241. TAMBAYA
YAUSHE AKE FITA DAGA I'ITIKAFI
Assalamu Alaikum. Malam inaso a fada min mafi
rinjayan zance game da lokacin fita daga I'itikafi?
Amsa
Wa'alaikumus salam,
To dan'uwa malamai suna da ra'ayoyi biyu akan
wannan mas'alar :
1. Fita
daga I'iitikafi daga zarar an ga watan Ramadhna, wato bayan rana ta fadi a daren Idi, saboda
I'itikafi ana yinsa ne a
Ramadhana kuma idan an ga wata Ramadhana
ya kare.
2. Mai I'itikafi zai iya zama har zuwa lokacin
sallar Idi, ta yadda zai fita bayan kammala sallar, Imamu Asshafi'i yana cewa: "Duk wanda ya yi
niyyar koyi da Annabi S.A.W. to ya fita daga I'itikafi bayan rana ta fadi in an
ga wata, watan ya yi nusan ko ya cika, amma in ya zauna zuwa sallar idi, hakan
shi ne yafi" Imamu Malik yana cewa:
"Na samu labarin wasu daga cikin mutanan kirki suna fita daga I'itikafi
bayan sallar idi"
Zance mafi inganci shi ne fita daga I'itikafi bayan ranar daren idi ta
fadi, saboda Annabi S. A. W. yana I'itikafin dararen goman karshe ne, su kuma
suna fita idan daren IDI ya shiga.
Don neman karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy
6/323 da kuma FaTaawa Allajnah Adda'imah 15/411
Allah ne mafi
sani
24/06/2017
Dr. Jamilu Zarewa
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
242. TAMBAYA
YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU!
Assalamu
alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba
kawai ya rubuta ne shin tasa ku?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ta saku mana, saboda rubutu