21. TAMBAYA
HUKUNCIN MUTUMIN DA YAKE TAKE WANDONSA
Assalamu alaikum,
Mene ne hukuncin mutumin da yake take
wandonsa, shin ya halatta a bi shi salla?
AMSA
Take wanda a Musulunci haramun ne
domin hadisai masu yawa sun zo suna hani akan haka, kuma ba lallai sai wando
ba.
Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama,
ya ce:
*"مَا أَسْفَلَ مِنْ الْكَعْبَيْنِ مِنْ
الْإِزَارِ فَفِي النَّارِ"* رواه البخاري (5787).
Duk abun da ya wuce idon sawu (na tufafi),
to yana wuta. Bukhari ne ya ruwaito hadisi na 5787.Malamai suka ce tun da har Allah
Ta'ala Ya yi barazana da wuta, to wannan ya nuna babban laifi ne.
Dangane da batun bin shi salla matukar
babu najasa a jikin tufan shi za a bi shi salla, domin laifin mai laifi bai
hana a karɓa sallansa
matukar ya yi ta yanda shari'a ta koyar kamar yadda Abdullahi Bn Umar ya yi
salla a bayan Hajjaj Bn Yusuf al-Thaqafee.
Wallahu A'alam.
Amsawa:
Sheikh muhammad bello Al-adamawiy,
Rahimahullah
22. TAMBAYA
HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA
Assalamu Alaikum
Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi
Da Fatan Za'a Fahimtar da ni. -wai Shin
Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka
Da Alkhairi .
Amsa
Wa'alaykumussalam.
To dan'uwa malamai da yawa sun haramta yin wasan
kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka :
1. Hakan zai iya bude kofar da wasu
masu kallon za su yi isgilanci ko ba'a
ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda
aya ta : 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.
2. Wasu daga cikin masu shirya film
din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin
musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a
matsayin Allah.
3. Irin wadannan wasannin na
kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da
matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma
ragewa annabawa kima ne.
4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar
Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi , kamar yadda ya zo a hadisi.
5. Kasancewar hakan zai jawo aki
girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan
mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
13/6/2014
23. TAMBAYA
MAHAIFIYATA TANA ZUWA WAJAN BOKA, INA
NEMAN SHAWARA?
Assalamu alaikum
Dan Allah malam a fitar dani cikin
duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata
naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma
likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi
mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta
kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar
kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman
ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta
halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin
da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta?
Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.
Amsa :
Wa alaikum assalamu To 'yar'uwa tabbas
ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar
ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta
hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma
aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu
Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai
a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.
Amma bai halatta ki taimaka mata ba,
wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a
wajen sabon Allah.
Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin
hikima, ki sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yana cewa :" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani
abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in" kamar yadda muslim
ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a wadannan
kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da
ita, a wani hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya je wajan boka ya
gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo
da shi" kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904,
kuma Albani ya inganta shi .
INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA
KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.
Allah ne mafi sani.
Amsaw:
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
8\3\2015
24. TAMBAYA
NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE
SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI
DAMAR KOME ?
Assalamu alaikum
Don Allah malam ka warware mana wannan
matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya
koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya
sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma
suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan
bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa
ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai naji daga gareka
Amsa
Wa'alaykumussalam
To dan'uwa idan abin haka yake kamar
yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in
ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun
yanke gaba dayansu .
Auren da kuka sake, ba zai goge sakin
da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka
sake auranta, da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun
malamai, amma tun da ba ta auri wani ba,
ya wajaba ku hakurewa juna .
Don neman Karin bayani duba : Al-mugni
na Ibnu-Khudaamah 7\388 .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
3\5\2015
25. TAMBAYA
AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI ?
Assalamu Alaikum
Malam don Allah ina da tambaya, don
Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci. Malam matsala ta
haihuwa greni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar
tsarin iyali don in huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan
sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na
nkeyi nacigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan
Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi
wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yamin
wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama
wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin tawa take.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a
cikin alqur'ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka
mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki
bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da
zai dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi
yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta
yadda ba zai hana sallah da azumi ba.
Duk da cewa tsara iyali ya halatta
saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da
maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda
Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali suna birkita
al'ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da
lalurar shan ba, ko kuma aka gane maganin ba ya crycutarwa ta hanyar jarrabawa.
Allah ne mafi sa ni
Amsawa:
DR. Jamilu Yusuf Zarewa
22\1\2016
26. TAMBAYA
WANDA YA TUBA DAGA ZINA SABODA HIV,
ALLAH ZAI AMSHI TUBANSA !
Assalamu Alaikum
Malan, mutumen dayake mazinacine amasa
wa'azi amma yaki yadaina...... Harsai da aka tabbatarmasa dacewa cutar HIV
takamashi sannan ya tuba... To Allah gafarta malan miye matsayin wannan tubar
tasa?
Amsa
Wa alaikum assalam,
In har ya tuba tuba ingantacce, Allah
zai iya amsar tubansa.
Annabi S.a.w. yana cewa: "Allah
yana amsar tuban bawa mutukar bai zo gargarar mutuwa ba", a wani hadisin
kuma yana cewa "Duk wanda ya tuba kafin rana ta fito daga yamma Allah zai
amshi tubansa".
Kasancewar ya samu cutar HIV ya daina
ba zai hana a amshi tubansa ba, tun da akwai wadanda suna da cutar amma suna
yi, tun da cutar ba ta hana jindadin zinar kwata-kwata.
Wanda ya bar zunubi saboda gajiyawa
za'a rubuta masa alhakinsa cikakke, kamar yadda hadisi ingantacce ya nuni zuwa
hakan.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
29/10/2017
27. TAMBAYA
YAWO BABU DAN-KWALI A TSAKAR GIDA ?
Assalamu alaikum, Allah gafarta malam
shin zan iya yawo acikin gida ba dan kwali?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan
tana tsakanin 'yan uwanta mata musulmai saboda al'aurar mace ga 'yar uwarta
mace musulma tana kasancewa ne tsakanin guiwa zuwa cibiya, mutukar akwai mazan
da ba muharramai ba to bai halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al'ura
ce in ban da fuska da tafukan hannu.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
24/1/2016
28. TAMBAYA
YADDA AKE ZAKKAR SHANU?
Assalamu alaikum
Malam. mutum ne yake da shanu guda (168) yaya
zakkarsu za ta kasance ?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To Dan'uwa zakkar shanu, tana da
mutukar sauki, saboda
duk guda talatin za ka fitar da wanda
ya cika
shekara daya, duk kuma guda arba’in za
ka fitar
da wanda ya cika shekaru biyu, kamar
yadda
hakan ya tabbata a hadisin Mu’az wanda
Abu-
dawud ya rawaito a Sunan a hadisi mai
lamba
ta: 1576, kuma Albani ya inganta. Don
haka
kana da zabi ko dai ka bayar da
wadanda suka
cika shekara biyu guda hudu, ko kuma
ka bayar
da wadanda suka cika shekara daya guda
hudu,
da wanda ya cika shekara biyu guda
daya.
Allah ne mafi sani
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
15/12 /2016
29. TAMBAYA
MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN
LOKACINSA, YAYA SALLARTA?
Assalamu alaikum,
Mallam ina hukunchin macen da in
mijinta ya fitine ta da jima'i take shan magani don jini yazo mata, Yaya
hukuncin jinin yaya kuma maganar sallah, ? tunda gayyato jinin ta yi.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To 'yar'uwa Allah da manzonsa sun
rataya hukunce-hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, kamar yadda aya ta : 222 a
suratul-Bakara take nuni zuwa hakan, duk da cewa gayyato shi ta yi saidai zai dauki dukkan Hukunce-hukuncen
haila, mutukar ya zo da siffofinsa.
Gayyato jini saboda hana miji jin dadi bai dace ba, saboda duk dabarar
da za ta kai zuwa haramun to ita ma ta zama sabon Allah, Ya wajaba ga mace ta
baiwa miji kanta duk lokacin da yake bukata, in ba tana da uzurin da sharia ta
yarda da shi ba, don haka bai kamata
mace ta hana mijinta saduwa da ita ba ta hanyar dabara.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
31/10/2015
30. TAMBAYA
SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARIA
?
Assalamu Alaikum
Dr. dafatar ka tashi lafiya Alagafarta
malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan
cewa shima yana haddasa lum'a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za
su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?
Amsa
Wa alaikum assalam,
a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji
ba matsala ba ne ta fuskar Lam'a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa
daga malamai, wannan yasa rashin shafar
ruwan ga hakori daya ba zai yi tasiri ba.
Amma zai iya zama matsala saboda yana
iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko
dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.
Idan ya kasance an yi hauren ne da
zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi S.A.W. ya ce: (An haramta
zinare ga mazajen Al'umata, amma an halatta ga matayansu)
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
1/11/2017
31. TAMBAYA
ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR
AIDS ?
Assalamu alaikum.
Malam matata ta yi rashin lafiya, da
aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce
bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya
malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?
