201. TAMBAYA
HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!
Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake
da janaba ya kira sallah?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan,
don haka ya halatta ga mai janaba, da mai karamin kari su yi kiran sallah, saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran sallah, saboda fadin Annabi s.a.w " Ina kin na ambaci Allah alhali ba ni da tsarki", kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta :16, kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abi-dawud 1\16.Don neman Karin bayani duba : Fathul-bary 3\113 da
Majmu'u fataawaa wa makaalatin mutanawwi'a 10\338.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
27/6/2015.
202. TAMBAYA
INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA HALATTA A
SHARI'ANCE?
Assalamu alaikum malam Dan Allah ina tambaya.
Namiji ne yakeso ya qara aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar
ta riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi tana kusa sai
ya riqa avoiding amma data dan daga sai shima ya fara respindingو
ko
ya kira ta kuma idan asuba tayi sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan
Allah a Shari'ance yanada laifi ko ba shi da ? sannan matar zata iya neman ya
dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance ?
Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa yana da kyau ka san
cewa matar da kake nema aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka
dinga hira da ita ba, sai gwargwadon bukata.
Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana
daga cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya kirga jin dadin
zancen wacce ba muharrama ba daga cikin ayyukan da Allah ya hana.
Duk wanda yake yawan hira da matar da ba
muharramarsa ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin dadin
zancen matarsa ta halal.
Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon
bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku ku aikata katon sabo, yana
daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk hanyar da take kaiwa zuwa barna.
Zunubi shi ne abin da ya sosu a ranka kuma ka ji
tsoron kar mutane su yi tsinkayo, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim
mai lamba ta: 2553.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
4\1\2016.
203. TAMBAYA
MAGANIN QARFIN MAZA?
Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist
yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda
yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. Jameel imani da lafiya da
ilimi, gaskiya muna amfana
Amsa
Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana
amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don
aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma'aurata
turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin
ka'idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum wadanda ba ibada ba ne
sun halatta, in har ba'a samu nassin da ya hana ba.
Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake
cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk
maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje
shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23/05/2016
204. TAMBAYA
MATATA TA YI BARI, AMMA JINI YANA DAUKEWA YA DAWO
Assalamu alaikum, Malam ga wata tambaya a
taimakama ,matata ta samu bari to abun bai gama fita ba tana zubar da jini sai
ya dauke kwana hudu sai ya dawo sai ta fara sallah sai ya dawo yanzu kusan wata
biyu kenan, shin za ta ci gaba da sallah tunda ya zama kamar jinin ciwo?.
Amsa:
Wa'alaikumus Salaam. Idan mace ta yi barin ciki,
to babban abin da za ta lura da shi, shi ne abin da ta yi barin, idan halittar
Mutum ta bayyana ga abin da ta yi barin ta yadda za a iya ganin hannu ko kafa
da makamancin hakan, to wannan jinin ya zama jinin biki. Don haka sai ta bar
Sallah, Azumi, Saduwa da Miji da sauran dukkan abin da aka hana mai biki
aikatawa.
Amma idan abin da ta yi bari yana nan a matsayin
maniyyi ko gudan jini ko tsokar da babu halittar Mutum a jikinta, to wannan
jinin ba jinin biki ba ne, jinin ciwo ne, don haka za ta yi Sallah, Azumi, da
sauran duk abin da aka halatta ma mace mai tsarki sai dai duk lokacin da za ta
yi sallah, to sai ta yi tsarki ta sake yin Alwala.
Kuma hukuncin jini yana tabbata ne tun daga
lokacin da jinin ya fara fitowa koda bata kammala zubar cikin ko haihuwar ba,
domin Malaman Musulunci sun hadu akan cewa mace tana iya fara zubar da jinin
biki kafin haihuwa indai ta fara nakuda, sai dai Ibn Hazam shi ne yace jinin
biki ba zai fara zuwa ba sai mace ta haife dukkan abin da ke cikin cikinta,
amma dai tabbatacciyar magana shine: jinin biki yana fara zuba ne a lokacin da
Uwa (wadda take fadowa bayan haihuwa a hade da cibin jaririn) ta ballo daga
bangon mahaifa.
Allah ya bamu ikon ganewa da gyarawa.
Amsawa
Malam Ibrahim Jushi
16/05/2017.
205. TAMBAYA
DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR ŞAKI, IN YA GAMA
KARATUNSA?
Assalamu alaikum. Malam shin ya halasta mutum yaje
karatu wani kasan da Ba nasaba zaiyi shekara 5 sai yayi aure da niyan idan ya
gama makarantan nashi sai ya saketa ya koma gida?
Amsa
Wa'alaikum assalam, wasu malaman sun halatta
hakan, sai dai zance mafi inganci shi ne rashin halarcinsa, saboda ya yi kama
da auran mutu'a, sannan kuma hakan ya sabawa wasu daga cikin manufofin
aure.
Kamar dawwamammar soyayya da kuma debe kewa, Aya
ta 21 a suratu Arrum ta tabbatar da cewa: an shar'anta aure ne dön ka nutsu da
matar da zaka aura, wannan manufar ta goce a aure da niyyar saki.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
12/05/2016
206. TAMBAYA
Malam ina neman shawara
Malam ina neman shawara inada saurayi me ilimin
addini dana buko amma mamana tana sona aure wani mutum mara ilimi kuma ni bana
sansa toh malam wazan zaba aciki?
ASSALAMU ALAIKHUM
Amsa
Wa'alaiku mussalam, Hadisi ya tabbata wani mutum
yazo wajan Annbi S.A.W yace dashi: cikin mutanan duniyannan wanene ya kamta
nayi mishi biyayya sai Annabi S.A.W yace dashi: mahaifiyarka ya sake cewa
sannan wa? Annabi S.A.W yasake cewa dashi mahaifiyarka, yasake cewa sannan wa?
Annabi S.A.W yasake cewa dashi mahaifiyarka, ya sake cewa sannan wa Annabi
S.A.W yace mahaifinka.
Muhimmancin hakkin uwa bayan hakkin Allah S.A.W da
na Annabi S.A.W babu wanda yafi shi girma daga ita sannan mahaifi, dan haka
wajibine bin mahaifiya.
SHAWARA
Ki lallabata har ta gamsu kiyi kokari ta wajan yi
mata biyayya da kuma bin kawayanta da yan uwanta cikin ladabi wajan su saka
baki dan shawo kanta har Allah yasa ta gamsu ta baki wanda kike so.
Muna Addu'a Allah ya zaba miki wanda yafi
Alkhairi.
Rubutawa:- Abubakar Eka.
207. TAMBAYA
ZAN IYA DAUKAN AZUMIN NAFILA A JAJIBARIN RAMADAN?
Assalamu
alaikum
Menene hukuncin wanda keyin azumin litinin da
alhamis sai azumin Ramadan ya kama ranan
juma'ah to ya halasta yayi azumin ranan
alhamis din Alhalin washe Gari azumin Ramadan?
Amsa
Wa alaikum assalam,
In ya saba yi babu laifi ya azumta, saboda hadisin
da Annabi S.A.W. yake cewa: " Kada ku gabaci Ramdhana da azumin yini daya
ko biyu sai Fa in azumin da mutum ya saba yi ne, kamar yadda Bukhari ya rawaito
hakan a hadisi mai lamba ta: 1914 da kuma Muslim a hadisi mai lamba: 1082.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
17/05 /2017
208. TAMBAYA
ZAN IYA AURAN 'YAR KANWAR MATATA?
Assalamu alaikum Malam, Ya halatta mutum ya auri
yar qanwar matarsa?
Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta ya aure ta, bayan
ya saki matarsa, amma bai halatta ya hada su ba saboda innarta ce, Annabi S.A.W
yana cewa: "Ba'a a hada mace da goggonta, ba'a hada mace da innarta a
auratayya, saboda in kuka yi haka, za ku lallata zumunci ku" kamar ayadda
ibnu Hibban ya rawaito.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20\5\2016
208. TAMBAYA
SANYA ZOBEN AZURFA A DAN YATSAN DAMA?
Assalamu Alaikum Malam ga wata tambaya nan kamar
haka:Assalam da fatan kana lpy! pls ga tambayana menene hukuncin sa AZURFA ZOBE
a hanun dama shin akwai wata illa ne koh kuma manzon Allah baisaba???
Amsa
Walaikum assalam.To dan'uwa ya halatta a
sanya zoben azurfa a karamin dan yatsan hagu da kuma dama, Nawawy ya hakaito
Ijma'in kasancewar hakan Sunna, saidai akwai hadisi mai lamba ta :2078 a Sahihi
Muslim wanda yake nuna haramcin sanya zobe a dan yatsan tsakiya da wacce take
binta, wasu malaman kuma sun dauki hanin a matsayin karhanci ba haramun ba.
Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawey
4\340.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28\12\2015
209. TAMBAYA
DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA?
Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam in nada
tanbaya, Malam mace ce tayi ciki batare
da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi sai Allah ya mata rasuwa toh malam yaron
zai ci gadonta ?.
Amsa
Wa alaikum assalam,
idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga
baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a
cikin suratun Nisa'i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan zina
kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.
Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi
yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.
Allah ne
mafi sani
Don neman karin bayani duba : Sunanu Attirmizy
hadisi mai lamba ta: 2113 da kuma Tabyinul haka'ik 6\214.
Dr. Jamilu Zarewa
25\5\2016
210. TAMBAYA
HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)?
Assalmu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da
imani, malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a musulunci.
Amsa
Wa alaikum assalam,
To 'yar'uwa
Babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da
al'aura har maniyyi ya fito, duk hadisan da suka zo ba su inganta ba.
Saidai wasu malaman sun haramta auran hannu saboda
aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan bukatar sha'awa ta hanyar matar
aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan
bukata ta hanyar su.
Yin wasa da
al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance, saidai yana
daga cikin ka'idojin shari'a ; idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda
za'a yi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa
Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta
auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.
Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai
barnar dake cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan
tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi 'ya'ya gantalallu, marasa
asali, wannan ya sa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu
sharudan da suka gabata.
Don neman
Karin bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu'ul fataawaa 34\146>
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23\1\2016
211. TAMBAYA
SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?
Assalamu alaikum.Malam yaya zakkar ma'aikaci ya
kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa
zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin
shekara ta zagayo sun kare.
Amsa
Wa alàikum assalam.To dan'uwa, hukuncin wannan
albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su
shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabi ne ya ke wajabta
zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga
mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara
to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba,
to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
Saidai yana daga cikin dabarun da sharia ta
haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka
mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa
Allah.
Allah ne ma fi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
14/5/2014
212. TAMBAYA
HUKUNCIN DILLANCI DA HOTUNAN 'YAMMATA
Assalamu alaikum. Malam menene hukuncin 'yan matan
da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure?
AMSA
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya haramta
kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka
kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda
Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami
damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD
Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata
mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin
hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a
kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya
baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka
mutum zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya
fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki
:
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar,
bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta
yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta
ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda
yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton
na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya
wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin
aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna
ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne ma fi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/5/2014
213. TAMBAYA
KO ZAN IYA BAWA KANNENA ZAKKA?
Assalamu alaikum,
Malam ansha ruwa lafiya? Malam ko ya halatta imba
ma'aikatana zakka?da kannena?.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Wa alaikum assalam. To dan'uwa ba ya halatta
musulmi ya bada zakka ga wadanda wajibi ne akansa ya ciyar da su; kamar iyaye
maza da mata, kakanni; maza da mata, da kuma 'ya'ya da 'ya'yan 'ya'ya ; saboda
bada zakka ga wadannan zai sauke masa nauyin ciyar da su da ya ke wajibi
akansa; daga nan kuma sai amfanin bada zakkar ta dawo kansa.
Amma kanne kuwa, to ciyar da su bai wajaba akanka
ba, don haka ya halatta ka ba su zakka, haka nan ma'aikatanka.
Sannan daga cikin ka'idojin da malamai suke fada a
wannan babin shi ne duk mutumin da idan ka mutu ba zai gaje ka ba, to ya
halatta ka ba shi zakka, ka ga kuwa
kanne, ba sa gado mutukar akwai 'ya'ya.
Duba fiqhul-muyassar shafi na : 145
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
08/07/2014
214. TAMBAYA
MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA, A
WATAN RAMADANA?
Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin meye
hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin
azumi,
amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito,
shin yaya
matsayin azumin su yake.? Nagode
Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da
mijinta su
jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan
Ramadhana, a zuminsu kuma ya inganta, saboda
Annabi
S.a.w yakan yi haka da matansa, kamar yadda
iyalansa
A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma
Muslim
ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba
ta: 1874.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/05/2016
215. TAMBAYA
BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA
HAILA?
Assalamu alaikum,
Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na
son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na
sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata
ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila
ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta
saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya
ta 1952. Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma
barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan
yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa,
musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila,
kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.Don neman karin bayani, duba :
Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
22\6\2015
216. TAMBAYA
SHIN AMAI NA KARYA AZUMI?
Assalamu alaykum'm Malam Dan Allah inada
tambaya,nice ina azumi se nayi irin Dan aman nan wanda ake ce masa aman
kaji,Dan kadanne ba wae amai da yawaba,to malam ya matsayin azumi na naji ance
amai yana karya azumi.Allah y qarawa malam Lpy.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Duk aman da akayi kadan ko mai yawa ba da gangan
ba toh baya karya azumi amma idan an kakaro shi ne to azumi ya karye, Don fadar
manzon Allah cikin hadisin Abu huraira wanda ke cikin sunan na imam tirmizi
720.
Don haka dai babu sabani tsakanin malamai cewa duk
wanda amai ya rinjaye shi toh azumin sa na nan amma wanda ya kago amai da kansa
to azumin sa ya baci, aduba:
Al'Mugni 4/368
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
29/05/2017
217. TAMBAYA
SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU
Assalamu alaikum,
Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan
"KUDRA da kuma SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa, Wannan yana daga cikin mas'aloli masu
mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwka game da haka :
Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar
ruwan ciwo, ya fito daga gabanta.
Kudra kuwa na nufin : ruwa ya ringa fitowa daga
farjin mace, wanda kalarsa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da baki wato
kamar ruwa gurbatacce,
Dangane da hukuncinsu kuwa : idan daya daga
cikinsu ya kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila kafin ta sami
tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan kuma bayan tsarki ne to ba
haila ba ne saboda fadin Ummu adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra
bayan tsarki a cikin haila) Abudawud ya rawaito shi da sanadi mai inganci,
A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin
da suke sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan da yake
kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa
ya fito, ta yadda za mu yi amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki,
ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila ba, hadisin
A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana cikin haila ta yadda za ta kirga
da su.
ALLAH ne mafi sani.
5/12/2014
Dr. Jamilu Zarewa
218. TAMBAYA
YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YA YI
KAFFARA?
Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne
ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani
auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.
Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga Malam.
Amsa
Wa alaikum assalam, Auransa na biyun ya inganta
saboda ba su da alaka da juna.
Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku
ne, to wancan ziharin ya warware, amma in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai
halatta ya taba ta har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah
ya fada a cikin Al-Mugni.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2017.
219. TAMBAYA
TANA AZUMI SAI MIJINTA YA SUMBACETA?
Malam macece tayi kitso alhalin tana azumi sai
mijinta yaga kitson ya basa sha'awa saiya sumbacesa ita kuma take sha'awa tazo
mata harta jika pant dinta
Amsa
Wa akaikumus salamTo yar uwa da farko dai anyi
wasa da azumi kwarai da gaske kuma ba daidai bane kina azumi ki bari mijinki ya
sumbaceki ta yadda har zaki fitar da wani abu dazai bata miki azumi' wannan
akwai ganganci a ciki.
Amma shi azumin nafila dama mai shi yanada yan'cin
ya karyashi koya cigaba Annabi S.A.W ya fada cikin hadisi sahihi mai azumin
nafila shine sarkin kansa idan yaga dama ya karya manzon Allah s.a.w. ya bada
wannan damar.
Malamai suna cewa fitar maziyyi idan har maziyyine
ya fita karamar sha'awa kenan zance mafi inganci baya karya azumi amma idan
maniyyi ne ya fita to azumi ya karye shikenan idan na nafila ne bakida lada
idan kuma farilla ne akwai kaffara akansu bisa kaulin malamai amma wasu malaman
sukace sai anyi jama'i kaffara take wajabta idan nafilane shikenan idan kuma na
farillah ne saiki rama guda daya wannan shine zance mafi inganci.
Allah shine mafi sani.
Amsawa
DR. ABDALLAH GADON KAYA
220. TAMBAYA
INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADHANA SAI ALFIJIR
YA KETO!
Assalamu alaikum Malam muna cikin saduwa da mijina
a cikin wannan wata, sai muka ji kiran sallar asalatu, me ye hukuncin azuminmu?
Amsa
Wa alàikum To 'yar'uwa mutukar kuna jin kiran
sallar, kun maza da sauri, kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan,
amma in har kuka ci gaba, da yi ko da na second daya ne, to azuminku ya karye,
kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki ya
yi, to zai yi kaffara shi kadai.
Duba Almugni: 3\65.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
18/06/2015
No comments:
Post a Comment