281. TAMBAYA
WANDA YA SAKI MATARSA A ZUCI BA TA SAKU BA!
Assalamu Alaikum,
Don Allah Malam, idan mutum da dare ya qudurta zai
saki matarsa zuwa safe, amma bai furta ba zuwa safiyar kuma sai ya canza
shawara. Shin yaya matsayin auren yake?
Allah Ya taimaka.
AMSA:
Wa alaikumus assalam, Mutukar bai furta ba kuma
bai rubuta ba to Ba ta saku ba, saboda Allah ba Ya kama Al'ummar Annabi
Muhammad S. A. W. da zancen zuci kamar
yadda hadisi ingantacce ya tabbatar.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
01/08/2017.
282. TAMBAYA
WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI, BAI TUBA BA?
Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah mene ne Hukuncin Mai shan taba (sigari), har ya
mutu bai tuba ba?. Na gode.Amsa:
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa
barakaatuhu, Dukkan wanda ya mutu yana shan taba (sigari) bai tuba ba, yana
karkashin ikon Allah, in ya so ya gafarta masa, in ya so ya kama shi da zunubin
shan tabar da ya yi, saboda shan taba haramun ne, saboda ta kunshi cuta, kuma
duk abin da yake cuta ne tsantsa haramun ne, kamar yadda ayoyin Alqur'ani da
hadisan manzon Allah suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
11/05/2016
3/8/1437
283. TAMBAYA
HUKUNCIN YIN DAWAFI DA SAUKAR AL-QUR'ANI GA MAMACI
Wani lokaci na kan yi dawafi ga wani daga cikin
makusantana ko Mahaifina ko Kakannina wanda suka rasu, mene ne hukuncin haka?,
sannan mene ne hukuncin sauke musu al-Qur'ani?. Allah Ya saka muku da alheri.
AMSA:
Abu mafi dacewa shi ne barin wadannan abubuwa da
ka ambata saboda babu wani dalili da ya yi nuni akan haka.
Sai dai shari'a ta baka dama ka yi sadaka ga wanda
kake so daga cikin makusantanka da ma wanda ba su ba matukar Musulmai ne, da yi
musu addu'a da yi musu Hajji da Umra.
Amma dangane da yi musu salla da dawafi ko karatun
al-Qur'ani, abu mafi dacewa shi ne ka bar shi domin babu dalili akan yin haka.
Hakika wasu daga cikin Malamai sun halatta haka ta hanyan qiyasi akan sadaka da
addu'a, amma abu mafi gamewa shi ne kar ka yi (domin asalin kowace ibada
tsayawa ake yi har sai an samu umurni daga Allah ko ManzonSa).
Ga Allah nake fatan dacewa.
Amsawa:
Abdulaziz Bn Baz, Rahimahullah
A duba littafin فتاوى
المرأة المسلمة shafi na 451-452.
Tattarawa:
Umar Shehu Zaria
284. TAMBAYA
HUKUNCIN FADIN "BALAA" A KARSHEN SURATU
ATTIN
Assalam alaikum warahmatallah Malam dafatan kana
lafiya amin. Malam akwai addua da akeyi a yayin da aka karanta Suratin Tin a
karshen surar wato "Balaa nahanu ala zalika laminash shahideen". Ya
ingancin wannan addua yake? Wassalam Allah ya kara lafiya.
AMSA
Wa alaikum assalam, akwai hadisin da Abu-dawud ya
rawaito mai lamba ta (887) wanda ya tabbatar dá hakan, saidai malaman hadisi
sun raunana shi kamar Nawawy a cikin Al-majmu'ú 3/563.
Saidai wasu daga cikin malaman Malikiyya sun só
fadin hakan in an karanta karshen Surar WATTIN, hakanan wasu a cikin Hanabila.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
04/08/2017
285. TAMBAYA
YAUSHE AKE YIWA YARO KACIYA?
Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa
yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa ?
Amsa
Wa'alaikum salam,
To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya
kayyade wani lokaci da za'a yiwa yaro
kaciya, saidai malamai suna cewa: babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa
a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda
idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba'a
yi masa kaciyar ba, daga cikin ka'aidojin malamai shine duk abin da wajibi ba
zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa,
tun yana dan karami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7 \ga
haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349
Dr. Jamilu Zarewa
18/11/2014
286. TAMBAYA
INA SON DALILI AKAN KACIYAR MATA
Assalamu alaikum, don Allah malam a taimaka min da
amsar wannan tambayar, ko Qur'ani da hadisi sun yi Magana akan halarcin kaciyar
mata, ko kuma wani daga cikin magabata na kwarai ya yi Magana akan haka?
Amsa
Wa'alaikum salam,
To 'yar'uwa akwai hadisai da suka zo akan cewa:
mustahabbi ne, yin kaciyar mata, saidai an yi sabani akan ingancinsu, wasu
malaman sun raunana su, wasu kuma sun inganta su. Baihaki a Sunanu Assugrah a
hadisi mai lamba ta: 3712, ya rawaito mustabbacin yin kaciyar mata daga Ibnu
Abbas da sanadi mai kyau.
Hadisin da
Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a lamba ta: 108, daga Nana A'isha tana
cewa:
"Idan kaciya ta hadu da kaciya, to wanka ya
wajaba"
na nuna cewa : al'ada ne yiwa mata kaciya a
zamanin Annabi (S.A.W) Ibnu- Abi-zaid Al-kairawany ya ambata a Risala shafi na:
410, cewa: yin kaciyar mata mustahabbi ne. Don neman Karin bayani duba Al-mugni
1\101.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
12\5\2015
287. TAMBAYA
BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI
Assalamu Alakum.
Malam ina da tambaya kamar haka,shin tabar wiwi
tana daukan dukkanin hukunce hukuncen da suka hau kan giya (barasa)ko kuwa
akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya a Zauren Fiqhu.nagode.
Amsa
Wa alaikum assalam,
mutukar ta
amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za ta dauki dukkan
hukunce-hukuncen giya na haramci.
Annabi s.a.w. yana cewa "Dukkan abin da yake
sanya Maye giya NE, kuma dukkan giya
haramun ce" kamar yadda Nasa'i ya
rawaito a hadisi ingantacce, wannan sai
ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
05/08/2017
288. TAMBAYA
TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA AURE ?
Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da
ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to
malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?
Amsa
Wa'alaikum salam,
In har an San tana da ciki aka yi auran wannan
hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai
inganta ba a zance mafi inganci, amma in
haihuwa ta yi Kafin ta cola wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to dansa
ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife
ciki a watanni shida.
Auran dá
aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba zá'à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba
shi ya yi ba.
In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Duk wanda ya
yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar
waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito.
In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta
aure, musamman in bai sani ba saí dá aka
daura.
Allah ne
mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
07/08/2017
289. TAMBAYA
SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN
YA YI MIN KOME?
Assalamu Alaikum.
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda,
saura kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome, amma bai sanar
da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki, ko kuma na kyale shi na yi aurena
? saboda gaskiya ina son wancan, amma
kuma ba na so na sabawa sharia ?
Amsa
Wa'alaikumsalam,
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa
matarsa kome mutukar tana cikin idda,
kamar yadda aya ta :228, a suratul
bakara take nuni zuwa hakan, Amma
mutukar bai yi mata kome ba har ta
kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.
Idan ya yi da'awar cewa ya yi mata kome tun tana
idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gasgata
shi ba, sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar hakan.
Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar
da za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake kin matarsa, zai
iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan yasa malamai suka ce sai ya kawo
shaidu za'a gaskata shi, idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auran ta.
Saidai wasu malaman suna cewa : idan har matar ta
gaskata shi, to ya isa, ko da bai kawo shaidu ba.
Allah ne mafi sani.
Duba : Al-mabsud 2\23 da Mawahibul-jalil 5\408
Dr. Jamilu Zarewa
29/12/2014
290. TAMBAYA
MIJINA YA YI MIN KOME, BAYAN NA SHIGA JINI NA UKU
?
Assalamu Alaikum
Malam inada
tambaya danAllah.A fahimta ta idan aka saki mace saki daya iddarta tsarki uku
ne dalili fadin Allah subhaanahu cikin suratul bakara aya 228. Sai nazo naji
sharhin wani malami cewa"idan aka saki mace cikin tsarki zata kirga wannan
tsarki a matsayin tsarki 1,idan tayi al'ada ya zama tsarki na 2 kenan idan ta
sake al'ada tsarki uku kenan ma'ana ta gama iddarta. Ko kuma yace idan tana
al'ada aka saketa to idan ta sake wata al'adar zata ce 1,ta kara wata tace 2,ta
kara wata tace 3,ta gama iddarta kenan. Tambaya anan malam itace ,saboda
fahimta ta ta tsarki uku,mun sami sabani da miki na har saki ya auku kuma ina
cikin tsarki,nayi tsarki na daya,nayi na biyu ina cikin al'ada ta uku ya ce ya
maidani kuma na koma. duba da sharhin malamin da na fada maka ina matsayin kome
na a shari'a ?danAllah malam ina cikin fargabar ko mun sa6ama shari'a .idan ko
mun sa6a malam mecece mafita? Allah ya karawa malam lafia da basira Amin.
Amsa
Wa'alaikummussalam,
'Yar'uwa in har kin shiga jini na uku, a iddarki,
ta bayan saki sannan mijinki ya miki kome, to komen ya inganta a bisa mazhabar
Abu Hanifa, amma a fatawar Imamu Malik kin kammala idda, tun da kın shiga cikin
jini na uku, saidai duk mazhabar da kika dauka kika yi aiki da ita a nan wurin,
ta yi, tun da lafazin Kur'i da ya zo a aya ta : 228 a suratul Bakara yana
daukar ma'anar haila, yana kuma daukar ma'anar tsarki, Don haka in har kin
tabbata kafin kammala jini na uku ya miki kome, to cigaba da mu'amalar auranku
babu matsala.
Allah ne
mafi Sani.
Don neman Karin bayani duba: Tafsirin Ibnu Kathir
1\542.
Dr. Jamilu Zarewa
29/12/2014
291. TAMBAYA
MUTUM NE YA SIYO HATSI, BAYAN YA SIYO, SAI
FARASHIN HATSIN YA TASHI, SHIN YA HALASTA YA QARA KUDIN KO KUWA ZAI SAYAR A
YANDA YA SAYO?
Assalamu Alaikum warahamatullah
malam,mtum ne ke sana'a irin su shinkafa,mai,wake da sauransu ,toh sai ya siyo su a farashin da yake siyarwa,ana
haka sai farashi ya hau, toh zai sayar a farashin daa ne kokuwa zai qara ne
ya cigaba da siyarwa?
Amsa
Wa alaikumus salam
Shari'ar musulunci ba ta qayyade ma dan kasuwa nawa zai sayar da kayansa
na kasuwanci ba, sai dai Annabin rahama (SAW) ya yi addu'a ga dan kasuwa ya ce:
"Allah yayi rahama ga dan kasuwan da zai saro da sauqi, ya sayar da sauqi"
A saboda haka; babu wata tanadaddiyar doka a
shari'a da ta iyakance ma dan kasuwa yadda zai saida kayansa da ya saro, sai
dai ya tausaya ba tare da ya cutar da kansa ba.
A kan haka; ya ga dama ya cigaba da saida tsohon
akan farashin da, har ya qare, sannan ya tada farashin, ko kuma ya canza
farashin kafin qarewar tsohon don in yaje sari yanzu zai sayo da tsada.
Imam Ibn Hazm ya fada a
cikin"Almuhalla": *Ba Wanda ke
da ikon qayyade ma dan kasuwa yadda zai sa farashin kayansa; hatta gwamnati
Amma Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah ya ce: *Idan
gwamnati ta fahimci yan kasuwa na wasa da farashi;to ya halasta ta qayyade
farashi
Wallahua'alam.
Amsawa
Malam Basheer Lawal Muhammad Zaria
07/08/2017
292. TAMBAYA
WANDA YA SAKI MATARSA ACIKIN MAYE, BA TA SAKU BA!
Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne
yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye
yace na zo nasameshi, nii kuma banzoba saboda bana son abin da yakesha
na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na. Shin yaya auren mu? Allah ya
saka da alheri.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Malamai sun
yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:
1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan
ya saki matarsa, tabbas sakin ya
auku, saboda shan giya sabon Allah
né, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'à yi masa uzuri ba, wannan ita
ce maganar Abu-hanifa da Malik da Shafii
a daya daga cikin zantukansa.
2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin dá Má'iz ya zo ya tabbatarwa Annabi S. A. W. ya yi zina saidá
ya tambaye shi ko ka sha giya né, kamar
yadda Baihaki ya rawaito a Sunanul-kubrah,
hakan saí ya nuna mashayin giya ba'a amsar maganarsa.
Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu
Abbas cewa : sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Sabá musu ba a
cikin Sahabbai.
wannan ita
ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya .
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik
Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da yake
fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci wanda
Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi
saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar
yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'í ta
tabbatar da hakan
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba : Al-Mugni 7/289 dá
kuma Sharhul Munti'i 10/233
Dr. Jamilu Zarewa
9/08/2017
293. TAMBAYA
YA HALATTA NA SAYI KARE SABODA GADI A GIDANA ?
Assalamu alaikum. Dr. Mene ne hukuncin ajiye kare
a gida saboda gadi? Allah muke roko ya kara wa Dr lafiya da basira Ameen.
Amsa
Wa alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari
da Muslim cewa: "Mala'iku ba sa
shiga gidan da yake akwai hoto ko KARE a ciki.
A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya
rawaito Annabi s.a.w. yana cewa: "Duk Wanda ya rike KARE, in ba Karen noma
ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa
manyan lada guda biyu a kowacce rana.
Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN
GADI akan wadancan nau'ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta
musulmi ya riki Kare saboda gadi in har akwai bukatar hakan.
Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne,
saboda Annabi S.a.w ya hana cin kudin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma
ya kira Shi da dauda.
Duk da cewa an halatta wadancan nau'ukan guda hudu
saboda bukata saidai bai halatta a siyar da su ba, saboda Ka'ida sananniya a
wajan malaman Fiqhu wacce take cewa:
ما جوز للحاجة لا يجوز أخذ العوض عليه
Idan mutun yana bukatar daya daga cikin wadanchan
nau'uka na karnuka guda huɗu da suke
halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba, ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar
yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya
fada a littafinsa na Muhallah 4/793, Ka'ida tabbatacciya a wajan malamai tana
cewa:
ما حرم سدا للذريعة يباح للحاجة أو المصلحة الراجحة
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
16/05/2017
294. TAMBAYA
TSAKANI KAFIRI DA MACE MUSULMA, WA ZAN
ZABA ?
Assalamu Alaikum. Na karanta post din da kayi akan
Shugabancin Mata, inda ka nuna bai halatta mace ta yi shugabanci ba in ba na
gidanta ba, Ina so ka dan yi mana Karin bayani
idan aka samu takarar shugabanci tsakanin Kafiri da kuma Mace Musulma, wanne ya kamata mutane
su zaba a matsayin Shugaba?
Amsa
Wa'alaikum salam.
To dan'uwa amsa wannan tambayar yana da wahala,
saboda ban ga littafin da ya tattauna mas'alar ba, amma dai na nemi
taimakon amsa tambayar wajan babban
malaminmu Prof. Muhd Sa'ad Al-yuby, don haka ga abin da zan iya cewa:
Farko dai zaben kafiri haramun ne, saboda fadin
Allah madaukakin sarki "Kuma Allah bai sanya wata hanya ba ga kafirai akan
muminai" Nisa'i aya ta : 141, hakan sai ya nuna bai halatta musulmai su
sanya kafiri ya mulke su ba, Kamar
yadda zaben mace a matsayin shugaba shi
ma haramun ne saboda hadisin Abu-bakrah inda Annabi s.a.w. yake cewa ;
"Duk mutanen da suka sanya mace ta zama shugabarsu, to ba za su rabauta
ba" kamar yadda Bukhari ya rawaito
shi a hadisi mai lamba ta: 4425, Ibnul-kayyim yana cewa: kore rabauta dalili ne da yake nuna haramcin abu .
Bada'i'ul-fawa'id 4\812.
Saidai kamar yadda malaman shari'a suke cewa: duk
lokacin da abubuwa biyu haramtattu suka
hadu, ya zama dole sai an aikata daya
daga ciki, to sai a dauki wanda ya fi saukin haramci a aikata.
