301. TAMBAYA
AZUMI NAWA AKE YI A WATAN MUHARRAM?
Assalamu Alaikum Malam Don Allah malam azumi nawa akeyi a wannan watan ?
Amsa
Wa Alaikum Assalam To 'yar'uwa ana so mutum ya zage dantse wajan yin Azumi a wannan watan, saboda fadin Annabi (SAW) : "Mafificin Azumi bayan Ramadhana shi ne Azumi a watan Muharram" kamar yadda Muslim ya rawaito.
Amma Wanda ya fi muhimmanci shi ne na ranar goma ga wata, sai kuma na ranar tara, Annabi S.A.W yana cewa: "Azumin ranar goma ga wata yana kankakare zunubin shekara daya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1162), sannan yana cewa: "Idan na rayu zuwa badi zan azumci ranar ranar tara ga MUHARRAM".
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
31/08/2019.
302. TAMBAYA
TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE ?
Assalamu alaikum malam Mace taba da jikinta ga
mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din
nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga
ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba?
Jazakallahu khairaljazaaa.
Amsa :
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game