GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Sunday, 20 May 2012

TAMBAYA TA DARI BIYU DA ARBA'IN DA DAYA (241) ZUWA TA DARI BIYU DA SITTIN (260)

241. TAMBAYA

YAUSHE AKE FITA DAGA I'ITIKAFI

 

Assalamu Alaikum. Malam inaso a fada min mafi rinjayan zance game da lokacin fita daga I'itikafi?

Amsa

Wa'alaikumus salam,

To dan'uwa malamai suna da ra'ayoyi biyu akan wannan mas'alar :

1. Fita  daga I'iitikafi daga zarar an ga watan Ramadhna,  wato bayan rana ta fadi a daren  Idi, saboda  I'itikafi ana  yinsa ne a Ramadhana kuma idan  an ga wata Ramadhana ya  kare.

2. Mai I'itikafi zai iya zama har zuwa lokacin sallar Idi, ta yadda zai fita bayan kammala sallar, Imamu  Asshafi'i yana cewa: "Duk wanda ya yi niyyar koyi da Annabi S.A.W. to  ya  fita daga I'itikafi bayan rana ta fadi in an ga wata, watan ya yi nusan ko ya cika, amma in ya zauna zuwa sallar idi, hakan shi ne yafi"  Imamu Malik yana cewa: "Na samu labarin wasu daga cikin mutanan kirki suna fita daga I'itikafi bayan sallar idi"

Zance mafi inganci shi  ne fita daga I'itikafi bayan ranar daren idi ta fadi, saboda Annabi S. A. W. yana I'itikafin dararen goman karshe ne, su kuma suna fita idan daren IDI ya shiga.

Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy 6/323 da kuma FaTaawa Allajnah Adda'imah 15/411

Allah ne mafi  sani

24/06/2017

Dr. Jamilu Zarewa

 

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

242. TAMBAYA

YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU!

 

 Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Ta  saku mana,  saboda rubutu

Saturday, 19 May 2012

TAMBAYA TA DARI BIYU DA ASHIRIN DA DAYA (221) ZUWA TA DARI BIYU DA ARBA'IN (240)

221. TAMBAYA

SHIN ME NENE ZIHARI?

 

Assalamu alaykum Warahmatullahi wabarakatuh. Don Allah Mallam menene ZIHARI? Allah yaqara ilimi mai amfani.

 

Amsa

Wa'alaykumussalam,

Zihari shi ne mutum ya kamanta matan shi da wata wanda take muharrama a gare Shi kamar Mahaifiyan sa, kanwar shi ko 'Yar shi da ya haifa.

Wallahu A'alam

Malam Umar Shehu Zaria

03/03/2017

 

 

222. TAMBAYA

ALAMOMIN KARBAR TUBA

 

Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya?

 

Amsa

 

Wa alaikum assalam.To dan'uwa

Friday, 18 May 2012

TAMBAYA TA DARI BIYU DA DAYA (201) ZUWA TA DARI BIYU DA ASHIRIN (220)

201. TAMBAYA

HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!

 

Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake da janaba ya kira sallah?

Amsa

Wa'alaykumussalam,

To dan'uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan,

Thursday, 17 May 2012

TAMBAYA TA DARI DA TAMANIN DA DAYA (181) ZUWA TA DARI BIYU (200)

181. TAMBAYA

ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

                 

Assalamu alaikum malam Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci

Amsa

Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai

Wednesday, 16 May 2012

TAMBAYA TA DARI DA SITTIN DA DAYA (161) ZUWA TA DARI DA TAMANIN (180)

161. TAMBAYA

YAYI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YAYI KAFFARA

 

Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.

Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga  Malam.

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Auransa na biyun ya inganta saboda ba su da alaka da juna.

Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware, amma

Monday, 14 May 2012

TAMBAYA TA DARI DA ARBA'IN DA DAYA (141) ZUWA TA DARI DA SITTIN (160)

141. TAMBAYA

TARAYYAN MAZA DA MATA YAYIN SALLAN JANAZA

 

Shin ya halatta Mace ta yi tarayya da Maza yayin sallan Janaza?

AMSA:

Abun da yake asali a dukkan ibada wanda Allah Ta'ala Ya shar'anta a littafinSa ko ManzonSa, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Ya nusar da mu a

Sunday, 13 May 2012

TAMBAYA TA DARI DA ASHIRIN DA DAYA (121) ZUWA TA DARI DA ARBA'IN (140)

121. TAMBAYA

WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU !!!*

 

 Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?

Amsa

Wa alaikum assalam,  ta  saku mana,  saboda rubutu yana  daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W.  yana cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame

TAMBAYA TA DARI DA DAYA (101) ZUWA TA DARI DA ASHIRIN (120)

101. TAMABAYA

Shin Malam mene ne matsayin direban motar da ayayi hadari aka mutu?,

Assalamu Alaikum Sheikh!!!; Mutum ne suka yi accident a cikin mota sai aka kai su asibiti, bayan wasu kwanaki wasu daga cikin wanda suka yi accident din suka mutu. Shin Malam mene ne matsayin direban motan?, zai yi azumi ne?; kuma idan zai yi guda nawa zai yi?, saboda ba mutun daya ne ya mutu ba.

Ina fata Sheikh zai amsa don ma amfanin ragowar musulmai masu damuwa da  irin wannan. Na gode Allah ya kara ilimi da imani.

Amsa:

To dan uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:

1. Diyya wacce dangin wanda

Saturday, 12 May 2012

TAMBAYA TA TAMANIN DA DAYA (81) ZUWA TA DARI (100)

81. TAMABAYA

SHIN AMAI NA KARYA AZUMI?

 

Assalamu alaykum'm Malam Dan Allah inada tambaya,nice ina azumi se nayi irin Dan aman nan wanda ake ce masa aman kaji,Dan kadanne ba wae amai da yawaba,to malam ya matsayin azumi na naji ance amai yana karya azumi.Allah y qarawa malam Lpy.

 

Amsa

Wa'alaykumussalam,                 

Duk aman da akayi kadan ko mai yawa ba da gangan ba toh baya karya azumi amma idan

Friday, 11 May 2012

TAMBAYA TA SITTIN DA DAYA (61) ZUWA TA TAMANIN (80)

61. TAMABAYA

 

Assalamu alaikum warahamatullahi wabara katuh.

Don Allah Malam inaso awarware min wannan rabon gadon.

mamaci ne yabar mahafiyar sa,da yan uwa mata(uwa daya uba daya),sai kuma yan uwa maza da mata(uwa daya uba kowa da nashi)da kakar sa(uwar mahaifinsa).

Shin Malam wadannan zasu iya cinye gadon ko yanuwan mahaifinsa (shakikai)zasu iya shigowa?

Allah yaba Malam ikon amsa tambaya ta.

 

AMSA

Wa alaikum assalam, Za'a