321. TAMBAYA
MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?
Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka.
Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Bai halatta ga mai takaba ba ta fita zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031) inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna
a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki
kammala iddarki"
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba
ba za ta fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a sharia.Imamu
Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi bayani cewa "Dukkan
Mata ana fitar da su daga gidanjansu Don su halarci idi, in ban da wacce take
iddar mutuwa.
Allah ne mafi Sani
Dr. Jamilu Zarewa
03/09/2017
322. TAMBAYA
Assalamu alaikum
Malam me hukuncin wanda ya qara gashi akansa irin
wanda maza suke zuwa ana musu surgery ashuka musu gashin musamman ga masu sanko
ko kuma waenda gashin kansu ke cincinyewa wai saboda su zama dai dai da sauran
Amsa
Wa alaikum assalam,
Bai halatta
ga namiji ya kara gashi ba, saboda hakan
canza halittar Allah ne.
Kasancewar Allah ya haramtawa mata kara gashi a
cikin hadisai ingantattu duk da cewa suna tasowa NE a cikin kwalliya kamar
yadda ayar Suratu Azzukruf ta tabbatar, hakan sai ya nuna namiji ne ya fi
cancanta da haramcin, tun da shi ba'a yi
shi don Ado ba.
Malamai suna cewa duka nassoshin da suke haramtawa
mata kara gashi, to maza ma suna ciki,
amma an kebance mata ne da haramcin saboda su ne suka fi yawan aikatawa.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
03/09/2017
323. TAMBAYA
Assalamu alaikum dr. Ina maka fatan alheri da
fatan anyi sallah lfy don Allah dr. ina da tambaya kamar haka? Mutum ne ya mutu
ya bar mace da yara maza 9 da mata 12 da kudi naira miliyan daya da dubu dari
to malam ya kason zai kasance Allah ya kara lfy Allah yasa kayi hajjin mabruor.
Amsa
Wa alaikum assalam, Za'a raba kudin gida takwas,
sai a bawa matar mamacin (137,500), ragowar (962,500) sai aka sa su gida
talatin kowanne namiji ya dau kashi biyu, tun da su tara ne, kowacce mace ta
dau kashi daya tun su (12).
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
06/09/2017
324. TAMBAYA
Assalamu alaikum, mutum ne yake cikin halin rashin
lafiya, kuma al'ummah da suke tare ba masu taimakawa ne ba,gashi wannan ciwon
nason ya hallaka shi, shi kuma ba shi da kudi kuma ba shi da hanyar kudi, malam
shin zai iya karbar kudin LOAN na govt don surika cirewa duk wata, ko babu
halin haka nagode Allah yakara karfin imani da basirah
Amsa
Wa'alaykumussalam,
Ya halatta ya amshi rancen mai ruwa, mutukar abin
da yake damunsa, ya kai wancan halin da ka ambata, saboda larura tana halatta
abin da aka hana, saidai ya wajaba ya amsa gwargwadon bukata .
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
3\6\2015
325. TAMBAYA
Assalamu alaikum.Don Allah malam ya matsayin
mutumin da ya sha nonon matarsa, ya
aurensu yake ?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka
jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa
da ita lokacin da take haila, don
haka ya halatta ka tsotsi nononta
mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani
akan halaccin hakan zuwa maganganu guda
biyu :
1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake
haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa" , Bukhari lamba ta
: 5102, ma'ana lokacin da ba zai iya
wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne
bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci
matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim,
don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba
ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha
nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya
sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin
malamai yana da kyau.
Don neman
Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67
Allah ne
mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
1\11\2014
326. TAMBAYA
Assalamu Alaikum.
Don Allah ataimake ni akan wannan tambayan, mutum
ne yarasu bashi da kowa sai mahaifinsa da kaninsa 1 Da kannansa mata 2 ,toh ya
za'ai masu rabon gado?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Mahaifinsa ne zai cinye dukkan dukiyar.
'Yan'uwan mamaci ba sa gado mutukar akwai Ubansa
yana raye.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
11/09/2017
327. TAMBAYA
Assalamu alaikum. malam don Allah ina da tambaya
da fatan za'a amsamin, wai mutum zai iya rabawa iyalansa gadansa kafin yamutu
wai hakandin ya halatta? nagode
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa malamai suna cewa hakan bai inganta ba,
saboda dalilai, ga wasu daga ciki :
1. Hakan yana daga cikin gaggauta abin da Allah ya
jinkirta, saboda Allah ya sanya rabon gado ne, bayan mutuwa.
2. Zai iya
yiwuwa daya daga cikin iyalan nasa ya
mutu kafin shi, ka ga sai a samu kwan-gaba kwan-baya.