Idan muka kalli manufar shugabanci a musulunci, za
mu ga ta kunshi : jagorancin mutane da kuma tsayar da addini, wannan manufar
za ta fi tabbatuwa idan aka zabi mace
musulma, fiye da kafiri Crister.
Don haka mutukar matar tana da kokari wajan
addini, to ita ya fi kamata a zaba, ba don kasancewar ya halatta a zabe ta ba,
sai don kawai hakan ya fi saukin haramci, kuma babu yadda za'a yi sai a zauna
babu shugaba.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamil Zarewa
22/01/2015
295. TAMBAYA
HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana
addininta yana musuluncinsa ?
Amsa
Wa'alaykumussalam.
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren
ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin
suratul Ma'ida aya mai lamba ta:
(5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun
aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya,
haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri
Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794.
Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin
dayafi shine rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da
yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani
lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka
samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikin su.
Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga
cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu
dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
02/12/2016
296. TAMBAYA
MACE, ZA TA IYA YIN AURAN KASHE WUTA !
Assalamu Alaikum,malam menene
hukuncin wadanda sukayi auran kisan wuta suka
maida aurensu, kuma menene hukuncin auren
nasu?
Amsa
Wa alaikum as salam,
Auren kisan
wuta bai halatta ba. Saboda Annabi (S.a.w) ya la’anci wanda ya yi da kuma wanda
aka yi
saboda shi, kamar yadda Tirmizy ya rawaito
kuma ya inganta shi Idan miji ya yi aure da
niyyar halattawa mijin baya, auran batacce ne,
amma idan mace ce ta yı da wannan niyyar,
kuma mijin da ta aura bai sani ba, to auran ya
yi.
Saboda ba dole ba ne mijin ya sake ta. Yana
daga cikin Ka’idojin sharia:
ﻣﻦ ﻻ ﻓﺮﻗﺔ ﺑﻴﺪﻩ ﻻ
ﺃﺛﺮ
ﻓﻲ ﻧﻴﺘﻪ
Duk wanda
babu saki a hannunsa, to
niyyarsa ba ta da tasiri.
Allah ne
mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
27/12/2016
297. TAMBAYA
YAYI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YAYI
KAFFARA
Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne
ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani
auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.
Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga
Malam.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Auransa na
biyun ya inganta saboda ba su da alaka da juna.
Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku
ne, to wancan ziharin ya warware, amma in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai
halatta ya taba ta har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah
ya fada a cikin Al-Mugni.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2017
298. TAMBAYA
HUKUNCIN DILLANCIN AURE
Assalamu Alaikum,
Malam
menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu
mijin aure ?
AMSA
Wa'alaykumussalam,
Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar
da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan
kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake
cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da
zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun yi
sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da yaje
neman aure :
*1*. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da
tafin hannu ne kawai.
*2*. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta
a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya
baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai
san yanayin matar da zai aura. Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya
fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki
:
*1*. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar,
bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
*2*. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce,
ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta
ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda
yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton
na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
*3*. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya
wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
*4*. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin
aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna
ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne mafi sani
Amsawa
Dr. jamilu zarewa
22/11/2016
299. TAMBAYA
HUKUNCIN JININ BARI
Assalamualaikum, malam ina da tambaya, Dan
Allah idan
mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin
ya zaka na ciwo ko zata daina azumi sallah
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan’uwa wannan jini ba zai hana
sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa bane,
malamai suna cewa : duk cikin da ya zube
kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana
sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne
daga 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka
duk cikin daya zube kafin haka, to jininsa ba
zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma
mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa
ta fara bayyana, to za’a bar sallah da azumi.
Allah ne mafi sani.
30/11/2016
Dr. Jamilu Zarewa
300. TAMBAYA
ALAMOMIN KARBAR TUBA
Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da
mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya ?
Amsa :
Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai alamomin da
malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga
ciki
*1.* Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da
zai kusantar da shi zuwa ga Allah.
*2.* Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya
ga Allah.
*3.* Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba
daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .
*4.* Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta
tuba, a matsayin ni'ima daga Allah.
*5.* Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da
kafin ya tuba.
*6.* Yawan istigfari.
*7.* Son kusantar salihan bayi.
Allah ne ma fi sani .
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
5/6/2014
No comments:
Post a Comment