GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Sunday 13 May 2012

TAMBAYA TA DARI DA ASHIRIN DA DAYA (121) ZUWA TA DARI DA ARBA'IN (140)

121. TAMBAYA

WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU !!!*

 

 Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?

Amsa

Wa alaikum assalam,  ta  saku mana,  saboda rubutu yana  daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W.  yana cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame

akan abin da ta riya  a zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata.

Hadisin da ya  gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa rubutu aiki NE,  shi kuma  ya yi aiki.

Yana daga cikin Ka'idojin Shariar da malamai fada a littattafan fiqhu:الكتاب كا الخطاب Rubutu kamar magana NE.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

24/06/2017

 

122. TAMBAYA

ZAN IYA YIN AZUMI UKU KAWAI A MATSAYIN SITTA SHAWWAL?

 

Assalamu alaikum, malam Tambayata shine don Allah Malan mutun ze'iyayin azumin sitta shauwal guda uku?

Amsa

Wa'alaikumus salam,

Ba za'a iya a zumtar kwana uku a matsayin sitta shawwal ba, domin manzon Allah cewa yayi kwana shida(6) don haka dole sai kwana shida din.

Wallahu A'alam.

Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

12/07/2017

 

123. TAMBAYA

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE

SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI

DAMAR KOME?

 

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware

mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta,

mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1 ya

koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata

shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan

sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake

rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu

akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren

wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya

kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa

ne yake kanta nagode Allah yakara imani da

basira sai naji daga gareka

Amsa :

Wa alaikum assalam  To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka

siffanta, to babu damar kome, sai in ta auri wani

mijin na daban, saboda igiyoyin da suke

tsakaninku sun yanke gaba dayansu.

Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a

baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da

ka mata, kafin ka sake auranta, da ba'a kirga da

saki biyun baya ba, amma tun da ba ta aura ba,

ya wajaba ku hakurewa juna .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na

Ibnu-Khudaamah 7\388 .

Allah ne mafi sani.

 Amsawa

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

3\5\2015

 

124. TAMBAYA

NA YI AURE KAFIN NA YI ISTIBRA’I

 

Assalamu alaikum

Ya kamata a ce na yi istibra’i kafin na yi aure,

amma ban yi ba, har na yi aure, yanzu haka ina

jini na farko ban yi tsarki ba, amma ba da wanda

na aikata laifin na yi aure ba. Ya ingancin aure

na? Gani nake kamar babu auren.

Amsa

Wa'alaikumus salam,

Toh

farko dai ina miki wasici da tsoron Allah saboda

zunubin da kika aikata, amma game da aure, to

aurenki ya yi, saidai yinsa bayan istibra’i shi ne

ya fi, sannan ya wajaba mutukar kin san kina da

ciki to bai halatta ki bawa sabon mijinki dama ya

take ki ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya yi

imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar

da ruwansa ga shukar waninsa” Abu- dawud :

1847. Don haka ya wajaba a gare ki ki yi stibra’i

kafin mijinki ya sadu da ke, sannan istibra’i jini

daya ne , idan kuma har kin dauki ciki, kafin ki yi

istibra’i, in kin haihu kafin wata shida to ba

dansa ba ne, amma in har kin haihu bayan wata

shida daga fara saduwarku, to dansa ne, mutukar

ba’a samu shaidar da take nuna kina da ciki ba,

tun kafin ku fara saduwa . Don neman Karin

bayani duba : Al-mugni na Ibnu kudaamah 8\79

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

1/12/2016

 

125. TAMBAYA

YAUSHE AKE FITARWA DA GOLD ZAKKA?

 

Assalama Alaikum Warrahmatullah. Malam ya

kokari, Allah ya saka da Alkhairi. Don Allah

Malam ina so in san nisabin zakka na gwal (gold)

nawa yake kaiwa idan za’a cire?.

 

AMSA

Wa alaikum assalam,

 Ana fitarwa da Goal zakka

idan ya kai gram tamanin da biyar (85).

Allah ne mafi sani.

1/08/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

126. TAMBAYA

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA  BA LAFIYA?

 

Assalamu Alaikum, Dr macece mijinta

ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya

zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani

dogon tunani na sha’awaba, ya matsayin

ibadarta yake ?

Amsa

Wa'alaikumus salam.

To gaskiya abin da yake

daidai shi ne :

 ya nemi magani, in kuma bai

samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga

cikin manufofin aure, kadange ma’aurata daga

fadawa haramun, kamar yadda shararren

hadisinnan ya tabbatar. Yawan fitar maniyyi zai

iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin

sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba,

saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin

neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya

rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa

ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama

mazinata ta hanyar wannan sababin ? ya

wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita,

tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

21/12/2016

 

127. TAMBAYA

WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?

