GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Saturday 19 May 2012

TAMBAYA TA DARI BIYU DA ASHIRIN DA DAYA (221) ZUWA TA DARI BIYU DA ARBA'IN (240)

221. TAMBAYA

SHIN ME NENE ZIHARI?

 

Assalamu alaykum Warahmatullahi wabarakatuh. Don Allah Mallam menene ZIHARI? Allah yaqara ilimi mai amfani.

 

Amsa

Wa'alaykumussalam,

Zihari shi ne mutum ya kamanta matan shi da wata wanda take muharrama a gare Shi kamar Mahaifiyan sa, kanwar shi ko 'Yar shi da ya haifa.

Wallahu A'alam

Malam Umar Shehu Zaria

03/03/2017

 

 

222. TAMBAYA

ALAMOMIN KARBAR TUBA

 

Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya?

 

Amsa

 

Wa alaikum assalam.To dan'uwa

akwai alamomin da malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga ciki :

1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai kusantar da shi zuwa ga Allah.

2. Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya ga Allah.

3. Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .

4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba, a matsayin ni'ima daga Allah.

5. Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da kafin ya tuba.

6. Yawan istigfari.

7. Son kusantar salihan bayi.

Allah ne ma fi sani .  

 Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA                                                                              5/6/2014

 

223. TAMBAYA

ZAN IYA CIN BASHIN BANKI SABODA ZUWA HAJJI ?

 

Assalamu alaikum, malam don Allah ina da tambaya kamar haka - ko zan iya cin bashin banki wato loan domin cika kudin kujerar maka,? Nabiya ma mahaifiyata sabida karin kudin da akayi ya wuce abinda muke zaton cikawa kuma ni ma'aikaciyar gwamnati ce. Na gode Allah yabada ikon amsawa. via UMMUHATUL MUMININ.

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

mutukar ba ki da hali to barin zuwa aikin hajjin shi ne daidai,, saboda Allah ya kwashewa kudin ruwa albarka a cikin suratul Bakara kuma ya yi shirin fito-na-fiton yaƙi da wanda ya ci riba,, sannan Allah bai wajabta miki hajji ba ta hanyar bashi,, balle kuma ki biyawa wani.

Hajji yana wajaba ne ga wanda  yake da iko da kuma isasheshen guzirin da zai wadatar da shi daga rokon mutane.

Allah ne mafi sani

5/6/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

 

 

224. TAMBAYA

AL'ADATA  TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI?

Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci. Malam matsala ta haihuwa greni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na nkeyi nacigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin tawa take.

Amsa

Wa'alaykumussalam,

To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a cikin alqur'ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki bar  sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda  ba zai hana sallah da azumi ba.

 

Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911, saidai  yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al'ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa.

Allah ne mafi sa ni

Dr. Jamilu Zarewa

22\1\2016

 

225. TAMBAYA

BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA

 

Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam.

Amsa:

Wa alaikum assalam,

 Annabi S. A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare.                                       Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin    Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare wutiri".

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr. Jamilu Zarewa

07/06/2017.

226. TAMBAYA

AURAN KAFURAI BAYAN SUN MUSULUNTA INGANTACCE NE!

 

Assalamu alaykum, Don Allah ina son a tambaya min malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalansa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar Musulunci ta tsara, sai yace min to yaya matsayin 'ya'yansu? To gaskiya wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah yataimaka ameen.

Amsa:

Wa alaikum assalam,

To ɗan uwa, auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure.

Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai  suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.

In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za a danganta shi zuwa babansa ba bayan ya musulunta.

Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti'i 12/239.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

07/06/2017.

 

227. TAMBAYA

SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA, MENENE SHAWARA

Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace. Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara daya mijina be kusanceniba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Nagode

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Auranku ingantacce ne,, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da saduwar ma'aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai ma'aurata zuwa saɓon Allah. In har ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka.

Allah ne mafi sani

08/06/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

228. TAMBAYA

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI DA MAZIYYI DA KUMA WADIYYI

Amsa:

 

 1. Maniyyi

 Maniyyin namiji : ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshin kwai.

 Maniyyin mace : ruwa ne tsinkakke, MAI FATSI-FATSI, WANI LOKACIN KUMA YANA ZUWA FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji tsananin sha'awa da kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshin kwai, kuma za ta ji sha'awarta ta yanke bayan fitowarsa.

HUKUNCINSA SHI NE : YANA WAJABTA WANKA

 

 2. Maziyyi : Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa, haka nan yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya sa sha'awa ta tafi, kuma wani lokacin ba'a sanin ya fito.

 Malamai suna cewa : Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da maziyyi zai fitowa namiji azzakarinsa zai mike.

 HUKUNCINSA SHI NE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA

 

 3. Wadiyyi wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wadanda suke fama da gwauranci ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

 

 YANA DAUKAR DUKA HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI

Allah ne mafi sani.

31/05/2013

Dr. Jamilu Zarewa

 

229. TAMBAYA

DAN ACABA ZAI IYA KAI KIRISTA COCI?

Assalamu alaikum, Akramakallahu, Shin ya halatta MUSULMI DAN ACABA ya dauki KIRISTA ya kai Shi COCI, ko ya dauko Shi daga Coci zuwa gida? Domin Suna cewa: Mu Sana'a kawai Mu ke yi, haka abin ya ke a bangaren MAGINA, TELOLI, KAFINTOCI da MA SU WAYARIN da sauran su.

Amsa:

To dan uwa Allah Madaukakin Sarki Ya hana taimakekeniya wajan aikata sabo, kamar yadda aya ta biyu a suratul Ma'ida ta tabbatar da hakan.

Yana daga cikin sharuddan cinikayya ya zama ta hanyar da shari'a ta yarda, wannan ya sa kafinta da magini ba za su taimaka wajan gina inda za a saba wa Allah ba, ko da kuwa za su samu kudi, kamar yadda bai halatta Tela ya dinka kayan da za a  sanya a coci a kira wanda ba Allah ba.

Duk wanda ya wadatu Allah Zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah Zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da bata karewa.

Don neman Karin bayani duba: Al'umm 4\213. Da kuma Iktidha'u siradil mustakim 2\41.

Allah ne mafi Sani

Amsawa:

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

12\2\2016.

 

230. TAMBAYA

DAN ACABA ZAI IYA KAI KIRISTA COCI?

Assalamu alaikum, Akramakallahu, Shin ya halatta MUSULMI DAN ACABA ya dauki KIRISTA ya kai Shi COCI, ko ya dauko Shi daga Coci zuwa gida? Domin Suna cewa: Mu Sana'a kawai Mu ke yi, haka abin ya ke a bangaren MAGINA, TELOLI, KAFINTOCI da MA SU WAYARIN da sauran su.

Amsa:

To dan uwa Allah Madaukakin Sarki Ya hana taimakekeniya wajan aikata sabo, kamar yadda aya ta biyu a suratul Ma'ida ta tabbatar da hakan.

Yana daga cikin sharuddan cinikayya ya zama ta hanyar da shari'a ta yarda, wannan ya sa kafinta da magini ba za su taimaka wajan gina inda za a saba wa Allah ba, ko da kuwa za su samu kudi, kamar yadda bai halatta Tela ya dinka kayan da za a  sanya a coci a kira wanda ba Allah ba.

Duk wanda ya wadatu Allah Zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah Zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da bata karewa.

Don neman Karin bayani duba: Al'umm 4\213. Da kuma Iktidha'u siradil mustakim 2\41.

Allah ne mafi Sani

Amsawa:

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

12\2\201

 

 

231. TAMBAYA

ZAN IYA DORA RIBA, IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU?

 

Assalamu Alaikum Mallam, dan Allah ina da tmby, kaman misalin mutum yana baka kudi ka sayo mishi abu, wataran ya baka kudin ka sayo, wataran kuma sai ka sayo ka kai zai baka kudin, shin koya halasta inci riba a wanda yaban kudinshi in sayo mai, ko kuwa a wanda na sayo da kudina ne kawai zan iyacin riba, banda Wanda ya bada kudinshi? Nagode Allah ya kara basira.

 

Amsa:

Allah ya amsa addu'arki 'yar'uwa, idan mutum ya wakilta ki, ya baki kudi ki sayo masa wani abu, bai halatta ki ci riba da shi ba, sai da izininsa, saboda hadisin Urwatu Al-ja'ady lokacin da Annabi s.a.w. ya ba shi dinare (1) don ya sayo masa dabbar layya, sai ya sayo akuyoyi guda biyu, ya sayar da daya akan dinare daya, ya zo ma da Annabi s.a.w. da akuya daya da kuma dinaran da ya aike shi, sai Manzon Allah ya amshe ya yi masa addu'a, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 3642.

 

Kasancewar Annabi S.a.w. ya tabbatar da shi akan aikinsa, sai ya nuna hakan shi ne shari'a, don haka idan wakili ya samu ragi ko ya ci riba a cinikayyar da aka wakilta shi ya wajaba ya dawo da ita zuwa wanda ya aike shi.

 

Idan ya wakilta bai bayar da kudi ba, to mutukar kuna kasuwanci a tsakaninku ya halatta a dora riba, amma in ba kwa yin kasuwanci ba za ki dora riba ba, za ki kawo masa abin a kudin da ake siyarwa a kasuwa, saidai in ya bada iznin cin riba, saboda wakili amintacce ne a shari'a, wasu malaman suna ganin za ki iya dora gwargwadon wahalarki, in bai bada kudi ba.

Don neman Karin bayani duba Al-mugni na Ibnu khudaamah 5\86.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

20\1\2016

 

232. TAMBAYA

ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA MIJINA?

 

Assalamu'alaikum, Malam don Allah wata ce mijinta ya ce hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a musulunci. Shin Malam ya abun yake? Haramun ne, ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne ta yi kwalliya da shi?.

Amsa:

Wa alaikumus Salaam, An tambayi Sheikh Ibnu Uthaimin akan wannan mas' alar ta huda Hancı sai yake cewa: Huda Hancı zai iya zama canza halittar Allah, amma idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yın ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi a yi hakan.

Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.

Haka nan an tambayi Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan haka.

Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce, saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

4\1\2016.

 

233. TAMBAYA

ZAN IYA JAN  CARBI, KO KO BIDI'A NE ?

 

Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Malam Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci. Ina matsayin haka a sharia?

Amsa:

Wa'alaykumussalam,

To dan'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai sa ya  zama bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.

Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486,  don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.

Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.

Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne.

Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne yafi.

Saidai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.

Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul fataawa  22\187. da Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.

 Allah ne mafi sani

Amsawa

DR JAMILU YUSUF ZAREWA

24\3\2015

 

234. TAMBAYA

Assalamu alaikum. Allah ya karama dr lafiya.mlm dan Allah yaya rabin gadon mutumin da ya rasu ya bar 'ya'ya 24 maza 14 amman daya arnene. Mata 10. da matanshi biyu. dr yaya rabon gadon su yake?? kuma dr rabon gado dole ne a musulunci

Amsa

Wa  alaikum assalam,

 za'a raba  abin  da ya bari gida:8, a bawa  matansa kashi  daya  su raba, ragowar  kashi  bakwan  Sai a bawa  'ya'yansa (23) su  raba, duk  namiji ya  dau  rabon   mata  biyu.

Ba za'a  bawa  dansa  kafuri ba, Domin Arne  ba ya  gadon  musulmi saboda  hadisin  Annabi  S. A. W da ya tabbata akan  haka.

Allah ne  mafi  Sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

16/06/2017

 

235. TAMBAYA

DIREBAN MOTA DA YA ZAMA SABABIN MUTUWAR MUTANE DA YAWA, YA YA KAFFARARSA ZA TA KASANCE?

 

Assalamu Alaikum Sheikh!!!; Mutum ne suka yi accident a cikin mota sai aka kai su asibiti, bayan wasu kwanaki wasu daga cikin wanda suka yi accident din suka mutu. Shin Malam mene ne matsayin direban motan?, zai yi azumi ne?; kuma idan zai yi guda nawa zai yi?, saboda ba mutun daya ne ya mutu ba.

Ina fata Sheikh zai amsa don ma amfanin ragowar musulmai masu damuwa da  irin wannan. Na gode Allah ya kara ilimi da imani.

Amsa:

To dan uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:

1. Diyya wacce dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.

2. Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi sittin (60), kamar yadda aya ta 92 a Suratun Nisa'i take nuni zuwa hakan.

Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga Direban motar ya yi wa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarce ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Direba, ko wuce ka'idarsa.

Idan hatsari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Direba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yi wa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hatsarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dadidai da abun.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Al'inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

29\12\2015.

 

236. TAMBAYA

NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO!

 

Assalamu Alaikum Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ?

 

Amsa

Wa'alaikumusalam,

To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to

azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai azumi

ya yi kokwanton huduwar alfijir, to ya halatta a gare

shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali,

kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : "Allah ya halatta

mana cin abinci - a Ramadhana- mutukar mun yi

kokwanton hudowar alfijir", saidai in da zai yi

kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi ya ci

abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.

 

Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa

20/6/2015

 

237. TAMBAYA

TAFIYA TA KAMA NI A TSAKIYAR YINI, KO ZAN IYA KARYA  AZUMINA?

 

assalamu alaikum. akramakallahu barka DA warhaka tambaya gareni, mutum ne zaije umara cikin azumi sai yazamana jirginsu zai tashi karfe biyu na ranan, shin kame bakine daga safe zuwa lokacin tashin KO kuwa bazaiyi azumi ba kwata kwata aranar?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Zancen mafi yawan malaman Hanafiyya da Malikiyya da Shafi'iyya shi ne : idan mutum ya yi tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci ba, saidai idan ya shiga wahalar da ba zai iya jurewa ba, amma a wajan malaman Hanabila ya halatta, saboda Allah ya halattawa matafiyi cin abinci a suratul Bakara kuma bai banbanta tsakanin wanda ya yi tafiya a farkon yini ba, da wanda ya yi a tsakiya.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani duba : Al'insaf 3/205

21/6/2015

Dr. Jamilu Zarewa

 

238. TAMBAYA

IDAN NA KUSANCI MIJINA, YANA KYAMATATA, MENENE MAFITA?

 

Assalamu alaikum MALAM nice ina da miji a duk lokacin da zan zo kusa da shi sai yace min barci yake ji, ai shari a ta hana na dameshi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina da shi, Allah taimaki MALAM menene mafita?

Amsa

Wa'alaikum assalam,

 Ki tambaye shi dalılin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma akwai Wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya fitowa fili.

Sharia ba ta halattawa namiji ya ki saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau'i ne na cutarwa, yana dağa cikin manufofin aure katange ma'aurata daga kallon haram.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

27/3/2016

 

239. TAMBAYA

MACE ZATA IYA ASKE GASHIN KANTA?

 

Assalamu alaikum. Malam gashin matata ne yake karyewa, musamman in tazo tajewa dayawa yana fita. Shi ne tace tana son ta aske don sabo yafito

Amsa

Wa alaikum assalam,

ya haramta ga mace ta aske gashin kanta saboda hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa: "Annabi S.A.W. ya hana Mace ta aske gashin kanta".

Idan Mace ta aske  gashin kanta zai zama ta Yi kama da Maza,  Allah kuma ya La'anci macen da take kamaceceniya da  maza kamar yadda ya zo a cikin hadisi.

Wasu  malaman sun halattawa Mace ta aske  gashin kanta don wani  sabon gashin  ya fito, idan wata lalura ta same ta kamar  KORA ko kwakuyewar Kai, Ibnu Uthaimin ya ambata hakan a Fataawaa  Nurun aladdarb 10/13 sannan Athram ya hakaito kwatankwacin wannan fatawar daga Imamu Ahmad.

Allah ne mafi  sani

24/06/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

240. TAMBAYA

BA A BATA AURAN KAFURAI BAYAN SUN MUSULUNTA!

 

Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to yaya matsayin yayan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah yataimaka ameen

 

Amsa

Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure.                             Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai  suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.

In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa baban sa ba bayan ya musulunta. 

Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti'i 12/239.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

23-06-2017


No comments: