41. TAMBAYA
LARABGANA A WATAN SAFAR?
Assalamu alaikum mallam tambayana
shine naji wasu mutane suna yin wani sallah yau, raka'a hudu wai sunan sallar
LARABGANA Ena so dan allah mallam yamin bayanin sallar?
Amsa
Wa alaikum assalam, To dan'unwa yana dağa cikin bidi'o'in zamanın maguzanci kudirta cewa
larabar karşhen watan Safar tana kunshe da bala'oi, addinin musulunci ya karya wannan camfin bayan zuwan Annabi S.A.W. don haka watan safar daya ne dağa çıkın watanni 12 wadanda Allah ya tabbatar, bai kebanta da wani bala'i na musamman ba.
Babu wata aya ko hadisi da ya kebance larabar karshen watan Safar da
wata ibada ta musamman, don haka yın nafilfili saboda neman kariya dağa musifun
LARABGANA, na daga çıkın bidi'o'i da ba su da asali a musulunci.
Don neman karın bayani duba Fatawa a Alajnah
Adda'imah 2/354. Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
9/12/2015.
42. TAMBAYA
FITINTINU SUN MANA YAWA, GA KUMA
FIRGICI, MENENE MAFITA?
Assalamu Alaykum Akaramakallah, da
fatan rubutuna zai zo maka cikin koshin lafiya. In cikin matsala da jarabawa
kusan shekara biyu yanzu. Na farko, na dauko wata yarinya na riko, ta gamu da
aljanu, ta koma gida, da zata dawo, ta dawo da jan kaya wai ta sa ajikinta duk
ranar lahadi, wai ta samu sauki. Maigida na ya hanata sa kayan. Bayan kamar
wata biyu, muka fita kasuwa, dukammu muka fita kasuwa sayayya, maigida na ya ga
pilowa ya saya, bayan hakan muka fara ganin gashin tsuntsaye a gida. duk
lokacin da karenmu yayi kuka sosai, tabbas zamu kwashe gashin da yawa a gida
ranar. Muka shiga addu'a da karanta alquran cikin gida. Yarana uku duk yammata,
duk safiyan Allah za su tashi da idanunsu jawur, da maigidana. Ni kuma, ina
cikin yin azkar dare da rana, abunda suka sa min shine firgita da tsoro, a duk
lokacin da karenmu ya fara kuka ko da rana ko da dare, sai in kama firgita
sosai da kuma ganin wadanan gashin. Mu na nan da haka, Allah ya nuna mamu
pilowan nan da muka saya gashi ne cike da ita. Muka kone ta. Bayan haka ne
damuwan ya karu. Gashinne cikin kayan sawanmu, da na yara, karkashin gadonmu da
na yara na, akan gado, cikin mota ne ko ina agida attah net na windodin mu, har
ata abincinmu. Muka bar gidan, inda muka koma, suka biyo mu, kuma duk lokacin
da muka shiga kauyenmu, sai su biyo mu gidan kauye. Ayanzu dai haka, muna sabon
gida, kuma sunanan da mu, akan kujerunmu, cikin net na windodin gida ne, gashin
na nan. Yanzu ma ciki gareni na wata shidda. Duk magungunan da zikirkiri na
sunnah, muna tayi, yarinya mai aljanin kuma har yanzu suna nan da ita, sun sha
yin alkawari zasu fita amma ba su fitaba, yanmata ne musulmai ajikinta. Ba kuma
wanda zai iya gaya mana ga abunda ke damumu. Mun sha magunguna da na wanka, da
hayakin mun gaji. Yanzu dai har, na bar duk magungun, amma ban bar yin addu'a
ba. Akaramakallah, ko za'a iya taimaka min da addu'a ko shawaran bi na samu
maganin abubawan da Ikon Allah anan. Allah ya saka da alkhairi..
Amsa
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri
ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani,
wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta
Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa
ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a
hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da
aka zuba magarya guda bakwai.