 

 Assalamu alaikum,malam Inada

tambaya?

Idan mutum akayi masa aiki a ido

ance kar ruwa ya taba, toh idan zai yi salla

taimama zaiyi ko zai iya yin alwala ba tare da

sa ruwa a wajen ba? Allah ya saka da alkhairi

Amsa*

Wa alaikum assalam,

zai yi alwala

cikakkiya, sai ya tsallake wurin da yake da

ciwon, saboda Ka’idar : ﺍﻟﻤﻴﺴﻮﺭ ﻻ ﻳﺴﻘﻂ ﺑﺎﻟﻤﻌﺴﻮﺭ

Duk ibadar da za’a iya yin wani bangarenta, to

dukanta ba ya saraya, saboda rashin iya aikata

wani bangarenta, sai fa idan bangaren na ta,

shari’a ba ta bukatarsa, kamar mai olsar da zai

iya yin azumi zuwa azahar ya sare,

Allah ne mafi sani

21/12/2016

Dr. Jamilu Zarewa

 

128. TAMBAYA

HUKUNCIN DAGA HANNU A KOWACE KABBARA YAYIN SALLAN JANA'IZA

 

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkan mu da yaw da fatan an yi sallar juma'a lafia malamai ina neman qarin bayani Akan sallar janaza. Wai a dukkan kabbarorin sai an daga hannu ?ko ya abin yake بارك الله فيكم

Amsa

Wa'alaykumussalam,

Bayan an daga a kabbara ta farko, toh  sauran kabbarorin ba sai an daga ba, in kuma an daga shima babu laifi

Wallahu A'alam.

Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)

15 /07/2017

 

129. TAMBAYA

ZAN IYA YIN AZUMIN SITTU SHAWWAL ALHALI INA MATAFIYI?

 

Assalam alaykum. Mallan Dan Allah a taimaka a answer min tambaya na. Nice nayi bulaguro kuma INA sallan kasaru, shin Dan Allah mallan zan Iya yin azumin sitta Shawwal?

Amsa

Wa'alaykumussalam,

Azumin sitta shawwal nafila ne, tafiya bata hana yin ibada ta nafila shiyasa ma manzon Allah yakanyi sallar nafila akan abin hawan sa yayin da yake halin tafiya, tare da cewa Sallar farillar ma an yi rangwame ga matafiyi ya sallaci raka'a biyu don saukakawa gare shi, amma duk da haka baya hana manzon Allah yin nafila, don haka dai babu laifi kiyi idan bazaki wahala ba.

Wallahu A'alam.

Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)

16/07/2017

 

130. TAMBAYA

HALASCIN KARATUN AL-QUR'ANI ANA RUWAN SAMA

 

Asssalamu Alaikum, mallam shin yahalasta akaranta Al Qur'ani  yayinda ake ruwan sama.

Amsa

Wa'alaykumussalam.

Babu wani nassi daya haramta karanta alkur'ani yayin saukar ruwan sama, tare da haka kada amanta da yin azkaar lokacin saukar ruwan sama kamar yadda yazo a sunna, ga addu'ar :-

 

اللهم صيبا نافعا

Ko

 اللهم اجعله صيبا نافعا

 

Wallahu A'alam

Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)

14/07/2017

 

131. TAMBAYA

HUKUNCIN TABA JIKIN MACE

 

Assalamu Alaikum Allah ya karawa Malam Lafiya Tamabaya ta itace menene hukuncin taba jikin mace Dan yaji dadi kuma ba matarsa bace har yakai ga ya fidda Mani

AMSA

Wa'alaikium salam warahmatullah wabarkatuhu  saika je kayi wanka da istigfari idan ba matarka bace wallahu ta'ala a'a lam.

Allah shine mafi sani

Amsawa

DR. ABDALLAH USMAN GADON KAYA

 

132. TAMBAYA

MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI?

 

Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin  haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina,  shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka .

 Amsa :

Wa alaikum assalam To 'yar'uwa  mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi s.a.w. ya fada a  hadisin da  Muslim  ya rawaito mai lamba ta : 81.

Ga shi kuma aya : 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.

Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta :  222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta : 616 ya tabbatar da hakan.

Saidai  zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

6\3\2015

 

133. TAMBAYA

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?:                                                                         

 

Asslamau alaikum. Malam shin mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba, shin ta saku? 

Amsa:                                                                

 Wa alaikum assalam To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta saku koda ba ta ji ba,  yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman fiqhun musulunci:

-Duk wanda ba'a damu da yardarsa ba wajan tabbatuwar abu, ba'a damuwa da saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajan zartuwar saki,  haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajan tabbatuwarsa.                                                                                  Allah ne mafi sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

 

134. TAMBAYA

INASO NASAN YADDA AKE TAIMAMA

SHIN SALLAR NAFILA ITAMA ANA QABLI DA BA'ADI CIKIN TA

 

Dr tambaya ta itace yaya ake taimama sannan kuma sallar nafila kamar sallar asham shin itama anayi mata kabli da ba'adi kamar ydd ake yiwa sallar farilla ?

