da wanda zai shedeta cikin danginta makusanta akan cewa haka hailarta
take.
A duba Majmu'ul fatawah na Sheikhul Islam Ibn
Taimiyya Mujalladi na 19, ko littafin Al-Haidu wal Hamdu wannifaas bainal fiqhu
waddibu na Umar Sulaimanu Al- Ashqar, dan samun karin bayani.
Allah ya
taimake mu.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
04/07/2017.
115. TAMBAYA KWANAKI NAWA NE TSAKANIN HAILA ZUWA
WATA HAILAR?
Assalamu alayk wa Rahmatullah wa Barakatuh. Don
Allah kwanaki nawa ne tsakanin haila da wata hailar don yau kwana 13 da na fara
haila sai na yi kwana 5 na yi tsarki sai kuma yau gashi ta zo. Allah Ya sa mu
dace.
Don Allah ina jiran answer don in san hukuncin da
ke kai na. Its urgent pls.
Amsa:
To, 'Yar uwa, Malaman Musulunci sun hadu akan cewa
shari'ar Musulunci ba ta kayyade wasu kwanakin tsawon tazarar Haila zuwa wata
Haila ba, amma sun yi sabani game da karancin tazarar kwanakin Haila zuwa wata
Hailar. Wasu Malaman sun ce: karancin kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Hailar,
sai ya kai kwana goma shabiyar (15), wasu suka ce: kwana goma sha uku (13),
wasu sukace kwana goma (10), wasu suka ce: kwana takwas (8) zuwa goma (10),
wasu suka ce kwana takwas (8).
Amma magana tabbatacciya ita ce Shari'ar Musulunci
ba ta kayyade karanci ko yawan tazarar kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Haila
ba, Mace tana iya yin Haila uku (3) cikin wata guda musamman masu amfani da
magani ko allurar tazarar haihuwa, nan da nan sai Haila ta ta zo musu. Sai dai
idan Mace ta yi da'awar ta gama idda kasa da lokacin da aka saba gama idda, to
sai ta zo da wanda zai shedeta cikin danginta makusanta akan cewa haka hailarta
take.
A duba Majmu'ul fatawah na Sheikhul Islam Ibn
Taimiyya Mujalladi na 19, ko littafin Al-Haidu wal Hamdu wannifaas bainal fiqhu
waddibu na Umar Sulaimanu Al- Ashqar, dan samun karin bayani.
Allah ya
taimake mu.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
04/07/2017.
116. TAMBAYA HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)?
Assalmu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da
imani, malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a musulunci
Amsa:
Wa alaikum assalam,
To 'yar'uwa
Babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da
al'aura har maniyyi ya fito, duk hadisan da suka zo ba su inganta ba.
Saidai wasu malaman sun haramta auran hannu saboda
aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan bukatar sha'awa ta hanyar matar
aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan
bukata ta hanyar su.
Yin wasa da
al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance, saidai yana
daga cikin ka'idojin shari'a ; idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda
za'a yi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa
Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta
auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.
Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai
barnar dake cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan
tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi 'ya'ya gantalallu, marasa
asali, wannan ya sa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu
sharudan da suka gabata.
Don neman
Karin bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu'ul fataawaa 34\146>
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23\1\2016
117. TAMBAYA HUKUNCIN MIJIN DA MATARSA TA NEME SHI
DA JIMA'I BAI AMSA MATA BA?
Assalamu alaikum, malam ina roko a taimaka min da
amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta
ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijin ta shi kuma yaki, shi
ma ya aikata zunubi ne ko ko?
Amsa
Wa'alaikumussalam,
To dan'uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi cewa
"Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa
ba ta amsa masa ba, to mala'iku za su tsine mata har ta wayi gari"
kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 1436. Saidai abin da malamai suke cewa shi ne :
Namiji ba shi da laifi, idan matarsa ta neme
shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin
namiji da mace sun bambanta, saboda mace za'a iya saduwa da ita ko da ba ta da
sha'awa, namiji kuwa sai yana da sha'awa, zai iya saduwa, don haka akwai
bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima'i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu
ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin
da za ta iya, sannan sha'awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji
ne yake neman matarsa ba akasin haka ba.
Allah ne ma fi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
19\3\2014
118. TAMBAYA NA TUBA DAGA ZINA, YAYA IDDATA
?
Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da
tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa ne ISTIBRAI din ta?
Amsa
Wa'alaikumus salam,
To 'yar'uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata
daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta
tuba, malamai sun yi sabani game da iddarta.
1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa za ta yı jini
uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai
tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi,
da kuma wacce aka şaka.
2. Za ta yi jini daya kawai, saboda fadin Annabi
S.a.w. "Ba'a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma
sai ta yi haila daya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.
Don neman Karin bayani duba Almausu'a Alfikhiyya
Alkuwaitiyya 30/341.
Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa
da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana
tabbata da jini daya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya,
saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa
babu shi a iddar zina.
Allah ne mafi Sani.
*Dr. Jamilu Zarewa
22\2\2016
119. TAMBAYA
BA'A YIN GATSE A SAKI !!!
Assalamu Alaiku Tambaya: Dr, mutum ne sukayi fada
da kawun matarshi sai kawun matar yace dashi iyakaci dai kace ka saki 'yata,
sai shi kuma mijin yace na saketa saki uku, amma matar bata gurin ma'ana bata
jiba, sai daga baya ta samu labari, don Allah Dr. Menene matsayin Aurensu?
Nagode Allah ya karawa Dr. Lafiya da Imani.
Amsa
Wa alaikum assalam, ta saku mana tun da ba'a wasa
a saki, mutukar an furta ai kalmar ta zartu
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
11/12/2016
120. TAMBAYA
MENENE MATSAYIN ADDU'AR MAWAKA A CIKIN WAKENSU..?
Assslam alaika Allah ya karawa Dr lafiya mallam
mene matsayin addu'ar da mawaka suke a cikin wakensu shin za'a iya amsawa
Amsa
Wa'alaikimus salam. To dan uwa da farko dai ita
addu'a tana da ladabi da ka'idoji wanda shari'a ta shimfida ayi addu'oin ba dai
dai bane mutum yana rokon Allah yana
waka yana kida wannan izgilancine, ya kamata mutane suji tsoron Allah su
kiyaye.
Dangane da amsawa kuma Allah madaukakin sarki
shine yake amsa addu'a a duk yadda bawa yayi' dayawa akan samu mutum yana cikin
sakoma ya roki Allah kuma ya amsa idan yaga dama amma baya daga cikin abinda
malamai magada Annabawa suka rubuta a litattafi cewa mutum' yayi addu'a a cikin
waka kuma Allah ya karba ya kamata komai mutum zaiyi yayi abinda shari'a ta
amince dashi sai dai idanya cika sharudan karbar addu'ar da malamai suka
shimfida idan yayi Allah zai karba sai dai kawai za'a kamasa da yayi izgilanci
yayi abin bata hanyar daya kamata yayi ba
Allah shine mafi sani
Amsawa
DR. ABDALLAH GADON KAYA
18/04/2017
No comments:
Post a Comment