Sannan ina yi miki wasici da yawan
karatun suratul Bakara,saboda muhimmancinta wajan kore shaidanu, kamar yadda ya
tabbata a hadisi, kada ki manta da karanta addu'o'in shiga bandaki da na bacci,
da azkar na safe da yamma, da kuma tuba daga zunubai, saboda wasu musifun
zunubai su ke kawo su.
Idan fitintinun suka cigaba za ku iya
mayar da 'yar rikon, saboda zai iya yiwuwa a tare da ita shu'umcin yake, tun da
a baya ba ku ga haka ba, yana daga cikin ka'idojin sharia, ana tunkude cutar da
ta shafi mutane da yawa ta hanyar kau da kai akan cutar da za ta shafi mutum
daya, wannan ya sa mayar da ita bai zai zama laifi ba.
Yana daga cikin hanyoyin tunkude
fititinu, nisantar dukiyar haram, in har a kayan gidan da kuke ciki akwai
dukiyar da kuka mallaka ta hanyar haram ya wajaba a fitar da ita zuwa mai
ita.
Yin
sadaka da taimakawa musulmi yana warware mushkiloli, saboda duk wanda ya yayewa
wani bakin ciki, Allah zai duba dumuwarsa, hakura da wancan shaidanin karen na
ku yana da muhimmanci, saboda mala'iku ba sa shiga cikin gidan da yake akwai
kare, kamar yadda ya tabbata a hadisin Bukhari.
In har kin bi wadannan shawarwari ina ga za ki samu nasara mai girma.
Allah ne mafi sani
Amsawa:
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
7\2\2016.
43. TAMBAYA
MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA ?*
Assalamu alaikum. Malam Menene sahihi
akan mace tabawa mijnta zakkah?
Amsa
Wa alaikum assalam,
ya halatta a zancen mafi yawan malamai
saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas'ud wanda Bukhari ya rawaito
a sahihinsa a lamba ta:(1462) da kuma
Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta nemi fatwa akan bawa mijinta
sadaka kuma Annabi S A W. ya halatta mata hakan.
Malaman sun kafa hujja da wannan
hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna .
Aya ta (60) a suratu Attaubah ta yi
bayanin nau'o'i takwas na mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka,
hakan sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi zakka, tun da
ba'a samu dalilin da ya fitar da shi ba.
Saidai Ibnul Munzir ya hakaito ijma'i
cewa: "Bai halatta miji ya bawa matarsa zakka ba idan tana fama da
talauci, tun da zai iya wadatata ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa.
Don neman karin bayani duba: Sharhul
Mumti'i (6/168) da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah (10/62)
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
21/11 /2017
44. TAMBAYA
HUKUNCIN RUFE MUSULMI HADE DA ARNA!
Assalamu Alaikum. Dr muna son karin
hasken shari'ar Musulunci akan yadda sojoji ke
bikin karrama matansu da kuma yadda suke rufe Musulmi da wadanda ba
musulmi ba a makabarta daya.?
Amsa
Wa alaikum assalam,
malaman musulunci suna cewa: Ba'a rufe
MUSULMAI da kafirai a makabarta daya kuma hakan shi ne aikin magabata tun
zamanin Annabi s.a.w, har zuwa yau daga cikin dalilai akan haka shi ne manzon
Allah S.A.W. ya wuce makabartar kafirai sai ya ce wadannan alkairi ya rigaye
su, da kuma ya wuce makabartar musulmai sai ya ce wadannan sharri ya rigaye su
kamar yadda Nisa'i ya rawaito, wannan sai ya nuna banbanci tsakanin makabartun
biyu.
Idan aka rufe musulmi a makabartar kafirai in
an yi musu azaba za ta same shi, saboda aya ta: 46 a suratu Gafir ta nuna ana
yi musu azaba a kabarinsu.
Yin bukukuwa yayin bunne musulmi ya
sabawa ka'idojin SHARIA sanannu, don haka ya kamata musulmi su jarraba amsar
gawarsu mutukar hakan zai yiwu.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba Al-mugni
na Ibnu-khudaamah 2/563
Amsawa: Dr. JAMILU ZAREWA
21/11/2016
45. TAMBAYA
MIJINA BA YA BIYA MIN BUKATA, MENENE
SHAWARA ?
Assalamun alaikum, Malam mace ce
mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da
ya raba shi da uwar gidansa kenan.
Kasancewar ba ya biya mata bukata ta
shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta
shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta
yanke ?
Amsa
Wa alaikum assalam,
A shawarata kamata yayi a kira magabatansu
su xauna su tattauna a gano yadda xa'a warware matsalar.
Idan har ya tabbata ba cikakken namiji
ba ne to xa'a bashi shekara daya ya nemo magani.
Idan ya warke shikenan, in bai warke
ba kuma xa ta iya fadawa cikin haram idan taci gaba da xama dashi, to ya
halarta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwar gidan.
Yana daga cikin manyan manufofin aure:
ma'aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to
akwai matsala a xamantakewar aure.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
22/11/2017
46. TAMBAYA
BA KOWACCE "ALLAH YA ISA"
TAKE TASIRI BA!
Assalamu Alaikum, Allah Ya Gafarta
Malam, Uba Ne A Cikin Gida Duk Hakkokin Dake Kan Shi Na Iyalan Shi Baya
Saukewa, Sai Matar Ce Take yin Komai, Kama Daga Cin Yara, Suturar Su,
Dawainiyar Makaranta Da Sauran Su, Sai Rannan Wata Yar Hatsaniya Ta Shiga
Tsakanin Su, Sai Yace Duk Abunda Ta Kara yi A Gidan Wanda Yake Hakkin Shi Ne
Allah Ya Isa Bai Yafe Mata Ba, Kuma Malam, Bayyi Idan Ta Bari Yayan Ta Zasu
Galabaita Su Shiga Ukku, To Malam Idan Taci Gaba Dayi Allah Ya Isan Shi Zata Bi
Ta? Nagode
Amsa
Wa alaikum as salam,
Ya wajaba ya ciyar da su, in kuma ya
kı sai ta Kai shi wajan alkali, tun da ciyar da iyalai wajibı ne akan Uba
mutukar yana da iko, Hindu bintu Utbah ta je wajan Annabi s.a.w. ta fada masa cewa: mijinta Abu
Sufyan marowaci ne ba ya bata abin da zai ishe ta, ita da iyalanta, sai Annabi
s.a.w. ya ce mata : Ki dauki abin da zai işhe ki ke da yaranki dağa dukiyarsa.
Buhari ne ya rawaito.
Idan kuma ba shi da hali kina iya
ciyar da su, "ALLAH YA ISAN SHI" ba za ta cutar da ke ba, saboda ba
kowacce adduar sharri Allah yake amsa ba, ında Allah yana amsar dükkan
addu'o'in sharrin da mutane suke yi, da sun hallaka sun kare, kamar yadda aya
ta : 11 a suratu Yunus take nuni zuwa
hakan.
Allah ne mafi
Sani
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
20/11/2015
47. TAMBAYA
INA SO NA YI TSAYUWAR DARE, AMMMA NA
GAZA?
Assalamu Alaikum
Malam ina sha'awar yin tsayuwar dare
saboda dimbin falalar da ta kunsa, saidai a lokuta da yawa, na kan so na tashi,
amma sai na kasa, ko malam zai taimaka min da shawarwari akan abin da zai
taimake ni wajan yin wannan babban aikin, Allah ya karawa malam daukaka, amin.
Amsa
Wa'alaikum assalam.
To dan'uwa ina fatan Allah ya datar da
mu gaba daya zuwa wannan ibada mai girma, akwai abubuwa da malamai suka yi
bayanin cewa, suna taimakawa wajan samun damar tsayuwar dare, ga wasu daga ciki :
1. Baccin rana : Hasanul Basary ya
wuce wasu mutane a kasuwa da rana, sai ya ce wadannan ba za su yi bacci ba, sai
aka ce masa E, sai ya ce ina ganin
darensu ba zai yi kyau ba" .
2. Yin bacci da wuri , Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya
karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kamar yadda ya zo a
hadisin Muslim mai lamba ta : 647, kuma dalilin da ya sa ya karhanta hin hira
bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.
3. Aikata ladubban bacci yayin
kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo a cikin sunna na ladubban bacci.
4. Umartar wani ya tashe shi kamar
matarsa ko wanda suke tare.
5. Rashin cika ciki da abinci.
6. Nisantar yin aiki mai wahala da
rana.
7. Nisantar abin da zai kawo maka
fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya wuce
8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh
yana cewa : "idan ka ga ba ka iya tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubai ne
suka dabaibaye ka
ALLAH NE MA FI SANI
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
25/11/2014
48. TAMBAYA
TSINTUWAR DA AKE YIMA CIGIYA?
Assalamu
alaikum
Malam wani bawan Allah ne ya tsinci
Naira: #500#, a wurin kuma bai ga
wadanda zai yi wa cikiya ba... Ya ya
kamata yayi da kudin tsintuwar?, suna
ajiye yanzu haka kusan wata daya .
Amsa
Wa alakum assalam
To dan'uwa idan mutum ya yi tsintuwa
ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai
ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai
biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761. Amma
idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani
da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa : Annabi s.a.w.
ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce : In ban da ına tsoron na sadaka ne da
na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta:2527,
sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.
Malamai şun yi sabani wajan iyakance
tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za'a koma al'adar mutane, duk
abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama
ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba,
wato daya bisa hudun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya ya
yi amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba.
Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai Naira (5,00)
din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da
cigiya ba, tun ba kudi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta
ba.
Don
neman karin bayani duba : Al-mugni 6/351.
Allah ne mafi Sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
1/11/2015
49. TAMBAYA
ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA
SANYA CONDOM?
Assalamu Alaikum. Malam Allah ya
karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa
idan tana Haila matukar yasa Condom?
Amsa
Wa'alaikum assalam.
To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai
haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai
haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan
ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini
da kuma yın wanka.
Ba namiji ne kadai haila take iya
cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini
ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu da mace mai haila ba ko
da an sa Condum .
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
28/11/2015
50. TAMBAYA
SAFARAR JAKUNA ZUWA GA ARNA!
Assalamu Alaikum
Dr. Barka da dare dafatan kunwuni
lafiya Dr. Mutanenmu musulmai suna kaiwa arna jakuna suna ci. Menene hukuncin
dillalai da masu sayarwa da masu saye su kai da direbobin da suke kaiwa da
sauran ma'aikata a cikin harkar?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
A zahirin nassoshin sharia, yin hakan
taimakekeniya ne wajan aikata zunubi, Don haka dukkansu sun aikata haramun,
tunda Annabi s.a.w. ya haramta cin jakin gida ranar yakin Khaibar.
Siyarwa Wanda aka tabbatar zai ci
taimaka masa ne wajan sabawa sharia, wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye shi,
Wanda ya keta dokokinsa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
30/11/2016
51. TAMABAYA
SHIN MACE NA IYA BIN SALLAN JANA IZA?
Assalamu alaikum ,malam menene halaccin bin mata
sallar jana iza?Allah yasakada alkairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam Warahmatullahi wa barakaatuhu,
Sheikh Abdulaziz Bn Baz yana cewa:
Sallan janaza an shar'anta ta ga maza da mata
saboda fadin Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama:
"Duk wanda ya halarci sallan janaza har aka
yi mata salla, to yana da kiraadi daya, wanda kuma ya halarci sallan kuma har
aka rufe ta tare da shi, to yana da kiraadi guda biyu” sai aka ce mene ne
kiraadi guda biyu?, sai ya ce: "misalin manyan dutsawu guda biyu”. Yana
nufin wurin lada da za a bashi. Bukhari da Muslim suka riwaito.
Sai dai ba a halasta ma mata su bi janaza zuwa
makabarta ba, saboda hadisin Ummu Adiyyah wanda ya tabbata a cikin Bukhari da
Muslim take cewa: “An hana mu, mu bi gawa zuwa makabarta...”.
Domin neman karin bayani a duba Majmu' Fataawaa na
Sheikh Bn Baz (13/134).
Wannan kuma ita Fatawar Sheikh Muhammad Salih
al-Uthaimeen, Allah Ta'ala Ya yi musu rahama baki daya.
Wallahu A'alam
Amsawa:
Malam umar shehu Zaria
26 /04 /2017
52. TAMABAYA
ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SAMUN ILIMIN
ADDINI
Assalamu alaikum
Akaramukallahu Allah ya kara basira, kuma ina
neman shawara cewa ni ina son na yi karatun addini, amma da na fara sai na ji
kamar raina ba ya so, a bani shawara nagode.
Amsa :
Wa alaikum assalam.To dan'uwa akwai abubuwan da
suke taimakawa wajan samun ilimin addini, ga muhimmai daga cikinsu :
1. Tsarkake niyya- duk lokacin da ka tsarkake
niyyarka wajan neman ilimi, to Allah zai taimakeka.
2. Yin aiki da abin da mutum ya karanta- domin yin
aiki da ilimi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin rike ilimi da
kuma kiyaye shi.
3. Neman taimakon Allah – saboda ana so mai neman
ilimi ya dinga tunawa cewa Allah shi ne MASANI mai sanar da kowa, don haka ya
dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsa ya buda masa basira.
4. Nisantar zunubai, saboda ilimin addini haske
ne, kuma hasken Allah ba ya bawa mai sabo.
5. Yawan maimaitawa, domin maimaita ilimi na daga
cikin abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimi da tabbatarsa a zukata .
6. Jure wahala da kuma hakuri , saboda neman ilimi
ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahala ba, zai yi
wuya ya iya neman ilimi yadda ya kamata.
7. . Farawa da abin da ya dace da dalibi, domin
ana so dalibi ya fara da littafin da ya dace da shi wurin neman ilimi, saboda
idan ya fara da littafin da ya wuce matakin karatunsa, ba zai fahimce ba.
Ina tabbatar maka mutukar ka rike wadannan to
Allah zai taimakeka, ka samu ilimi cikin kwanciyar hankali
Allah ne
mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/4/2014
53. TAMABAYA
WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA !
Assalamu alaikum.
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace
mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta
yadda ba za ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam ko akwai wasu lokuta ne
da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar a saki
mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku
sake su a farkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da ba ku take su ba, Addalak aya ta
: (1) saidai akwai wurare guda hudu da ya halattta a saki mace mai haila :
1.Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko
kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.
2. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.
3. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to
anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi s.a.w. bai tambayi matar Thabit
ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i,
kamar yadda Bhukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5273.
4. Idan watanni hudu suka cika a lokacin ila'i, to
ko da tana haila zai iya sakinta.
Don neman karin bayani duba : Dima'uddaabi'iyya
shafi na :33
In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki
mai haila ba, kuma yin har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu
malaman.
Allah ne mafi sani.
Dr.Jamilu Zarawa
27/4/2014
54. TAMABAYA
SHIN BAIKO AURE NE?
Assalamu alaikum,
Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai
yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min
kauli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga mun yi aure, ni dai gaskiya malam na ki
yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa
a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure
ba ne saboda hujjoji kamar haka :
1. Abin da aka sani shi ne kudin da ake bayarwa
yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunkulewa su
bayar gaba daya, kin ga kuwa in haka ne, to ai dukkan aiyuka ba sa ingatuwa sai
da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito.
2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a
dawo masa da kudinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne.
3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan
wani ashararu zai iya kai kudi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da
ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna.
4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu
malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kudin da za'a yi
baiko, zai iya zama mutum daya, kin ga akwai nakasu kenan.
5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an
yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko
daban, aure daban.
6. Sannan duk
mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado
tsakanin wadanda aka yiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne,
domin ma'aurata suna gadon junansu.
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Zarewa
24/3/2014
55. TAMABAYA
BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA
Assalamu alaikum, malam
Don Allah ina da tambaya? wai miye riba a
musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya sai da akan nera 8?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malama riba ta kasu kashi biyu :
1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin
naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum
bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da
ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100
tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati
kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.
Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta
su, kuma ya kwashe musu albarka.
Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar
naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar
da Allah ya halatta, saidai ana so mutum ya saukaka idan yana siyar da kaya,
Annabi s.aw. yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai
siyar da kaya yake rangwame.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr Jamilu Zarewa
24/4/2013
56. TAMABAYA
ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN
HARAM?
Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani
ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa za mu ce
Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari'a? Saboda
tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa
Annabi s.a.w. yana cewa : "Allah ya la'anci mai cin
riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya
rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.
Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a
bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma
ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan
aike . .
Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da
Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.
Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa
haramun ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a auransa,
saboda zai ciyar da matarsa da haramun
Malamai
suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya
maka kyauta za ka iya amsa, saboda
Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da
haram, amma in ba shi da wata sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin
dukiyarsa ba.
Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna
masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
10\4\2015
57. TAMABAYA
MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI, YA YA
KAMATA MU YI?
Assalamu alaikum, Malam dan Allah ina da tambaya?
tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga
watan karamar sallah Allah yayi mata
rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da
hairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har
zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba,
saboda fadin Allah madaukaki : "Kuma duk wanda yake mara lafiya ko
matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta : 185, wato
bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga
wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba,
don haka sai ya saraya akan shi.
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata,
saboda fadin Annabi s.a.w. : "Duk
wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa" .
kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 1851. Duba Fataawa
nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DrJamilu Yusuf Zarewa
1\11\2014
58. TAMABAYA
YAUSHE NE LOKACIN SALLAR WALAHA?
Assalamu alaikum. Malam daidai wanne lokaci ne ya da ce a bisa kiyasin lokacin ayi sallar
walaha?
Amsa
Wa alaikum assalam,
To malam lokacin sallar walaha yana farawa ne daga
sanda rana ta daga ta fara zafi, kamar yadda Annabi s.a.w. yake cewa a cikin
hadisin Muslim mai lamaba ta : 748 "Sallar walaha lokacin da 'ya'yan
rakuma suka fara jin zafi" sannan lokacin yana karewa dab da zawalin rana,
da minti sha biyar ko kusa da haka.
Allah ne mafi sani.
25/2/2014
Dr. Jamil Zarewa
59. TAMABAYA
Assalamu alaikum, Dr. Allah Ta'ala Ya saka da
alheri. Don Allah tambayata ita ce: an ce idan mutum ya rasu mahaifi da
mahaifiyarsa suna raye amma bashi da 'ya'ya ko mata, iyayen ne kadai za su gaje
shi koda yana da kanne da yayyi.
Idan haka ne, to ya za a raba gadon tsakanin
mahaifi da Mahaifiyar shi?.
Amsa:
Wa alaikumus Salaam wa rahmatullahi wa
barakaatuhu, na gode da addu'a.
Dangane da rabon gado tsakanin iyaye kuwa, za a
raba abun da ya bari gida uku (3), mahaifi zai dauki kaso biyu (2), Mahaifiya
kuma ta dauki kaso daya (1).
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
03/05/2017.
60. TAMABAYA
WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN
SAMA?
Assalamu
alaikum Allah ya karawa
malam ilimi da fahimta. Shin da Allah malam ko
mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa
masallaci?. Nagode malam.
Amsa
Wa alaikum assalam. To dan’uwa malamai sun yi
sabani akan wannan mas’alar zuwa maganganu guda biyu :
I. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada
salloli saboda ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah
ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa
da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila
kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF
2\340.
2 Bai halatta ga wanda bai je sallar
jam’i ba ya hada salloli saboda ruwan sama,
saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je
masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa,
wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah
a gida, don haka rahusar baza ta sameshi ba, sannan kuma shari’a ta yi nufin ta
kiyaye sallar jam’i shi ya sa ta saukaka wajan hada
salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse
sallar jam’i ta tozarta, wannan ita ce maganar
Imamu shafi’i a littafinsa Al’umm 1\195,
Afahimtata maganar karshe ta fi inganci, don haka wanda yake gida ba zai hada
salloli ba.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
12/11/2015
No comments:
Post a Comment