AMSA

Wassslam alaikum warahamatullah wabrakatuhu

To dan uwa dangane da yadda ake taimama shine mutum zai samu kasa mai tsarki ko wuri mai tsarki wanda yake da kasa a wajan kokuma kura sai mutum ya bude tafin hannayensa biyu ya shafi kasar sannan ya karkade, kasar daya debo ko tsakuwar, saiya shafi hannayensa biyu amma iya wuyan hannun sai

kuma ya shafa fuskarsa baki daya idan mutum yayi wanann ya aikata taimama ta sunnah sannan bugun kasar sau daya akeyi shine abinda hadisi ingantacce sahihi yace

Hadisin da yace ayi taimama bugu biyu bai inganta ba.

Dangane da bayani akan kabli ko ba'adi a sallar nafila babu shakka itama sallar nafila anayi mata kabli da ba'adi domin itama sallah ce

Allah shine mafi sani

Amsawa

Dr Abdallah Gadon kaya

18/07/2017

 

135. TAMBAYA

ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR AIDS?

 

Assalamu alaikum. Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?

Amsa                                                                                                                               Wa alaikum assalamu To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba'a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai  idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma'aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari kuma  ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fiqhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478   Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani.

Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game,Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za'a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

30/8/2015

 

136. TAMBAYA

HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA

Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.

 

AMSA:

An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.

Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:

An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami.

Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.

Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta. Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Amsawa:

Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 863.

Tattarawa:

Umar Shehu Zaria

 

137. TAMBAYA

INA KOKWANTO KO NA FITAR DA ISKA; YA SALLATA?

 

Assalamu alaikum

Malam nicenakefama da lallurata basir Amman bayayawaitasani hutu sainazowurin alwala ko sallah sai ya ring a sakani konkonto kamar inafidda hutu to Malam menene hukuncin alwalata da kuma sallah ta pls?

Amsa

Wa alaikumus salam zaki cigaba da alwalar ki ne saifa in kin samu yakinin fitar hutu (iska) wato kinji sauti kenan ko kuma kinji wari, toh a wannan hali saiki sake alwala, amma shi mujarradin kokonto baya warware alwala duk da dai akwai malaman da suke fahimtar cewa kokwanto na walwale alwala, amma dai maganar farko tafi karfi.

Wallahu A'alam

Amsawa

MALAM NURUDDEEN MUHAMMAD MUJAHEED

20/07/2017

 

138. TAMBAYA

MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA

 

Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.

AMSA:

An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.

Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:

An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami.

Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.

Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Amsawa:

Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 863.

Tattarawa:

Mal Umar Shehu Zaria

 

139. TAMBAYA

WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA?

 

Waye ya dace ya yi ma mace wanka idan ta mutu?, kuma shin ya halatta Mace kafira wanda ba Musulma ba ta yi mace Musulma wanka idan ta rasu?. Sannan da shigar da ita Kabari sharadi ne dole sai Makusantanta, ko kuwa kowane Musulmi zai iya shigar da ita kabari?. Akwai wasu mutane shin ya halatta a bar su, su shigar da mace kabarinta?.

AMSA:

Musantan mace su ne za su yi mata wanka kuma za a yi la'akari da wanda suka fi kusanci daga cikin wanda za su iya kyautata wankan. Kuma ya halatta a wakilta kowace mace wanda za ta iya kyautata wanke ta, koda kuwa ba makusanciyarta ba ce. Haka nan ya halatta miji ya wanke matan shi, ita ta wanke shi.

Dangane da Mace kafira ta wanke Musulma, wannan bai halatta ba, domin wanke mamaci ibada ce, kuma Ibadan wanda ba Musulmi ba, bata inganta.

Dangane da shigar da mace kabarinta, ya halatta wani daga cikin Musulmi ya shigar da ita koda ba makusancinta ba ne, matukar zai kyautata haka.

Amsawa: Al-Lajnatu al-Daa'imah Lil iftaa'i.

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 441.

Tattarawa:

Umar Shehu Zaria

 

140. TAMBAYA

YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?

 

Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.

Amsa

Wa alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude accout din da za'a  dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba  à cikin aya ta 275 a Suratul  Bakara da ayoyin da suka zo  bayanta.

Annabi SAW ya la'anci  mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a  hadisi ingantacce.

Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga  Allah da niyyar ba zai sake amsa  ba, tun da Allah ya Hana.

A zance mafi inganci zai iya amfani da  kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su  wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.

 wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu.

Allah ne  mafi  sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

27/07/2017


No comments: