GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Sunday 24 July 2022

TAMBAYA TA DARI UKU DA DAYA (301) ZUWA TA DARI UKU DA ASHIRIN (320)

 301. TAMBAYA


 AZUMI NAWA AKE YI A WATAN MUHARRAM?


Assalamu Alaikum Malam Don Allah malam azumi nawa akeyi a wannan watan ?


Amsa

Wa Alaikum Assalam To 'yar'uwa ana so mutum ya zage dantse wajan yin Azumi a wannan watan, saboda fadin Annabi (SAW) : "Mafificin Azumi bayan Ramadhana shi ne Azumi  a watan Muharram" kamar yadda Muslim ya rawaito.

Amma Wanda ya fi muhimmanci shi ne na ranar goma ga wata, sai kuma na ranar tara, Annabi S.A.W yana cewa: "Azumin ranar goma ga wata yana kankakare zunubin shekara daya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1162), sannan yana cewa: "Idan na rayu zuwa badi zan azumci ranar ranar tara ga MUHARRAM".

 Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA


31/08/2019.



302. TAMBAYA

TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE ?

 

Assalamu alaikum malam Mace taba da jikinta ga mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa.

 

Amsa :

Wa alaikum assalam

To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game

da tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.

Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.

Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr.JAMILU YUSUF ZAREWA

4/4/2014

 

303. TAMBAYA

BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?

 

Assalamu Alaikum.

Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?

 

Amsa:

Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo.                                                                               Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo".                                                Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida suka siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.       

 Allah Ne mafi Sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

16/08/2016

 

304. TAMBAYA

HUKUNCIN KARBAR LOAN

 

Assalamu Alaikum, Malam menene hukunchin karbar bashi amma na kaya ma'ana kamar (Car loan,) ko nau'insu kamar abinchi, wanda mutum zai amsa ya biya zuwa wani lokaci, amma kuma farashin yana bambamta da wanda zai je kasuwa ya bayar da kudinsa ya siya. Shin akwai RIBA a cikin irin wannan loan din? Koko babu. Allah ya saka da alkhairi.

 

Amsa :

Wa alaikum assalam

To dan'uwa Mutukar an bayyana masa kudin tun da farko, to ba riba ba ne ko da ya sabawa farashin kasuwa, domin lokaci yakan yi tasiri wajan ciniki, saboda in har an biya 'yan kasuwa kudin su cikin lokaci to za su iya amfana da su, wajan sayo wasu kayan da za su ci riba, don haka malamai suka yi bayyani cewa hakan ya halatta, idan har an yi sharadi da farko .

Saidai abin da sharia ta hana shi ne : ayi kari akan sharadin farko, kamar ya sayar masa da abu naira (10,0000) sai ya zama ya kasa biya a lokacin da suka yi alkawari,, sai ya kara masa 3,000, akai, wannan shi ne abin da ya haramta , saboda Annabi s.a.w. ya hana yin ciniki byu cikin ciniki daya. kamar yadda ya zo a hadisin da Malik ya rawaito a Muwada'a a lamba ta : 2640

Don neman Karin bayani : duba : Fiqhul muyassar : shafi na : 219.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

7/4/2014

 

305. TAMBAYA

Assalamu alaikum

Ya gida Dan Allah mal.ina so kataimaka mana akam

Raban gadone.macece ta mutu tabar yaya guda biyu mace daya namiji daya se mahaifiyar ta.km abinda tabari shine kudi 800000k dubu Dari ta takwas

Dan Allah yaza’a rabamusu

 

Amsa

Wa'alaikum assalam,

 zá'a raba gida shida sai a bawa Uwa (133,333.333333) ragowar (666,666.666664) sai a bawa 'ya'yanta su raba duk namiji ya dau rabon matá biyu.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

18/08/2017

 

306. TAMBAYA

HUKUNCIN KARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA

 

ASSALAMU ALAIKUM, da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan ALLAH mal ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode

 

Amsa

Wa'alaykumussalam,

To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa : "Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bukhari 1\426

ALLAH NE MAFI SANI

Dr. Jamil Zarewa

16/8/2014

 

307. TAMBAYA

Assalamu Alaikum a taimaka mini a mikawa Mallam Jamilu wannan tambayar:-

Macece tarasu tabar 'ya mace, da 'yar uwa shaqiqiya, da 'yar uwa li'ammiya. Yaya rabon gadonta Zai kasance?

 

Amsa

Wa  alaikum assalam,

 Za'a raba gida biyu, a bawa 'Ya rabi,  sai kuma ragowar rabin a bawa 'yar uwa shakikiya.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

10/08/2017

 

308. TAMBAYA

 Assalamu Alaikum Allah yaqarawa Malam Ilmi, mlm wai in mace bata ta6a haihuwar namijiba har ta mutu amma tana da yaya mata, towai bayan iyayanta yan uwanta ma sun shiga cikin gadonta??

 

Amsa

Wa  alaikum assalam, In har 'yayan nata mata sun kai biyu,  kuma iyayan nata biyun duka suna raye, 'yan'uwa ba za su yi gado ba.

Uba yana kare 'yan'uwa na kowanne bangare ba sa gado tare da shi.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

20/08/2017

 

309. TAMBAYA

ZAN IYA AURAN JIKAR YAYATA ?

 

Assalamu Alaikum, Allah yasa Malam yana cikin koshin lafiya. Malam Ina neman a warwaremun wata matsala ne, Akwai aure tsakanina da jikar yayata? Wato dani da kakar yarinyan mahaifinmu daya.

 

Amsa

Wa alaikum assalam,  Babu aure a tsakaninku mutukar mahaifiyarku daya da kakarta, saboda aya ta  (23) a suratun Nisa'i ta haramta auran 'yar 'yar'uwa wacce kuke  uwa daya ko uba daya ko kuma shakikai.

'Yar 'yar'uwa a wannan ayar ta hada da Jikarta da jikar jikarta har zuwa can kasa kamar yadda malaman Fiqhu su ka yi karin bayani.

Don neman karin bayani duba babun NIKAH a Fiqhul Muyassar da tafsiran malamai ga aya ta (23) a Suratun Nisa'i.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

19/08/2017

 

310. TAMBAYA

NA JONA SALLATA DA TA MAMU,BAYAN AN GAMA

SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?

 

Assalamu alaikum malam. Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam'i

ba sallah? Misali, na zo masallaci na taradda jam'i na sallar asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don karasa raka'a

2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada jam'i da ni.

Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya halatta, tare da hujjoji.

 

Amsa

Wa alaikum assalam.To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar

zuwa zantuka guda biyu:

1. Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba, sannan kuma

shi masabuki ba liman ba ne, Annabi S.A.W kuma ya yi umarni da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta ki karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in ya gama yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka sai ya haramta . Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma Mawahibul-jalil 4\489.

2. Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin

zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da daddare sai ya bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta:666, A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya halatta mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi S.A.W bai hana Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara da shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai ne, don haka sai ya halatta a bi shi.

Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.

Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu saboda abin da ya gabata da kuma hadisan da suke nuna falalar sallar jam'i.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

07/12/2014

 

311. TAMBAYA

HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN SALLAR NAFILA

 

Assalamu alaikum. malam Menene asali ko dalili idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya dan matsa baya ko gaba daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?

 

AMSA :

Wa alaikum assalam To dan'uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba : 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178 Saidai malamai suna cewa : ana so ayi hakan saboda gurare da yawa su yi ma mutum shaida,

Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin da aka rawaito daga Aliyu - Allah ya kara masa yarda- yana cewa : "Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila" wannan yasa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335

ALLAH NE MAFI SANI

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

22/8/2014

 

312. TAMBAYA

SHIN ZA'A IYA YIWA DAN SHI'A SALLAMA ?

 

Assalamu'alaikum.  warahaamatullahi wabarakatuhu : Malam shin zan iya yiwa dan Shi'a sallama ?

 

Amsa:

Wa alaikum assalam. To dan'uwa Allah da manzonsa sun kwadaitar akan sallama saboda kasancewarta tana sanya soyayya a tsakanin mutane, tana kawo hadin kai tana gusar da kewa, wannan yasa Annabi s.aw. ya yi umarni da sallama, saboda tana kaiwa zuwa Aljanna, kamar yadda hadisin Tirmizi mai lamba ta: 599 ya tabbatar da hakan.

Tabbas 'yan shi'a suna da akidu wadanda suke warware musulunci, Daga ciki akwai zagin sahabban da Allah ya yarda da su, da riya tawayar qur'anin da Allah ya yi alqawarin kiyaye shi, da siffanta Nana A'isha da mazinaciya duk da Allah ya kubutar da ita daga can saman saman bakwai.

 Saidai ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za'a kira shi da kafiri , dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.

 Yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman Tauhidi ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin 'yan shi'a da gama-gari wadanda suka shiga shi'a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirta su ba,kuma ba za mu ki yi musu sallama ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa da suka gabata, saboda akwai hadisai da yawa da suke bada uzuri ga wanda ya aikata kafirci bisa kuskure ko jahilci.

 Don haka duk musulmin da ka san an shigar da shi SHI'A a ba-bai saboda jahilcinsa kana iya masa sallama, kyakykyawar mu'amala tana iya sanyawa mutum ya gane gaskiya, kamar yadda hakan ya faru ga mutane da yawa a zamanin annabi S.a.w. da sahabbansa.

Allah nai mafi sani.

 

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

17/1/2016

 

313. TAMBAYA

IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA?

 

Assalamu alaikum.

yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi???

 

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.

Wasu  malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya  yi ranar 14 ko kuma  ranar 21.

Duk wanda bai samu damar yiwa dansa Akika  ba a  kwanakin da aka ambata a sama,  to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya  yi duk lokacin da ya samu dama.

AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa a lokacin da Annabi S. a. w  ya ambata, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.

Allah ne mafi sani

Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha 1/615.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

26/08/2017

 

314. TAMBAYA

AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI?

 

Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma'aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum, a ciki ?

 

Amsa:

Wa alaikum assalam

To dan'uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta b\a, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.

Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: "Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da b a huruminsa ba ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika'u babil maftuh: 238.

Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da hakan.

An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul'aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama'a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.

Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

25\2\2016

 

315. TAMBAYA

 Salam Dr.Yar babana ta rasu ba ta da Da ko jika sai dai yarta wacce suke uba daya damu 'ya'yan kaninta da kanwarta wadanda suke shakikai.Ya gadonta yake?

 

Amsa

 Wa alaikum assalam,  za'a kasa abin da ta  bari gida Biyu, a bawa yarta kashi daya, ragowar saí a bawa 'ya'yan kaninta maza su raba, ban da matan.

'Ya'yan kanwa ba sa cikin mutum 25 da suke gado.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF  ZAREWA

27/08/2017

 

316. TAMBAYA

SANA'A DA WUTAR LANTARKI A GIDAJAN GWAMNATI ?

 

Assalamu alaikum malam. Tare da fatan Allah Ya karbi ibadun mu da ku Alhazai baki daya.

Malam ina hukunchin wanda suke zaune a gidan hukuma, kudin wuta da ruwa duk hukuma ke biya. Ya halatta suyi harkan kasuwanchi da ruwa da wuta, kamar niqa gari, ko yin qanqara suna chin kudin da suka samu. Ina matsayin wannan a Shari'a?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

 In har a cikin albashinsa ake dauka babu laifi in ya yi sana'a kamar yadda hakan yake faruwa a cikin albashinmu na malaman jami'o'i, tun da hakkinsa ne kuma in da ba ya shan wutar da ba'a cira a albashinsa.

Misali a A. B. U. Zaria hukuma tana cirar min dubunanai daga Albashina duk wata, saboda wutar lantarkin GIDANA, kin ga babu laifi in na yi Sana'a da wutar saboda na riga na biya.

Amma idan akwai sharadin da hukuma  ta sanya na hana amfani da wutar a wasu halaye da kuma lokuta ko wasu kayan lantarki saboda kar asha ta wuce ka'ida ko gudun fadawa hadari ya wajaba a kula da su, mutukar bai sabawa sharia ba, tun da musulamai suna kan sharudansu ne kamar yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

28/08/2017

 

317. TAMBAYA

SON KARIN BAYANI AKAN 'YAN TABLIG ?

 

Assalamu alaikum . Da fatan Malam yana lafiya . Dan Allah ina son bayani akan tabligh da mutanen pakistan suka assasa kuma suke yawon da awa suna kiran mutane su fita da'awa na wasu kwanaki ko watanni. Mijina ya shiga kuma zai tafi kwana 40 amma ni hankali na ya ki kwanciya da hakan . Jazakallah . Ina binku ne a whatsapp.

 

Amsa:

Wa alaikum assalamu.To 'yar'uwa 'yan tablig wasu jama'a ne wadanda suka sanya da'awa i zuwa ga Allah babban aikinsu,   kuma mutane ne masu gudun duniya, in sun je gari da'awa ba sa sauka wajan kowa,  saidai şu shiga masallaci, suna dagewa sosai wajan da'awa duk alhamis a  wasu kasashen, Muhammed Yûsuf Al-kandahlawy Ba'indiye wanda ya mutu a shekara ta:1364 bayan hijira  shi ne ya kafata.                                                                                        Saidai akwai kura-kurai da yawa a tafiyarsu,  daga cikin akwai:

*1.* Karancin ilimi,  ba şu damu şu yi ilimi mai zurfi ba, ko dan yaya şu ka Samu sai şu tsunduma çıkın da'awa.                                                        *2.* Ba şu damu da hana aikata mummuna ba, şuna karfafa da'awarsu ne wajan umarni da ayyukan da Allah ya ke so.

 *3.* Suna da karancin ilimin tauhidi,  sun fi damuwa da bayanin falalolin ayyuka

*4.* Suna kafa hujja da hadithai raunana da na karya.

*5.* Wasu daga cikinsu suna sakaci da hakkokin iyalansu,  saboda shagalarsu da da'awa.

*6.* Sukan aibanta malaman da ba sa cikinsu,  da rashin damuwa da Şakacı da da'awa.                                                                                        *7.*Karancin iliminsu yana jawo musu fadawa kura-kurai wajan fassara Al'qur'ani.                                              In har kin san mijinki yana da karancin ilimi  zai fi kyau ki sanya a tsawatar masa, game da bin su don kar ya fito kafin ya nuna,  duk wanda ya zamar da kansa malami kafin ya isa, barnarsa za ta fi gyaransa yawa.                                                                 

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

5/3/2016

 

318. TAMBAYA

DAGA YANZU MAHAJJATAN NIGERIA BA ZA SU SAKE HALARTAR JIFAN SHAIDAN BA!

 

Dr. muna so ayi mana bincike  akan wannan : Daga Yanzu Mahajjatan Nijeriya Ba za Su Sake Halartar Jifan Shedan Ba, Inji Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II kuma Amirul Hajji na bara, a hajjin da ya gabata ya bayyana cewa daga yanzu mahajjatan Nijeriya ba za su sake halartar jifan Shedan ba, saidai idan an sama musu masauki a kusa da Jamrat inda a nan ne za a gudanar da jifan, Ya kuma kara da cewa bakaken fata irin al'ummar Nijeriya bai zama wajibi sai sun gudanar da jifan Shedan ba.

Sarkin ya bayyana hakan ne bayan yawan mace-macen da aka samu a wurin turmutsitsin jifan Shedan a hajjin bara, wanda ciki har da mahajjatan Nijeriya kimanin saba'in suka rasa ransu. Ya kuma kawo hujjoji da dama daga ayoyin Kur'ani, wadanda suka nuna cewa rashin halartar jifan Shedan ba zai kawo rauni a hajjin mahajjaci baa.

 

Amsa:

Ina rokon Allah ya ba mu dacewa, ya kuma sanya rayuwarmu  kamar yadda yake so, tabbas wannan Magana ta mai martaba ta girmama, amma ga amsoshin da zan iya bayarwa  a takaice:

*1.* Farko dai abin da bincikena ya tabbatar min shi ne: 

Daga cikin manyan dalilan da suka sanya shemomin Nigeria su ka yi nisa da wajan jifa shi ne saboda kasancewar su sun fi sauki, sannan ba Nigeria ce kawai take da shemomi ba a Muzdalifa, daga cikin kasashen da suke zaune a Muzdalifa akwai:

FARANSA, INGILA, MURITANIYA, BANGALADESH, CHAINA, PAKISTAN, INDIA, KARLA,  AFGNISTAN, TURKISTAN,

da wasu daga cikin Agencies na cikin  Saudiyya masu araha.

*2.* Samawa alhazan Nigeria wuri kusa da wajan Jifa, zai jawo kudin hajji ya kara tsada, ta yadda zai gagari talaka, saboda duk shemar da ta fi kusa da wajan Jifa to tafi tsada.

