181. TAMBAYA
ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA
Assalamu alaikum malam Don Allah malam ta yaya zan
samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar
an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci
Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai
abubuwan da malamai suka yi bayani cewa : suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka1.Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk
wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su .
2.Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a zuciyar
bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.
3.Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin
mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa.
4.Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah
"Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah"
Suratu Arra'ad aya ta 28
5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da
yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake
kasancewa cikin kunci.
6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.
7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.
8. Barin baccin da ba shi da amfani.
9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa
akan haka.
10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon
bukata.
Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin
ciki da damuwa da kuma kunci.
Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22
Allah ne ma fi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
17/8/2014
182. TAMBAYA
MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?
Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka.
Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Bai halatta ga mai takaba ba ta fita zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031) inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna
a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki
kammala iddarki"
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba
za ta fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a
sharia.
Imamu
Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi bayani cewa "Dukkan
Mata ana fitar da su daga gidanjansu Don su halarci idi, in ban da wacce take
iddar mutuwa.
Allah ne mafi Sani
Dr. Jamilu Zarewa
03/09/2017
183. TAMBAYA
NAMIJI ZAI IYA KARA GASHI!
Assalamu alaikum
Malam me hukuncin wanda ya qara gashi akansa irin
wanda maza suke zuwa ana musu surgery ashuka musu gashin musamman ga masu sanko
ko kuma waenda gashin kansu ke cincinyewa wai saboda su zama dai dai da sauran
Amsa
Wa alaikum assalam,
Bai halatta
ga namiji ya kara gashi ba, saboda hakan
canza halittar Allah ne.
Kasancewar Allah ya haramtawa mata kara gashi a
cikin hadisai ingantattu duk da cewa suna tasowa NE a cikin kwalliya kamar
yadda ayar Suratu Azzukruf ta tabbatar, hakan sai ya nuna namiji ne ya fi
cancanta da haramcin, tun da shi ba'a yi
shi don Ado ba.
Malamai suna cewa duka nassoshin da suke haramtawa
mata kara gashi, to maza ma suna ciki,
amma an kebance mata ne da haramcin saboda su ne suka fi yawan aikatawa.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
03/09/2017
184. TAMBAYA
CIWO YA DAMENI, ZAN IYA AMSAR BASHI DA RUWA DON NA
YI MAGANI?
Assalamu alaikum, mutum ne yake cikin halin rashin
lafiya, kuma al'ummah da suke tare ba masu taimakawa ne ba,gashi wannan ciwon
nason ya hallaka shi, shi kuma ba shi da kudi kuma ba shi da hanyar kudi, malam
shin zai iya karbar kudin LOAN na govt don surika cirewa duk wata, ko babu
halin haka nagode Allah yakara karfin imani da basirah
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Ya halatta ya amshi rancen mai ruwa, mutukar abin
da yake damunsa, ya kai wancan halin da ka ambata, saboda larura tana halatta
abin da aka hana, saidai ya wajaba ya amsa gwargwadon bukata.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
3\6\2015
185. TAMBAYA
NA SHA NONON MATATA, YAYA AURANMU?
Assalamu alaikum.Don Allah malam ya matsayin mutumin
da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka
jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa
da ita lokacin da take haila, don
haka ya halatta ka tsotsi nononta
mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani
akan halaccin hakan zuwa maganganu guda
biyu :
1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake
haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa" , Bukhari lamba ta
: 5102, ma'ana lokacin da ba zai iya
wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne
bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci
matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim,
don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha
nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya
sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin
malamai yana da kyau.
Don neman
Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67
Allah ne
mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
1\11\2014
186. TAMBAYA
NA RABA
GADONA KAFIN NA MUTU, KO YA INGANTA?
Assalamu alaikum. malam don Allah ina da tambaya
da fatan za'a amsamin, wai mutum zai iya rabawa iyalansa gadansa kafin yamutu
wai hakandin ya halatta? nagode
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa malamai suna cewa hakan bai inganta ba,
saboda dalilai, ga wasu daga ciki :
1. Hakan yana daga cikin gaggauta abin da Allah ya
jinkirta, saboda Allah ya sanya rabon gado ne, bayan mutuwa.
2. Zai iya
yiwuwa daya daga cikin iyalan nasa ya
mutu kafin shi, ka ga sai a samu kwan-gaba kwan-baya.
3. Yana iya jawo hassada saboda daya daga cikin
magadan zai iya yin kasuwanci da gadon da aka ba shi ya samu riba mai yawa
kafin magajinsa ya mutu, wanda hakan zai iya kawo hassada tsakanin magada, don
za su ga da ba'a yi gaggawar rabawa ba da ya kasance daga cikin rabonsu.
4. Yana daga cikin sharudan gado tabbatar da
mutuwar wanda za'a gada .
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
6\7\2015
187. TAMBAYA
SHIN
MUSULMI ZAI IYA AIKI A CHOCHI, DON SAMUN NA KALACI?
Assalam alaikum malam ina da tambaya; misali ni
brikilane kuma na kasance musulmine sai aka ban contrc din gini na church,
ogana ya ce mu za muyi; yaya matsayin mu yake idan munyi wannan aikin?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa malamai sun yi bayani cewa : bai halatta
musulmi ya zama Birkila a Chochi ba, saboda hakan yana daga cikin
taimakawa aikata zunubi, kuma zai iya jawowa mutum ya ga yadda ake shirka da
Allah, wanda hakan zai iya masa tasiri.,
Allah madaukaki yana cewa " kada ku yi
taimakekeniya wajan aikata sabo",
" suratul Al-maidah aya ta : 2, sannan duk abin da yake kaiwa zuwa barna,
to zai zama haramun ko makaruhi.
Don neman kari bayani duba : Al'umm ta
Shafi'i 4/213.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
19\5\2015
188. TAMBAYA
ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDU?
Assalama alaikum. Malam dan Allah
Ina aiki ne
akarkashi wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai kudisa bana halal bane wasu suce dan luwadi ne
wasu kuma suce kudin lukudu ne
ina so insan yadace nacigaba damai aiki ko inbari Allah y
kara lpy da ilimi da kafin basira ameen
Amsa
Wa alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan
kafin ka yanke hukunci.
Ba'a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato
mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a
cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan.
Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani
kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.a.w. ya yi mu'amala da
yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
16/09/2017
189. TAMBAYA
RAYUWAR DUNIYA A WAJEN MAGABATA NA-KWARAI
Aun bn Abdullahi yana cewa : "Wadanda su ka
zo gabaninmu sun kasance suna sanya abin da ya ragu na lahirarsu ga duniyarsu,
amma sai ga shi ku, kuna sanya abin da ya ragu na duniyarku ga lahirarku"
Yana nufin mutanen zamaninsa ba sa bawa Allah sai
dan lokacin da ya dan ragu na harkokin duniyarsu.
Subhanallah in da ya zo a wannan zamanin me zai
fada!!!
Wallahi na ga mutumin da kullum yake hada salloli
guda biyar a lokaci daya, yakan faro daga azahar din jiya har ya zo asubar yau,
gobe ma haka zai yi.
Rubutawa
Dr.Jamilu yusuf Zarewa
may 2014
190. TAMBAYA
ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SAMUN ILIMIN
ADDINI
Assalamu alaikum Akaramukallahu Allah ya kara
basira, kuma ina neman shawara cewa ni ina son na yi karatun addini, amma da na
fara sai na ji kamar raina ba ya so, a bani shawara nagode
Amsa :
Wa alaikum assalam.To dan'uwa akwai abubuwan da
suke taimakawa wajan samun ilimin addini, ga muhimmai daga cikinsu:
1. Tsarkake niyya- duk lokacin da ka tsarkake
niyyarka wajan neman ilimi, to Allah zai taimakeka.
2. Yin aiki da abin da mutum ya karanta- domin yin
aiki da ilimi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin rike ilimi da
kuma kiyaye shi.
3. Neman taimakon Allah – saboda ana so mai neman
ilimi ya dinga tunawa cewa Allah shi ne MASANI mai sanar da kowa, don haka ya
dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsa ya buda masa basira.
4. Nisantar zunubai, saboda ilimin addini haske
ne, kuma hasken Allah ba ya bawa mai sabo.
5. Yawan maimaitawa, domin maimaita ilimi na daga
cikin abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimi da tabbatarsa a zukata .
6. Jure wahala da kuma hakuri , saboda neman ilimi
ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahala ba, zai yi
wuya ya iya neman ilimi yadda ya kamata.
7. . Farawa da abin da ya dace da dalibi, domin
ana so dalibi ya fara da littafin da ya dace da shi wurin neman ilimi, saboda
idan ya fara da littafin da ya wuce matakin karatunsa, ba zai fahimce ba.
Ina tabbatar maka mutukar ka rike wadannan to
Allah zai taimakeka, ka samu ilimi cikin kwanciyar hankali
Allah ne
mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/4/2014
191. TAMBAYA
WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA!
Assalamu alaikum.
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace
mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta
yadda ba za ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam ko akwai wasu lokuta ne
da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar a saki
mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku
sake su a farkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da ba ku take su ba, Addalak aya ta
: (1) saidai akwai wurare guda hudu da ya halattta a saki mace mai haila :
1.Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko
kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.
2. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.
3. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to
anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi s.a.w. bai tambayi matar Thabit
ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i,
kamar yadda Bhukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5273.
4. Idan watanni hudu suka cika a lokacin ila'i, to
ko da tana haila zai iya sakinta.
Don neman karin bayani duba : Dima'uddaabi'iyya
shafi na :33
In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki
mai haila ba, kuma yin har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu
malaman.
Allah ne mafi sani.
Dr.Jamilu Zarawa
27/4/2014
192. TAMBAYA
SHIN BAIKO AURE NE?
Assalamu alaikum,
Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai
yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min
kauli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga mun yi aure, ni dai gaskiya malam na ki
yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa
a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure
ba ne saboda hujjoji kamar haka :
1. Abin da aka sani shi ne kudin da ake bayarwa
yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunkulewa su
bayar gaba daya, kin ga kuwa in haka ne, to ai dukkan aiyuka ba sa ingatuwa sai
da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito.
2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a
dawo masa da kudinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne.
3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan
wani ashararu zai iya kai kudi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da
ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna.
4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu
malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kudin da za'a yi
baiko, zai iya zama mutum daya, kin ga akwai nakasu kenan.
5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an
yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko
daban, aure daban.
6. Sannan duk
mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado
tsakanin wadanda aka yiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne,
domin ma'aurata suna gadon junansu.
Allah ne mafi sani.
24/3/2014
Dr. Jamilu Zarewa
193. TAMBAYA
BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA
Assalamu alaikum, malam
Don Allah ina da tambaya? wai miye riba a
musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya sai da akan nera 8?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malama riba ta kasu kashi biyu :
1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin
naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum
bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da
ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100
tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati
kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.
Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta
su, kuma ya kwashe musu albarka.
Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar
naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar
da Allah ya halatta, saidai ana so mutum ya saukaka idan yana siyar da kaya,
Annabi s.aw. yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai
siyar da kaya yake rangwame.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr Jamilu Zarewa
24/4/2013
194. TAMBAYA
ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN
HARAM?
Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani
ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa za mu ce
Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari'a? Saboda
tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa
Annabi s.a.w. yana cewa : "Allah ya la'anci mai cin
riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya
rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.
Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a
bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma
ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan
aike...
Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da
Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.
Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa
haramun ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a auransa,
saboda zai ciyar da matarsa da haramun
Malamai
suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya
maka kyauta za ka iya amsa, saboda
Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da
haram, amma in ba shi da wata sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin
dukiyarsa ba.
Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna
masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
10\4\2015
195. TAMBAYA
MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI, YA YA
KAMATA MU YI?
Assalamu alaikum, Malam dan Allah ina da tambaya?
tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga
watan karamar sallah Allah yayi mata
rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da
hairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har
zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba,
saboda fadin Allah madaukaki : "Kuma duk wanda yake mara lafiya ko
matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta : 185, wato
bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga
wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don
haka sai ya saraya akan shi.
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata,
saboda fadin Annabi s.a.w. : "Duk
wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa" .
kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 1851. Duba Fataawa
nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr.Jamilu Yusuf Zarewa
1\11\2014
196. TAMBAYA
YAUSHE NE LOKACIN SALLAR WALAHA?
Assalamu alaikum. Malam daidai wanne lokaci ne ya da ce a bisa kiyasin lokacin ayi sallar
walaha?
Amsa
Wa alaikum assalam,
To malam lokacin sallar walaha yana farawa ne daga
sanda rana ta daga ta fara zafi, kamar yadda Annabi s.a.w. yake cewa a cikin
hadisin Muslim mai lamaba ta : 748 "Sallar walaha lokacin da 'ya'yan
rakuma suka fara jin zafi" sannan lokacin yana karewa dab da zawalin rana,
da minti sha biyar ko kusa da haka.
Allah ne mafi sani.
25/2/2014
Dr. Jamil Zarewa
197. TAMBAYA
WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN
SAMA?
Assalamu alaikum Allah ya karawa
malam ilimi da fahimta. Shin da Allah malam ko
mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa
masallaci?. Nagode malam.
Amsa
Wa alaikum assalam. To dan’uwa malamai sun yi
sabani akan wannan mas’alar zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada
salloli saboda ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah
ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa
da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila
kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF
2\340.
2. Bai halatta ga wanda bai je sallar
jam’i ba ya hada salloli saboda ruwan sama,
saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je
masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa,
wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah
a gida, don haka rahusar baza ta sameshi ba, sannan kuma shari’a ta yi nufin ta
kiyaye sallar jam’i shi ya sa ta saukaka wajan hada
salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse
sallar jam’i ta tozarta, wannan ita ce maganar
Imamu shafi’i a littafinsa Al’umm 1\195,
Afahimtata maganar karshe ta fi inganci, don haka wanda yake gida ba zai hada
salloli ba.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
12/11/2015
198. TAMBAYA
ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?
Assalamu alaikum,
Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace
Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?
Amsa
Wa alaikumus salam,
Bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba
muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, ya kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai
musu mubaya'a, yana yi musu mubaya'a ne da Magana, kamar yadda ya tabbata a
hadisi.
Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga
Zina saboda yana tayar da sha'awa, Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a
aya ta 32 a suratul Isra'i, Zina tana daga cikin manyan zunuban da babu kamar
su bayan shirka da Allah.
Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai
kiyaye shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
05/05/2016.
199. TAMBAYA
SHIN ZAN IYA NEMAN SAKI DON MIJINA BAYA
HAIHUWA...!!
Assslam alaika warahamatullah
Dr inada matsala kamar haka fatan za'a taimakamin
da amsa malam munyi aure da mijin yau kusan shekara goma muna tare amma Allah
bai bamu haihuwa ba sannan kuma dan uwa nane na jini gashi yanzu banason zama
dashi shin idan na nemi ya sawwakemin nayi laifi?
Kuma hakan na nuna cewa nakasa cinye jarrabawar da
Allah yayimin kenan?
AMSA
Wassslam Alaiki warahamatullah wabrakatuhu
To yar uwa shi asalin aure a musulunci yana daga
cikin manufofinsa shine samun zuri'a ma'ana yaduwa a samu al'ummah
Annabi s.a.w. yace kuyi aure Ku domin Ku samu
zuri'a kuma ku auri matayen da kukeso masu haihuwa ni zanyi alfahari da yawanku
wajan yawan al'umma ranar alkiyama
To yar uwa bazan ce dake ki rabu dashi ba
shawarata gareki shine kiyi hakuri ki yawaita addu'oi wata kila Allah ya baku
haihuwar nan gaba amma idan kinga shekarun da kukayi sunyi yawa sunyi miki yawa
ba zaki iya cigaba da zama dashi ba bakwa haihuwa zaki iya neman ya sawwake
miki amma badon kunyi fada ba kuyi rabuwar lami lafiya to babu laifi shima ya
kamata ya sawwake miki amma yar uwa ki sani cewa ba'asan matsalar daga gareki take
ba ko daga garesa ne kada sai bayan kun rabu a gane daga gareki ne matsalar
Allah shine mafi sani
Dr. Abdallah Gadon kaya
11~2~2017
200. TAMBAYA
LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH?
Assalamu alaikum malam Dan Allah macece take fama
da yawan zuban yawu a bakinTa na laulayin ciki, Wanda yakai kafun nayi raka'a
daya ya cikamun baki sai na dan juya in zuba akan tsumma, sallan yayi ko bani
da halin juyawa kadan?
Amsa
Wa alaikum assalam. To 'Yar'uwa Annabi s.a.w. yana
cewa : "Waiwaye a sallah wani faucewa ne da Shaidan yake fauta daga sallar
bawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata : 718.
Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne
saboda hadisin da ya gabata.
Waiwaye yana halatta idan akwai bukata, saboda
akwai lokacin da sayyidina Abubakar ya
fara limanci, saboda Annabi s.a.w. baya nan, bayan Annabi s.a.w. ya dawo sai ya shigo masallaci,
sahabbai suna ganinsa sai suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar ya waiga
lokacin da ya ji tafi ya yi yawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 2544.
Malamai suna cewa : waiwayan da Abubakar ya yi
yana nuna hallacin yin waiwaye saboda bukata, tun da Annabi s.a.w. bai masa
inkari ba.
Don neman karin bayani duba : Fataawaa nurun
Aladdarb 9\225.
A bisa abin
da ya gabata, ya hallata ki dinga yin waiwaye saboda zubar da yawun da ya zama lalura, saidai duk
abin da aka halatta saboda bukata, ba'a so a wuce gwargwadonta.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREAWA
19\4\2015
No comments:
Post a Comment