3. Yana iya jawo hassada saboda daya daga cikin
magadan zai iya yin kasuwanci da gadon da aka ba shi ya samu riba mai yawa
kafin magajinsa ya mutu, wanda hakan zai iya kawo hassada tsakanin magada, don
za su ga da ba'a yi gaggawar rabawa ba da ya kasance daga cikin rabonsu.
4. Yana daga cikin sharudan gado tabbatar da
mutuwar wanda za'a gada .
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
6\7\2015
328. TAMBAYA
Assalam alaikum malam ina da tambaya; misali ni
brikilane kuma na kasance musulmine sai aka ban contrc din gini na church,
ogana ya ce mu za muyi; yaya matsayin mu yake idan munyi wannan aikin?
Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa malamai sun yi bayani cewa : bai halatta
musulmi ya zama Birkila a Chochi ba, saboda hakan yana daga cikin
taimakawa aikata zunubi, kuma zai iya jawowa mutum ya ga yadda ake shirka da
Allah, wanda hakan zai iya masa tasiri.,
Allah madaukaki yana cewa " kada ku yi
taimakekeniya wajan aikata sabo",
" suratul Al-maidah aya ta : 2, sannan duk abin da yake kaiwa zuwa barna,
to zai zama haramun ko makaruhi.
Don neman kari bayani duba : Al'umm ta
Shafi'i 4/213.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
19\5\2015
329. TAMBAYA
Assalamu alaikum waraha matullah.malam mijina ne
ya rasu ya barmu da abukiyar zamana da yara ukku mata da mahaifiyarshi inda
yabar gida da mota malam ya hukuncin rabon gadon yake nagode
Amsa
Wa alaikum assalam,
Za'a raba
abin da mijinku ya bari gida (24), a bawa 'ya'yansa mata kashi (16),
mahaifiyarsa kashi (4) ku kuma matansa a ba ku kashi (3) ku raba, ragowar kashi
dayan sai a bawa wanda yafi kusa da mijinku daga mazan da sharia ta tabbatar
suna gado .
In kuma babu sai a yagalgala shi a tsakaninku.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
16/09/2017
330. TAMBAYA
Assalama alaikum. Malam dan Allah
Ina aiki ne
akarkashi wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai kudisa bana halal bane wasu suce dan luwadi ne
wasu kuma suce kudin lukudu ne
ina so insan yadace nacigaba damai aiki ko inbari Allah y
kara lpy da ilimi da kafin basira ameen
Amsa
Wa alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan
kafin ka yanke hukunci.
Ba'a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato
mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a
cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan.
Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani
kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.a.w. ya yi mu'amala da
yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
16/09/2017
331. TAMBAYA
Assalam Alaikum.
Malam, menene hukuncin amfani da *LAYA KO GURU a
musulunci?
Allah yasa mu dace.
Amsa
Wa alaikum assalam,
To dan'uwa Layu da guru sun kasu kashi biyu:
1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko
sunayan aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur'ani ba, wannnan malamai sun
cimma daidaito game da haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna
Adda'imah 2/212 saboda fadin Annabi S.A.W. (LAYU da kuma abin da ake daurawa
mace don miji ya sota shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da Imamu Ahmad
ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi S.A.W. yake cewa: (Wanda ya
rataya laya to ya yi shirka, shima wannnan hadisin Albani ya inganta shi a
Silsila Sahiha.
Hadisan da suka gabata suna nuna haramcin daura
Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum
daga musulunci.
2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani ko hadisai
ingantattu, wadannan na'u'i malamai sun yi sabani akansu:
A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da
kuma karatun alqur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya dogara ga
Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga cikin
magabata.
B. Ba su halatta ba saboda Ba'a samu Annabi S.A.W.
ya yi ba, da hakan sharia ne da an gan shi ya yi ko da sau daya ne a
rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da Alqur'ani zai jawo a wulakanta
su tun da za'a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye
hakan kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun
da suke daga Alqur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga manzon Allah
S.A.W, sannan shariar musulunci ta halatta mana addu'o'i da yawa na neman
kariya wadanda suka wadatar da mu daga layu.
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba: Taisirul Azizil Hamid
shafi na : (136) da kuma Ma'arijul Kabul 2/510
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
4/10/2017
332. TAMBAYA
Assalamu alaikum
Don Allah Malam wata tambaya aka yi min, shi ne na
ke son a taimaka min wajan ba da amsa, tambayar ita ce : me ya kamata mai yaron
ciki ta kula da shi ?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To malama akwai abubuwan da ya kamata mace ta kula
da su, lokacin da take da ciki, ga wasu daga ciki :
1. Ki yi kokari, ki dinga cin halal, saboda
lokacin da yaro yake ciki, na daga cikin lokutan da yaro yake ginuwa, don haka,
idan kina cin haramun, yaron zai ginu da ita, sai Allah ya fara cirewa
gabobinsa son alkhairi, tun yana yaro, domin duk jikin da ya ginu da haramun
zai zama mai kasala wajan aikata abin da Allah yake so, kamar yadda malamai
suka yi bayani.
2. Wasu malaman suna cewa : yawan saduwa yana
karfafa yaro a ciki, saboda Annabi s.a.w ya kamanta ciki da shuka, kamar yadda
ya zo a hadisin Abu dawud, mai lamba ta :
1847, kuma shuka tana kara karfi duk lokacin da aka bata ruwa.
3. Neman masa tsari daga shaidan, kamar yadda
mahaifiyar nana Maryam ta nemarwa 'yarta tsari, lokacin da ta haife ta.
4. Nisantar duk wani abu da zai cutar da shi,
saboda musulunci ya yi umarni da kula da rai, don haka zai yi kyau a matsayinki
na sabon aure, ki nemi shawarar magabata da kuma likitoci, saboda ki gujewa
abin da zai cutar da yaronki.
5. Zuwa asibiti, lokaci-lokaci don tabbatar da
lafiyar yaron.
ALLAH SHI NE MAFI SANI.
Dr. Jamilu Zarewa
16\6\2014
333. TAMBAYA
Assalamu Alaikum
malam AWAL
ga tambayata kamar haka minene hukuncin wanda yatararda liman Acikin sallar
Isha sai yasami raka biyu nakarshe idan
zaikawo cikon raka watarana yakan bayyana karatun fatiha da sura batareda yayi
Ba,adiyaba ko Qabliyya shima yaya hukuncinsa yake?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Wato an samu sabani ne tsakanin malamai wajen
wanda ya samu raka'o'i biyun karshe tare da liman, shin sune na farkon sa ko
kuwa sune na karshen sa shima, wadan da sukace abinda ya samu sune na farkon sa
kaga kenan zai ciko biyun karshe a yadda suke wato fatiha kawai kuma a asirce,
amma wadan da suka ce abinda ya samu sune na karshen sa toh kaga zai rama biyun
da suka wuce shi kenan, a yadda suka wuce shi wato fatiha da sura kuma a
bayyane dukkan ma'abota wadannan maganganun suna da madogara daga abinda suka
fahimta na hadisan manzon Allah, amma abinda yafi rijaye wajen malamai shine
maganar farko wato abinda ya samu sune na farkon sa don haka zai cika abinda ya
rage masa, wato zai karanta fatiha kawai a boye a duk raka'o'in biyu.
Wannan shiyafi dacewa da fadar manzon Allah...
ما أدركتم فصلوا وما فاتكم فأتموا...
Duk abinda kuka riska ku sallata kuma Abinda ya
wuce ku sai ku ciko..
Wallahu A'alam.
Malam NURUDDEEN MUHAMMAD(MUJAHEED)
26/09/2017
334. TAMBAYA
Assalamu alaikoum malam muna so a fidda mu cikin
shakku. Manzon Allah SAW ya hana ayi azumin nafila a ranar Asabar toh yaya
zamuyi? ayi mana bayyani game da azumin assabar na tasu'a
Za mû yi shi ko kuma tsallakeshi za mû yi saï mû
azumci ranar ashura lahdi?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Babu komai zaku iya yin azumin ku, hanin dake
cikin Hadisin Abdullahi bin Busrin al'maziny na kada ayi azumi ranar asabar
malamai sun kebance shi da halaccin yi saboda hadisai masu yawa daga cikin su
akwai hadisin Abu Huraira wanda ke cikin Bukhari ( kada kuyi azumi ranar
Jumma'a saifa in kun hada da na yinin kafin Jumma'a din (wato alhamis kenan) ko
yinin bayan Jumma'a din (wato asabar kenan)
Da kuma hadisin Juwairiyya, wanda manzon Allah ya
shigo wurin ta ranar Jumma'a sai ya tarar tana azumi sai ya tambaye ta kinyi na
jiya tace a'a sai yace zakiyi na gobe sai tace a'a sai yace to in haka ne ki
karya azumin ki...
Da ire iren wadannan hadisan malamai suka ce hanin
ya shafi kebance ranar asabar din ne ita kadai.
Amma idan za'a hada da wata rana toh babu laifi,
Imam Ibn Kudaama a cikin littafin sa Al'mugni yace
makaruhi ne kebance ranan asabar da zumi amma in za'a hada da wata ranar toh
babu karhanci.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
26/09/2017
335. TAMBAYA
Assalamu alaikum.
Shin idan miji ya saki matarsa sai bayan mako biyu
Allah ya yi masa rasuwa zatayi takaba?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Macen da mijinta ya sake ta kafin ta kammala idda
sai mijin ta ya rasu, malamai sunyi maganganu uku:-
(1) ya zamanto sakin akwai kome a cikin sa wato
saki daya ko biyu, toh malamai sunyi ittifaqi zata fita daga idda ta koma
takaba kuma tana da gado, domin mace matukar tana cikin idda bata fita daga
hurumin mijinta ba don haka ma yana da ikon dawo da ita ba tare da andaura aure
ba, don bata halatta ga wani sai bayan idda.
(2) ya zamanto sakin babu kome a cikin sa kamar
saki uku kuma mijin yayi sakin a lokacin yana lafiya lau, toh a wannan hali ba
zata ci gado ba bisa ijma'in malamai sunce domin alaqar dake tsakanin su ta
yanke.
(3) ya zaman toh sakin babu kome a cikin sa wato
saki uku amma a lokacin sakin mijin yana kwance ba lafiya/yana jinya (ciwon ajali)
ya zamanto nufin mijin shine haramta wa matar cin gado toh a irin wannan
matsalar malamai sunyi sabani:
* Mazhabar imam A shafi'i sunce ba tada gado / ba
zatayi takaba ba.
* Mazhabar Abu hanifa sunce tana da gado/takaba
matukar tana cikin idda hakan ta faru.
* Mazhab na Imam Ahmad bin hambal suce za taci
gado/takaba matukar ba ta auri wani mijin na daban bane.
Aduba littafin (Al'mugni 9/194-196)
Da yawa daga cikin malaman wannan zamann sun tafi
akan ra'ayin mazhabar iman Ahmad kamar irin su Sheikh Bin Bazz da Sheikh Ibn
Usaimeen da Sheikh Swaleh fauzan da sauran su...
A duba ( Fawa'idul Jaleelah Fil mabaahithul
Fadiyya na Sheikh bin bazz Shafi na 6) da (tahkikatul Fardiyya Fi mabaahithul
fardiyya na Sheikh swaleh fauzan shafi na 33- 36).
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
28/09/2017
336. TAMBAYA
Assalamu Alaikum, mutum musulmi zai iya shiga
chikin church domin halartar aure na aboki ko abokiyar karatun sa?
Amsa
Wa alaikum assalam
Yawanci auran Crista a wannan zamanin ba ya rabuwa
da kade-kade da raye-raye, da roko da Neman albarka a wajan Jesus a matsayinsa
na Allah a Wajansu, da Addu'o'i Wadanda suka sabawa koyarwar addininmu.
Wannan ya sa barin halartar ya fi dacewa da
sharia.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
05/10/2017
337. TAMBAYA
Assalamu Alaikum Dr. dan Allah inada tambaya akan
matar da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata daga baya kuma
sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu yakan iya dawowa ko bayan wasu awoye shin
ya hukuncin sallar ta? xata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko xata rika yin
wanka duk sanda ya dauke tayi rankon sallolin baya ne.
Nagode
Amsa
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa mutukar cikin ya
kai wata hudu kuma jinin da yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama
jinin biki, kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to mutukar ya zo
da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama haila, tun da a zance mafi
inganci mai ciki tana iya yin haila.
In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta
ta yadda ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki iya
jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallaolin da aka yi su kina
da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki, babu kunci da damuwa a
cikinsa, kamar yadda aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
03/02/2016
338. TAMBAYA
Assalamu Alaikum
Tambaya
daga jahar Taraba Suna so Dr ya amsa musu a wannan zaure mai albarka.
Wata ce take da Miliyan daya tana so tafir da
zakka nawa ne ya kamata ta fitar dashi?
Allah ya tsare mana Dr ya yi mashi sakamako da
gidan aljannah fiddaus.
AMSA
Wa alaikum assalam,
Idan ta
mallaki miliyan daya (1,00000), kuma su ka yi shekara daya a wajanta, to za ta
fitar da dubu ashirin da biyar (25,000), wato daya cikin arba'in din abin da ya
mallaka.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
10/10/2017.
339. TAMBAYA
Assalamu alaikum, Mallam Na kasance ina tsotsan
azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina
matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian
ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu
Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata,
saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba
maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna
bada shawarar cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda
neman kariya
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya
ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan
bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce
nassi ya togace.
Allah ne mafi sani.
Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul
Khalil 3\406,
Dr. Jamilu Zarewa
20/12/2014
340. TAMBAYA
Assalamu alaikum.
yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala ya bashi
karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna
Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi???
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa
abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu
malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin
bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.
Duk wanda bai samu damar yiwa dansa Akika ba a
kwanakin da aka ambata a sama, to
babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi
duk lokacin da ya samu dama.
AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa
a lokacin da Annabi S. a. w ya ambata,
in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha
1/615.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/08/2017
No comments:
Post a Comment