*3.* Akwai  Agencies  da yawa na bakaken fata wadanda suke zaune a kusa da wajan jifa, amma suna da tsada, wannan sai  ya nuna ba kasancewarsu 'yan Afrika ba ne  yasa ake ba su  wuri mai nisa ba, mas'ala ce ta kudi kawai.

*4.* Jifan Shaidan ibada ce tabbatacciya daga manzon Allah s.aw, wacce ya yita kuma ya umarci  mutane su koya a wajansa, kamar yadda ya tabbata a hadisin da Muslim ya rawaito a  lamba ta: 3197, wannan sai ya nuna hana bakaken fata zuwa jifan Shaidan sabawa nassi ne karara.

*5.* Dukkan ayyukan da shari'a ta yi umarni da  su ba sa rabuwa da wahala, wacce za'a iya jurewa,  wannan ya sa aka siffanta su  da TAKLIF, kamar yadda ya tabbata a ilimin Usulul-fiqh, Hana Alhazan Nigeria jifan Shaidan saboda wahalarsa, rashin kulawa ne da ka'idojin   ilimin MAKASIDUSHSHARIA.

*6.* Jifan Shaidan wajibi ne a wajan malamai da yawa, saboda Manzon Allah ya yi shi kuma ya umarci mutane su yi koyi da shi, In da ace zai kai zuwa ga halaka, tabbas ana iya barinsa saboda ka'aidar: لا واجب مع العجز, duk sanda aka samu kasawa wajan aikata wajibi to yana faduwa, saidai har yanzu ba'a samu ba, tun da Shari'a ta ba da damar yin jifa tun daga safe a ranar sallah har zuwa dare, tun daga zawalin rana a ranakun 11-13, har zuwa dare,  yana daga cikin ka'aidojin sharia: Hukuncin sharia yana zagayawa ne da sababinsa.

*7.* Hukunce-hukuncen sharia ba sa bambanta daga baki zuwa fari, saboda Annabi  s.a.w. an aiko shi ne zuwa dukkan mutane kamar yadda  aya ta: 28 a suratu Assaba'i ta tabbatar da hakan.

*8.* Ayoyin alqur'ani da hadisan za'a iya jawowa akan faduwar jifa saboda tirmitsitsi, suna magana ne akan wahalar da ta wuce wacce aka saba da ita,ko kuma wani uziri da sharia ta yadda da shi, amma ba wahalar da aka saba da ita ba a yawancin hukunce-hukunce.

*9.* Hajji ginshiki ne daga cikin turakun addinin musulunci, wanda yake da bangarori da yawa, barin wani sashe daga cikinsa ba tare da uzuri ba yana iya gurgunta shi, babu mamaki kuma ba za ka sake samun damar yin wani ba.

*10.* Allah ya sanya ibadoji da yawa a cikin aikin hajji saboda mutane su samu lada cikin sauki, ya kamata  ka dage wajan yin kowacce  ibada ba tare da nakasu ba, in har ka samu ikon hakan.

Allah ne mafi sani.                                              

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA                         

8 Zul-hijja 1437

10\9/2016

 

319. TAMBAYA

KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR IDI, MENENE HUKUNCIN?

 

Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka. Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan.

Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin shi. Allah ya bada ikon amsawa.

 

Amsa

Wa'alaikum assalam,

Amin Allah ya amsa adduarka.

Malamai sun yi sabani game azumin kaffara idan ya ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu :

1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

2. Ya  wajaba ya  sha azumi a ranar idi,  saboda yin AZUMI  haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin Umar dan khaddabi ya tabbatar,  wannan yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da Sharia ta yi masa  izni.

Zance mafi inganci shi ne na Biyu,  saboda idan hani da umarni suka ci karo da juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda  Idi ko tafiya ko haila.

Don neman Karin bayani duba: Al-Muntaka min Fataawa Alfauzaan 1/152

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

31/08/2017

 

320. TAMBAYA

ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

 

Assalamu alaikum malam Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci

 

Amsa

Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa : suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka

*1.* Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su .

*2.* Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.

*3.* Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa.

*4.* Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta 28

*5.* Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci.

*6.* Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.

*7.* Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.

*8.* Barin baccin da ba shi da amfani.

*9.* Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka.

*10.* Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata.

Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci.

Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22

Allah ne ma fi sani

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

17/8/2014

No comments: