61. TAMABAYA
Assalamu alaikum warahamatullahi wabara katuh.
Don Allah Malam inaso awarware min wannan rabon
gadon.
mamaci ne yabar mahafiyar sa,da yan uwa mata(uwa
daya uba daya),sai kuma yan uwa maza da mata(uwa daya uba kowa da nashi)da
kakar sa(uwar mahaifinsa).
Shin Malam wadannan zasu iya cinye gadon ko
yanuwan mahaifinsa (shakikai)zasu iya shigowa?
Allah yaba Malam ikon amsa tambaya ta.
AMSA
Wa alaikum assalam, Za'a
raba abin da ya bari gida:6, a bawa mahaifiyarsa kashi daya, 'yan'uwansa da suka hada uwa kuma kashi biyu, su raba daidai, ragowar kashi ukun sai a bawa 'yan'uwan nasa da suke uwa daya uba daya, duk namiji ya dau rabon mata biyu.Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr.
Jamilu Yusuf Zarewa
4/5/2017
62. TAMABAYA
ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?
Assalamu alaikum,
Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace
Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?
Amsa
Wa alaikumus salam,
Bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba
muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, ya kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai
musu mubaya'a, yana yi musu mubaya'a ne da Magana, kamar yadda ya tabbata a
hadisi.
Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga
Zina saboda yana tayar da sha'awa, Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a
aya ta 32 a suratul Isra'i, Zina tana daga cikin manyan zunuban da babu kamar
su bayan shirka da Allah.
Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai
kiyaye shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
05/05/2016.
63. TAMABAYA
Assalamu alaikum, Malam tambayata anan macece ta
rasu bata haihu ba tana da uwa araye da yaya namiji wanda suke uwa daya uba
daya da
Ƙane na miji wanda yake uwa kawai suka hada da ƙannai mata suma uwa kawai suka
hada Allah gafarta malam yaya rabon gado?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Za'a raba abin da ta bari gida :6.
A bawa mahaifiyarta kashi daya, 'yan uwanta da
suka hada uwa kashi biyu, sai su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da
mace, ragowar kashi ukun sai a bawa dan' uwanta da suke uwa daya uba daya.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
6/05/2017
64. TAMABAYA
SHIN ZAN IYA NEMAN SAKI DON MIJINA BAYA
HAIHUWA...!!*
Assslam alaika warahamatullah
Dr inada matsala kamar haka fatan za'a taimakamin
da amsa malam munyi aure da mijin yau kusan shekara goma muna tare amma Allah
bai bamu haihuwa ba sannan kuma dan uwa nane na jini gashi yanzu banason zama
dashi shin idan na nemi ya sawwakemin nayi laifi?
Kuma hakan na nuna cewa nakasa cinye jarrabawar da
Allah yayimin kenan ?
AMSA:
Wassslam Alaiki warahamatullah wabrakatuhu
To yar uwa shi asalin aure a musulunci yana daga
cikin manufofinsa shine samun zuri'a ma'ana yaduwa a samu al'ummah
Annabi s.a.w. yace kuyi aure Ku domin Ku samu
zuri'a kuma ku auri matayen da kukeso masu haihuwa ni zanyi alfahari da yawanku
wajan yawan al'umma ranar alkiyama
To yar uwa bazan ce dake ki rabu dashi ba
shawarata gareki shine kiyi hakuri ki yawaita addu'oi wata kila Allah ya baku
haihuwar nan gaba amma idan kinga shekarun da kukayi sunyi yawa sunyi miki yawa
ba zaki iya cigaba da zama dashi ba bakwa haihuwa zaki iya neman ya sawwake
miki amma badon kunyi fada ba kuyi rabuwar lami lafiya to babu laifi shima ya
kamata ya sawwake miki amma yar uwa ki sani cewa ba'asan matsalar daga gareki
take ba ko daga garesa ne kada sai bayan kun rabu a gane daga gareki ne
matsalar
Allah shine mafi sani
Dr Abdallah Gadon kaya
65. TAMABAYA
LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH?
Assalamu alaikum malam Dan Allah macece take fama
da yawan zuban yawu a bakinTa na laulayin ciki, Wanda yakai kafun nayi raka'a
daya ya cikamun baki sai na dan juya in zuba akan tsumma, sallan yayi ko bani
da halin juyawa kadan?
Amsa
Wa alaikum assalam. To 'Yar'uwa Annabi s.a.w. yana
cewa : "Waiwaye a sallah wani faucewa ne da Shaidan yake fauta daga sallar
bawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata : 718.
Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne
saboda hadisin da ya gabata.
Waiwaye yana halatta idan akwai bukata, saboda
akwai lokacin da sayyidina Abubakar ya
fara limanci, saboda Annabi s.a.w. baya nan, bayan Annabi s.a.w. ya dawo sai ya shigo masallaci,
sahabbai suna ganinsa sai suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar ya waiga
lokacin da ya ji tafi ya yi yawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 2544.
Malamai suna cewa : waiwayan da Abubakar ya yi
yana nuna hallacin yin waiwaye saboda bukata, tun da Annabi s.a.w. bai masa
inkari ba.
Don neman karin bayani duba : Fataawaa nurun
Aladdarb 9\225.
A bisa abin
da ya gabata, ya hallata ki dinga yin waiwaye saboda zubar da yawun da ya zama lalura, saidai duk
abin da aka halatta saboda bukata, ba'a so a wuce gwargwadonta .
Allah ne mafi sani .
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREAWA
19\4\2015
66. TAMABAYA
HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!
Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da
yake da janaba ya kira sallah?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa wasu daga cikin malamai suna cewa
tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce
wanda ya nuna hakan, don haka ya halatta ga mai janaba, da mai karamin kari su
yi kiran sallah, saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran
sallah, saboda fadin Annabi s.a.w " Ina kin na ambaci Allah alhali ba ni
da tsarki", kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta :16,
kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abi-dawud 1\16.
Don neman Karin bayani duba : Fathul-bary 3\113 da
Majmu'u fataawaa wa makaalatin mutanawwi'a 10\338.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
27/6/2015.
67. TAMABAYA
INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA HALATTA A
SHARI'ANCE ?
Assalamu alaikum malam Dan Allah ina tambaya.
Namiji ne yakeso ya qara aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar
ta riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi tana kusa sai
ya riqa avoiding amma data dan daga sai shima ya fara respinding ko
ya kira ta kuma idan asuba tayi sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan
Allah a Shari'ance yanada laifi ko ba shi da ? sannan matar zata iya neman ya
dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance ?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa yana da kyau ka san
cewa matar da kake nema aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka
dinga hira da ita ba, sai gwargwadon bukata.
Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana
daga cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya kirga jin dadin
zancen wacce ba muharrama ba daga cikin ayyukan da Allah ya hana.
Duk wanda yake yawan hira da matar da ba
muharramarsa ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin dadin
zancen matarsa ta halal.
Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon
bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku ku aikata katon sabo, yana
daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk hanyar da take kaiwa zuwa barna.
Zunubi shi ne abin da ya sosu a ranka kuma ka ji
tsoron kar mutane su yi tsinkayo, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim
mai lamba ta: 2553.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
4\1\2016.
68. TAMABAYA
MAGANIN QARFIN MAZA?
Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist
yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda
yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. Jameel imani da lafiya da
ilimi, gaskiya muna amfana
Amsa:
Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana
amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don
aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma'aurata
turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin
ka'idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum wadanda ba ibada ba ne
sun halatta, in har ba'a samu nassin da ya hana ba.
Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake
cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk
maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje
shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23/05/2016
69. TAMABAYA
MATATA TA YI BARI, AMMA JINI YANA DAUKEWA YA DAWO
Assalamu alaikum, Malam ga wata tambaya a
taimakama ,matata ta samu bari to abun bai gama fita ba tana zubar da jini sai
ya dauke kwana hudu sai ya dawo sai ta fara sallah sai ya dawo yanzu kusan wata
biyu kenan, shin za ta ci gaba da sallah tunda ya zama kamar jinin ciwo?.
Amsa
Wa'alaikumus Salaam. Idan mace ta yi barin ciki,
to babban abin da za ta lura da shi, shi ne abin da ta yi barin, idan halittar
Mutum ta bayyana ga abin da ta yi barin ta yadda za a iya ganin hannu ko kafa
da makamancin hakan, to wannan jinin ya zama jinin biki. Don haka sai ta bar
Sallah, Azumi, Saduwa da Miji da sauran dukkan abin da aka hana mai biki
aikatawa.
Amma idan abin da ta yi bari yana nan a matsayin
maniyyi ko gudan jini ko tsokar da babu halittar Mutum a jikinta, to wannan
jinin ba jinin biki ba ne, jinin ciwo ne, don haka za ta yi Sallah, Azumi, da
sauran duk abin da aka halatta ma mace mai tsarki sai dai duk lokacin da za ta
yi sallah, to sai ta yi tsarki ta sake yin Alwala.
Kuma hukuncin jini yana tabbata ne tun daga
lokacin da jinin ya fara fitowa koda bata kammala zubar cikin ko haihuwar ba,
domin Malaman Musulunci sun hadu akan cewa mace tana iya fara zubar da jinin
biki kafin haihuwa indai ta fara nakuda, sai dai Ibn Hazam shi ne yace jinin
biki ba zai fara zuwa ba sai mace ta haife dukkan abin da ke cikin cikinta,
amma dai tabbatacciyar magana shine: jinin biki yana fara zuba ne a lokacin da
Uwa (wadda take fadowa bayan haihuwa a hade da cibin jaririn) ta ballo daga
bangon mahaifa.
Allah ya bamu ikon ganewa da gyarawa.
Amsawa
Malam Ibrahim Jushi
16/05/2017.
70. TAMABAYA
DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR ŞAKI, IN YA GAMA
KARATUNSA?
Assalamu alaikum. Malam shin ya halasta mutum yaje
karatu wani kasan da Ba nasaba zaiyi shekara 5 sai yayi aure da niyan idan ya
gama makarantan nashi sai ya saketa ya koma gida?
Amsa:
Wa'alaikum assalam, wasu malaman sun halatta
hakan, sai dai zance mafi inganci shi ne rashin halarcinsa, saboda ya yi kama
da auran mutu'a, sannan kuma hakan ya sabawa wasu daga cikin manufofin
aure.
Kamar dawwamammar soyayya da kuma debe kewa, Aya
ta 21 a suratu Arrum ta tabbatar da cewa: an shar'anta aure ne dön ka nutsu da
matar da zaka aura, wannan manufar ta goce a aure da niyyar saki.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
12/05/2016
70. TAMABAYA
Da wanda nake so da wanda mahaifiyata ta ke so
wazan aura?
Malam ina neman shawara inada saurayi me ilimin
addini dana buko amma mamana tana sona aure wani mutum mara ilimi kuma ni bana
sansa toh malam wazan zaba aciki?
ASSALAMU ALAIKHUM
Amsa
Wa'alaiku mussalam, Hadisi ya tabbata wani mutum
yazo wajan Annbi S.A.W yace dashi: cikin mutanan duniyannan wanene ya kamta
nayi mishi biyayya sai Annabi S.A.W yace dashi: mahaifiyarka ya sake cewa
sannan wa? Annabi S.A.W yasake cewa dashi mahaifiyarka, yasake cewa sannan wa?
Annabi S.A.W yasake cewa dashi mahaifiyarka, ya sake cewa sannan wa Annabi
S.A.W yace mahaifinka.
Muhimmancin hakkin uwa bayan hakkin Allah S.A.W da
na Annabi S.A.W babu wanda yafi shi girma daga ita sannan mahaifi, dan haka
wajibine bin mahaifiya.
Shawara
Ki lallabata har ta gamsu kiyi kokari ta wajan yi
mata biyayya da kuma bin kawayanta da yan uwanta cikin ladabi wajan su saka
baki dan shawo kanta har Allah yasa ta gamsu ta baki wanda kike so.
Muna Addu'a Allah ya zaba miki wanda yafi Alkhairi.
71. TAMABAYA
ZAN IYA DAUKAN AZUMIN NAFILA A JAJIBARIN RAMADAN?
Assalamu alaikum
Menene hukuncin wanda keyin azumin litinin da
alhamis sai azumin Ramadan ya kama ranan
juma'ah to ya halasta yayi azumin ranan
alhamis din Alhalin washe Gari azumin Ramadan?
Amsa
Wa alaikum assalam,
In ya saba yi babu laifi ya azumta, saboda hadisin
da Annabi S.A.W. yake cewa: " Kada ku gabaci Ramdhana da azumin yini daya
ko biyu sai Fa in azumin da mutum ya saba yi ne, kamar yadda Bukhari ya rawaito
hakan a hadisi mai lamba ta: 1914 da kuma Muslim a hadisi mai lamba: 1082.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
17/05 /2017
72. TAMABAYA
ZAN IYA AURAN 'YAR KANWAR MATATA?
Assalamu alaikum Malam, Ya halatta mutum ya auri
yar qanwar matarsa?
Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta ya aure ta, bayan
ya saki matarsa, amma bai halatta ya hada su ba saboda innarta ce, Annabi S.A.W
yana cewa: "Ba'a a hada mace da goggonta, ba'a hada mace da innarta a
auratayya, saboda in kuka yi haka, za ku lallata zumunci ku" kamar ayadda
ibnu Hibban ya rawaito.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20\5\2016
73. TAMABAYA
SANYA ZOBEN AZURFA A DAN YATSAN DAMA?
Assalamu Alaikum Malam ga wata tambaya nan kamar
haka:Assalam da fatan kana lpy! pls ga tambayana menene hukuncin sa AZURFA ZOBE
a hanun dama shin akwai wata illa ne koh kuma manzon Allah baisaba???
Amsa
Walaikum assalam.To dan'uwa ya halatta a sanya
zoben azurfa a karamin dan yatsan hagu da kuma dama, Nawawy ya hakaito Ijma'in
kasancewar hakan Sunna, saidai akwai hadisi mai lamba ta :2078 a Sahihi Muslim
wanda yake nuna haramcin sanya zobe a dan yatsan tsakiya da wacce take binta,
wasu malaman kuma sun dauki hanin a matsayin karhanci ba haramun ba.
Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawey
4\340.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28\12\2015
74. TAMABAYA
DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA?
Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam in nada tanbaya,
Malam mace ce tayi ciki batare da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi sai Allah
ya mata rasuwa toh malam yaron zai ci gadonta ?.
Amsa
Wa alaikum assalam,
idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga
baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a
cikin suratun Nisa'i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan zina
kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.
Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi
yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.
Allah ne
mafi sani
Don neman karin bayani duba : Sunanu Attirmizy
hadisi mai lamba ta: 2113 da kuma Tabyinul haka'ik 6\214.
Dr. Jamilu Zarewa
25\5\2016
75. TAMABAYA
HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)
Assalmu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da imani,
malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a musulunci
Amsa
Wa alaikum assalam,
To 'yar'uwa
Babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da
al'aura har maniyyi ya fito, duk hadisan da suka zo ba su inganta ba.
Saidai wasu malaman sun haramta auran hannu saboda
aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan bukatar sha'awa ta hanyar matar
aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan
bukata ta hanyar su.
Yin wasa da
al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance, saidai yana
daga cikin ka'idojin shari'a ; idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda
za'a yi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa
Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta
auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.
Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai
barnar dake cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan
tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi 'ya'ya gantalallu, marasa
asali, wannan ya sa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu
sharudan da suka gabata
Don neman
Karin bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu'ul fataawaa 34\146>
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23\1\2016
76. TAMABAYA
SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?
Assalamu alaikum.Malam yaya zakkar ma'aikaci ya
kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa
zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin
shekara ta zagayo sun kare
Amsa
Wa alàikum assalam.To dan'uwa, hukuncin wannan
albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su
shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta
zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga
mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara
to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba,
to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
Saidai yana daga cikin dabarun da sharia ta
haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka
mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa
Allah.
Allah ne ma fi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
14/5/2014
77. TAMABAYA
HUKUNCIN DILLANCI DA HOTUNAN 'YAMMATA
Assalamu alaikum. Malam menene hukuncin 'yan matan
da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure ?
AMSA
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya haramta
kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka
kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda
Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami
damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU
DAWUD
Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata
mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin
hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a
kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya
baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka
mutum zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya
fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki
:
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar,
bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta
yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta
ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda
yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton
na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya
wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin
aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna
ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne ma fi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/5/2014
78. TAMABAYA
KO ZAN IYA BAWA KANNENA ZAKKA?
Assalamu alaikum,
Malam ansha ruwa lafi Malam ko ya halatta imba
ma'aikatana zakka da kannena?.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Wa alaikum assalam. To dan'uwa ba ya halatta
musulmi ya bada zakka ga wadanda wajibi ne akansa ya ciyar da su; kamar iyaye
maza da mata, kakanni; maza da mata, da kuma 'ya'ya da 'ya'yan 'ya'ya ; saboda
bada zakka ga wadannan zai sauke masa nauyin ciyar da su da ya ke wajibi
akansa; daga nan kuma sai amfanin bada zakkar ta dawo kansa.
Amma kanne kuwa, to ciyar da su bai wajaba akanka
ba, don haka ya halatta ka ba su zakka, haka nan ma'aikatanka.
Sannan daga cikin ka'idojin da malamai suke fada a
wannan babin shi ne duk mutumin da idan ka mutu ba zai gaje ka ba, to ya
halatta ka ba shi zakka, ka ga kuwa
kanne, ba sa gado mutukar akwai 'ya'ya.
Duba fiqhul-muyassar shafi na : 145
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
08/07/2014
79. TAMABAYA
MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA A
WATAN RAMADANA?
Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin meye
hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin
azumi,
amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito,
shin yaya
matsayin azumin su yake.? Nagode
Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da
mijinta su
jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan
Ramadhana, a zuminsu kuma ya inganta, saboda
Annabi
S.a.w yakan yi haka da matansa, kamar yadda
iyalansa
A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma
Muslim
ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba
ta: 1874.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/05/2016
80. TAMABAYA
BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA
HAILA?
Assalamu alaikum,
Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na
son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na
sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata
ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila
ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta
saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta
1952. Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma
barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan
yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa,
musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila,
kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.Don neman karin bayani, duba :
Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
22\6\2015
No comments:
Post a Comment