261. TAMBAYA
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA Mijina BA LAFIYA?
Assalamu Alaikum, Dr macece mijinta
ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya
zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani
dogon tunani na sha’awaba, ya matsayin
ibadarta yake ?
Amsa
Wa'alaikumus salam.
To gaskiya abin da yake dai-dai shi ne :
ya nemi
magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin
manufofin aure, kadange ma’aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan
ya tabbatar. Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da
saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya
wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya
azurta kowa dağa falalarsa.
Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa
ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata
ta hanyar wannan sababin ? ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun
da ya fita ne ta hanyar jin dadi.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
21/12/2016
262. TAMBAYA
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA Mijina BA LAFIYA?
Assalamu Alaikum, Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana
yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha’awaba, ya matsayinibadarta yake ?
Amsa
Wa'alaikumus salam.
To gaskiya abin da yake dai-dai shi ne :
ya nemi
magani, in kuma bai
samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga
cikin manufofin aure, kadange ma’aurata daga
fadawa haramun, kamar yadda shararren
hadisinnan ya tabbatar.
Yawan fitar
maniyyi zai
iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin
sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba,
saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin
neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya
rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.
Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa
ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama
mazinata ta hanyar wannan sababin ? ya
wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita,
tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
21/12/2016
263. TAMBAYA
WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?
Assalamu
alaikum,malam Inada tambaya?
Idan mutum akayi masa aiki a ido ance kar ruwa ya
taba, toh idan zai yi salla taimama zaiyi ko zai iya yin alwala ba tare da sa
ruwa a wajen ba? Allah ya saka da alkhairi.
Amsa
Wa alaikum assalam,
zai yi alwala
cikakkiya, sai ya tsallake wurin da yake da ciwon,
saboda Ka’idar : ﺍﻟﻤﻴﺴﻮﺭ ﻻ ﻳﺴﻘﻂ
ﺑﺎﻟﻤﻌﺴﻮﺭ
Duk ibadar da za’a iya yin wani bangarenta, to
dukanta ba ya saraya, saboda rashin iya aikata
wani bangarenta, sai fa idan bangaren na ta,
shari’a ba ta bukatarsa, kamar mai olsar da zai
iya yin azumi zuwa azahar ya sare,
Allah ne mafi sani
21/12/2016
Dr. Jamilu Zarewa
264. TAMBAYA
HUKUNCIN DAGA HANNU A KOWACE KABBARA YAYIN SALLAN
JANA'IZA
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkan mu da yaw
da fatan an yi sallar juma'a lafia malamai ina neman qarin bayani Akan sallar
janaza. Wai a dukkan kabbarorin sai an daga hannu ?ko ya abin yake بارك
الله فيكم
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Bayan an daga a kabbara ta farko, toh sauran kabbarorin ba sai an daga ba, in kuma
an daga shima babu laifi
Wallahu A'alam.
Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)
15 /07/2017
265. TAMBAYA
ZAN IYA YIN AZUMIN SITTU SHAWWAL ALHALI INA
MATAFIYI?
Assalam alaykum. Mallan Dan Allah a taimaka a
answer min tambaya na. Nice nayi bulaguro kuma INA sallan kasaru, shin Dan
Allah mallan zan Iya yin azumin sitta Shawwal?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Azumin sitta shawwal nafila ne, tafiya bata hana
yin ibada ta nafila shiyasa ma manzon Allah yakanyi sallar nafila akan abin
hawan sa yayin da yake halin tafiya, tare da cewa Sallar farillar ma an yi
rangwame ga matafiyi ya sallaci raka'a biyu don saukakawa gare shi, amma duk da
haka baya hana manzon Allah yin nafila, don haka dai babu laifi kiyi idan
bazaki wahala ba.
Wallahu A'alam.
Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)
16/07/2017
266. TAMBAYA
HALASCIN KARATUN AL-QUR'ANI ANA RUWAN SAMA
Asssalamu Alaikum, mallam shin yahalasta akaranta
Al Qur'ani yayinda ake ruwan sama.
Amsa
Wa'alaykumussalam.
Babu wani nassi daya haramta karanta alkur'ani
yayin saukar ruwan sama, tare da haka kada amanta da yin azkaar lokacin saukar
ruwan sama kamar yadda yazo a sunna, ga addu'ar :-
اللهم صيبا نافعا
Ko
اللهم اجعله صيبا
نافعا
Wallahu A'alam
Malam Nuraddeen Muhammad (Mujaheed)
14/07/2017
267. TAMBAYA
HUKUNCIN TABA JIKIN MACE
Assalamu Alaikum Allah ya karawa Malam Lafiya
Tamabaya ta itace menene hukuncin taba jikin mace Dan yaji dadi kuma ba matarsa
bace har yakai ga ya fidda Mani.
AMSA
Wa'alaikium salam warahmatullah wabarkatuhu saika je kayi wanka da istigfari idan ba
matarka bace wallahu ta'ala a'a lam.
Allah shine mafi sani
Amsawa
Dr.ABDALLAH USMAN GADON KAYA
268. TAMBAYA
MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI?
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara
basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai
damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta
mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da
ita tana jinin haila, kuma ta fada masa
haramun ne amma ya ki ya daina, shin
malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama
da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka .
Amsa :
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za
ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi
inganci, kamar yadda Annabi s.a.w. ya fada a
hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta : 81.
Ga shi kuma aya : 10 a suratul Mumtahanah ta
tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai
matsala a addinan ce.
Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul
Bakara aya ta : 222, Saduwa da mace da
rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta :
616 ya tabbatar da hakan.
Saidai
zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki
ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.
Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy
2\69.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
6\3\2015
269. TAMBAYA
FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?:
Asslamau alaikum. Malam shin mutum ya furta saki
ga matarsa ba ta jiba, shin ta saku?
Amsa:
Wa alaikum
assalam To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi daga cikin
sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta saku koda ba ta ji ba, yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman
fiqhun musulunci:
-Duk wanda ba'a damu da yardarsa ba wajan
tabbatuwar abu, ba'a damuwa da saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajan
zartuwar saki, haka ma saninta an yi
sakın ba sharadi ba ne wajan tabbatuwarsa Allah ne
mafi sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
270. TAMBAYA
NASAN YADDA AKE TAIMAMA
SHIN SALLAR NAFILA ITAMA ANA QABLI DA BA'ADI CIKIN
TA
Dr tambaya ta itace yaya ake taimama sannan kuma
sallar nafila kamar sallar asham shin itama anayi mata kabli da ba'adi kamar
ydd ake yiwa sallar farilla ?
AMSA
Wassslam alaikum warahamatullah wabrakatuhu
To dan uwa dangane da yadda ake taimama shine
mutum zai samu kasa mai tsarki ko wuri mai tsarki wanda yake da kasa a wajan
kokuma kura sai mutum ya bude tafin hannayensa biyu ya shafi kasar sannan ya
karkade, kasar daya debo ko tsakuwar, saiya shafi hannayensa biyu amma iya
wuyan hannun sai
kuma ya shafa fuskarsa baki daya idan mutum yayi
wanann ya aikata taimama ta sunnah sannan bugun kasar sau daya akeyi shine
abinda hadisi ingantacce sahihi yace
Hadisin da yace ayi taimama bugu biyu bai inganta
ba.
Dangane da bayani akan kabli ko ba'adi a sallar
nafila babu shakka itama sallar nafila anayi mata kabli da ba'adi domin itama
sallah ce
Allah shine mafi sani
Amsawa
Dr. Abdallah Gadon kaya
18/07/2017
271. TAMBAYA
ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR AIDS?
Assalamu alaikum. Malam matata ta yi rashin
lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni
amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da
ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman
shawara ?
Amsa Wa alaikum
assalamu To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba'a
tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta
saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma'aurata ko su duka,
za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa
cuta ce mai hadari kuma ana daukarta,
don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fiqhu sun
halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil
Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478 Cutar
Sida kuma tafi kuturta tsanani.
Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan
an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau da kai daga tunkude
cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game,Cigaba da zama da ita zai
jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za'a waiga zuwa
damuwarta ba a nan wurin.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
30/8/2015
272. TAMBAYA
HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da
Muharrami ba?.
AMSA:
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami
wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.
Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana
mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:
An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu
Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Kada mace ta
yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami.
Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu,
Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya
yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.
Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu
Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Ba Ya halatta ga
mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta. Bukhari
da Muslim ne suka riwaito.
Amsawa:
Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah
A duba littafin فتاوى
المرأة المسلمة shafi na 863.
Tattarawa:Umar Shehu Zaria_
273. TAMBAYA
INA KOKWANTO KO NA FITAR DA ISKA; YA SALLATA?
Assalamu alaikum
Malam nicenakefama da lallurata basir Amman
bayayawaitasani hutu sainazowurin alwala ko sallah sai ya ring a sakani
konkonto kamar inafidda hutu to Malam menene hukuncin alwalata da kuma sallah
ta pls?
Amsa
Wa alaikumus salam zaki cigaba da alwalar ki ne
saifa in kin samu yakinin fitar hutu (iska) wato kinji sauti kenan ko kuma
kinji wari, toh a wannan hali saiki sake alwala, amma shi mujarradin kokonto
baya warware alwala duk da dai akwai malaman da suke fahimtar cewa kokwanto na
walwale alwala, amma dai maganar farko tafi karfi.
Wallahu A'alam
Amsawa
Malam NURUDDEEN MUHAMMAD MUJAHEED
20/07/2017
274. TAMBAYA
HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da
Muharrami ba?.
AMSA:
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami
wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.
Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana
mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:
An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu
Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Kada mace ta
yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami.
Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu,
Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya
yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.
Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu
Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Ba Ya halatta ga
mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta. Bukhari
da Muslim ne suka riwaito.
Amsawa:
Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah
A duba littafin فتاوى
المرأة المسلمة shafi na 863.
Tattarawa:Mal Umar Shehu Zaria
275. TAMBAYA
WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA?
Waye ya dace ya yi ma mace wanka idan ta mutu?,
kuma shin ya halatta Mace kafira wanda ba Musulma ba ta yi mace Musulma wanka
idan ta rasu?. Sannan da shigar da ita Kabari sharadi ne dole sai Makusantanta,
ko kuwa kowane Musulmi zai iya shigar da ita kabari?. Akwai wasu mutane shin ya
halatta a bar su, su shigar da mace kabarinta?.
AMSA:
Musantan mace su ne za su yi mata wanka kuma za a
yi la'akari da wanda suka fi kusanci daga cikin wanda za su iya kyautata
wankan. Kuma ya halatta a wakilta kowace mace wanda za ta iya kyautata wanke
ta, koda kuwa ba makusanciyarta ba ce. Haka nan ya halatta miji ya wanke matan
shi, ita ta wanke shi.
Dangane da Mace kafira ta wanke Musulma, wannan
bai halatta ba, domin wanke mamaci ibada ce, kuma Ibadan wanda ba Musulmi ba,
bata inganta.
Dangane da shigar da mace kabarinta, ya halatta
wani daga cikin Musulmi ya shigar da ita koda ba makusancinta ba ne, matukar
zai kyautata haka.
Amsawa:
Al-Lajnatu
al-Daa'imah Lil iftaa'i.
A duba littafin فتاوى
المرأة المسلمة shafi na 441.
Tattarawa:
Umar Shehu Zaria
276. TAMBAYA
YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?
Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman
Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya
yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.
Amsa
Wa alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi
ya bude accout din da za'a dinga saka
masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki
da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta
275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka
zo bayanta.
Annabi SAW ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda
aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce.
Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya
wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai
sake amsa ba, tun da Allah ya Hana.
A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a
kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za
su bi su wala, saidai ba shi da ladan
wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.
wannan ita
ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da
sauransu.
Allah ne
mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
27/07/2017
277. TAMBAYA
TARAYYAN MAZA DA MATA YAYIN SALLAN JANAZA
Shin ya halatta Mace ta yi tarayya da Maza yayin
sallan Janaza?
AMSA:
Abun da yake asali a dukkan ibada wanda Allah
Ta'ala Ya shar'anta a littafinSa ko ManzonSa, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Ya
nusar da mu a cikin sunnoninsa, shi ne, tana game maza da mata, har sai idan an
samu wani dalili da ya kebance maza ko mata.
Kuma sallan
janaza tana daga cikin ibadu wanda Allah da ManzonSa suka shar'anta, don haka
tana game maza da mata. Sai dai sahun mata yayin sallan janaza yana kasancewa
ne a bayan sahun Maza, kuma ya tabbata cewa Mata sun yi ma Manzon Allah,
Sallallahu 'alaihi wa sallama, salla kamar yadda maza suka yi masa, sai dai
basu zuwa makabarta domin rufe mamaci saboda Manzon Allah, Sallallahu' alaihi
wa sallama, ya yi hani akan haka.
Amsawa: Al-Lajnatu al-Daa'imah Lil iftaa'i.
A duba littafin فتاوى
المرأة المسلمة shafi na 443.
Tattarawa:
Mal Umar Shehu Zaria.
278. TAMBAYA
ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA SABODA AIKIN
HAJJI?
Assalamu alaikum.
Tambaya
gare mu kamar haka: Ya halatta mace ta tsayar da jinin haila saboda hajj?
AMSA:
Wa'alaykumussalam,
To, 'Yar uwa
ya halatta, mutukar likita ya tabbatar miki ba zai cutar da ke ba, sai dai
tsayawa a Dabi'ar da Allah ya halicce ki akai shi ya fi kyau, saboda shan
magunguna irin wadannan yana birkita kwanakin al'ada, kamar yadda bincike ya
tabbatar.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
21\12\2015
279. TAMBAYA
YA HALLATA NA YIWA
WANI DAWAFI?
Assalamu alaikum, Malam, yayata ta jidda ta ce in
tambaye ka mene ne hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa
suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in
gaya ma wai don Allah ka amsa a face book,
saboda ana bukatar sanin amsar.
AMSA:
To, 'Yar uwa, babu wani dalili ingantacce wanda
yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba a samu magabata na kwarai suna yi
ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba'a yin ta sai da dalili daga
al-Qur' ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake
yiwa kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin
yiwa wani Umara ko Hajji, sai dai ba a samu na dawafi a karan kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba,
saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka
hada jiki da dukiya. Duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci,
amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.
Allah ne mafi sani.
Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta: 87
Amsawa:
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
7\12\2014.
280. TAMBAYA
SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?
Assalamu alaikum, Malam, yayata ta jidda ta ce in
tambaye ka mene ne hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa
suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in
gaya ma wai don Allah ka amsa a face book,
saboda ana bukatar sanin amsar.
AMSA:
To, 'Yar uwa, babu wani dalili ingantacce wanda
yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba a samu magabata na kwarai suna yi
ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba'a yin ta sai da dalili daga
al-Qur' ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake
yiwa kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin
yiwa wani Umara ko Hajji, sai dai ba a samu na dawafi a karan kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba,
saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka
hada jiki da dukiya. Duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci,
amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.
Allah ne mafi sani.
Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta: 87
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
7\12\2014.
No comments:
Post a Comment