Amsa
Wa alaikum assalamu To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka
sababbi, wadanda ba'a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta
saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma'aurata ko su duka,
za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa
cuta ce mai hadari kuma ana daukarta,
don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fiqhu sun
halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil
Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478 Cutar
Sida kuma tafi kuturta tsanani.
Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta
yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau da kai
daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game,Cigaba da
zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba
za'a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin.
Allah ne mafi sani
Amsawa:
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
30/8/2015
32. TAMBAYA
MAI TAKABA, ZA TA IYA FITA AIKIN
GWAMNATI
Assalamu alaikum malam inada tambaya
mace ce mijnta ya rasu kuma takasance tana aikin gomnati shin zata iya fita a
lokacin da take takaba?
Amsa
Wa'alaiku mussalam
warahmatullah, a zahirin maganar
malamai, mai takaba ba za ta je aikin gwamnati ba, tun da bai halatta mai
takaba ta fita ba sai lokacin tsananin lalura, aikin gwamnati ba ko yaushe zai
zama lalura ba, tun za'a iya ba ta hutu, in har ta nema, in tana da yadda zata
cı abinci ya wajaba ta amshi hutu, ko da babu albashi. Saboda bin sharia shi ne
zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah, to shi ma zai kiyaye shi, duk wanda ya
yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.
Amma idan ta rasa yadda zatayi ta cı
abinci sai ta hanyar aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi
(S.A.W) ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a gidan daya dağa cikinsu
domin hira da debe kewa da rana, lokacin da suka takuru da zaman kadaici, duk
da ya wajabta musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya
rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai takaba fita da rana,
kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata a littafinsa na Mugni 8/130.
Duk da cewa wasu malaman Hadisin sun
raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan
Mas'ud da Abdullahi dan Umar, Allah ya kara musu yarda, maganar Sahabi hujja
ce, in har ba'a samu wani sahabin ya
saba maşa ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fiqh.
ALLAH NE MAFI SANI
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
22/3/2016
33. TAMBAYA
AKWAI GADO GA DAN DA MACE TA SHAYAR DA
IYAYEN SHI ?
Assalamu alaikum malamaina don Allah
ga wata tambaya kamar haka : idan aka haifi yaro sai daga baya aka samu cewa da
babanshi da mamarshi duk mace guda ta shayar dasu to wai wannan yaron yana da
gadansu koko?
Amsa
Wa'alaykumussalam.
A na gado da takaba a auren da a ka gano
rashin ingancinsa, kuma a na danganta yaro ga mahaifinsa. [AL-MUGNY; 8/590]
Wallahu A'alam.
Amsawa:
MALAM: NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)
25/10/2017
34. TAMBAYA
A GUJI MUGUWAR ADDU’A GA IYALAI!
As-salaamu alaykum Malam Allah ya
kara maka imani da fahimta Tambayata
itace
Mahaifinane yake nuna banbanci a
tsakanin mu
sannan yana yawan zagin mahaifiyata
musamman in ‘kanne na sunyi masa laifi
sai ya
kama zaginta Sai na nuna masa rashin
jindadina
da wannan Al’amari har ya kai ga mun
daga ma
juna murya. Karshe sai ya fara yimin
Allah ya
isa yana tsine mun.
Amsa
Wa'alaykumussalam
Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin
‘ya’yansa, Annabi S.a.w. yana cewa : “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a
tsakanin
‘ya’ya yanku” Wannan ya sa lokacin da
Sahabi
Bashir ya yiwa dansa kyauta, ya nemi
Annabi s
a w. ya yi shaida akan haka, ya
tambaye shi :
shin Duka ‘ya’yanka ka yi musu kyauta
? sai ya
ce A’a, sai manzon Allah ya ce : Ba ka
so su
zama daidai wajan yi maka biyayya ? ba
zan yi
shaida akan zalunci ba”. Bukhari da
Muslim sun
rawaito wadannan riwayoyi.
Yin adalci a tsakanin iyalai yana
inganta tarbiyya, yana sanyawa su ji tausayin Uba bayan ya girma,
yana kara musu hadin kai da son juna.
Ya
wajaba mazaje su Sani cewa : zagin
matayansu
ya sabawa ka’idojin sharia, kuma hanya
ce ta
tabarbarewar tarbiyya, domin Yaran za
su rabu
biyu, wasu suna bayan mahaifinsu, wasu
kuma
Babarsu za su ga ta yi daidai. Ya
wajaba a
tausasa harshe lokacin da za’a yi
magana da
mahaifi saboda Allah ya hana fadawa
Uba kalma
mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya
zo a
Suratul Isra’i.
Allah ne mafi sani.
Ba’a son ana
yın muguwar addu’a ga iyalai saboda in
aka
dace da lokacin amsar addu’a za ta
zamar
masa matsala, kamar yadda ya tabbata a
hadisin Muslim mai lamba ta: 3014.
Amsawa:
Dr Jamilu Zarewa
21/12/2016
34. TAMBAYA
BA’A SON DABARA WAJAN FITAR DA ZAKKA!
Assalamu Alaikum
Malam Tambaya ce daga wata ‘yar
uwa kamar haka: “Akwai Marayu a
karkashi
na,kuma dukiyarsu tana tare dani,ina
ririta musu
bana son taba ta,musamman asalin
dukiyar.
Yanzu haka sai iyayena suka nemi na
bawa
daya daga cikin ‘yan uwa rancen kudi
don yaja
Jari. Yanzu haka an fitar da Zakkah
daga kudin
marayun,shine nake so na bashi amma ba
bashi
ba. Sai dai in nace Zakkah ce, to su
iyaye na ba
za su fahimci dole ne ko an sami
hasara dole
ne a fitar da zakkah ba,zasu kara
tattaro
matsaloli suce a bada kudi akansu.
Shin ina iya
bashi kudin ba tare da nace Zakkah
bace,
la’akari da matsalolin da fadar Zakkar
ce zai
jawo min???? Allah ya karawa Malam
ilimi da
ikhlasi.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To ‘yar’uwa Allah madaukaki ya
yi umarni da kiyaye dukiyar maraya, da
kuma
hana cinta, in ba da gwargwadon bukata
ba, ga
wanda yake talaka, kamar yadda ayoyin
farko-
farkon suratunnisa’i suka tabbatar da
hakan. Ba
shi daga cikin sharadin zakka, sai an
sanar da
wanda aka bawa cewa zakka ce, kamar
yadda
Ibnu Khudamah ya yi bayanin hakan a
littafinsa
Al-mugni 2\508 da kuma Annawawy a
littafinsa
Al-majmu’u 6\233, don haka in kika
bawa fakiri
da niyyar kin fitar da zakka ko da ba
ki sanar dashi ba ta yi. Saidai malamai sun hana yin
dabara wajan bada zakka, kamar ya zama
kana
so ka yi ma mutum kyauta, amma
maimakon ka
dauki kudinka ka ba shi sai rowa ta
hana ka, sai
ka yi dabara ka ba shi zakkar da ka yi
niyyar
fitarwa. Duk mutumin da ya bayar da
zakka
yadda Allah ya yi umarni, tabbas Allah
zai
mayar masa da ninkin-ba-ninki.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
21/12/2016
35. TAMBAYA
BAWA MAKUSANTA ZAKKA, A MAIMAKON KYAUTA!
Assalamu Alaikum,
malam yaya matsayin
mutumin da yake baiwa yan uwansa
KYAUTA
duk shekara kafin dukiyarsa ta isa
ZAKKA? Da
dukiyarsa ta isa zakka kuma sai ya
janye
kyautar shekara da yake basu ya fara
basu
ZAKKA? Wannan zakkar ta inganta kuwa?.
Mungode.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To dan’uwa Allah yana kallon
niyyar mutum ne a duk lokacin da ya
aikata aiki,
kamar yadda hakan ya tabbata a
hadisai, don
haka in har ba dabara ya yi nufi a
zakkarsa ba,
to ta yı, mutukar makusantan suna
cikin
wadanda suka cancanci su ci zakka.
Annabi
S.a.w. yana cewa : “Yın sadaka ga
miskini
sadaka ce kawai, amma yin sadaka ga
makusanci, to sadaka ce da zumunci”,
kamar
yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya
kyautata shi
a hadisi mai lamba ta: 658 a
Littafinsa na
Sunan. Niyya ita ce kashin bayan
kowanne aiki,
za ta iya gyara shi, ko ta bata shi ko
ta daidaita shi.
Allah ne mafi Sani
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
21/12/2016
36. TAMBAYA
ADDU'AR ZIYARAR MAKABARTA?
Assalamu alaikum Malam wacce addua'a mamaci yafi bukata ? ko
kuma Idan an ziyarci kabarin sa wacce addu'a za'a masa ?
Amsa
Wa alaikum as salam,
Annabi saw ya shar'anta ziyarar makabarta
saboda tana tuna lahira, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta
: 3237, kuma Albani ya inganta shi.
In mutum ya je kabari an shar'anta ya
fadi wannan adduar :
السلام عليكم أهل الديار من
المؤمنين والمسلمين، وإنا إن شاء
الله للاحقون، أسأل الله لنا ولكم
العافية.
Assalamu alaikum Ahlad diyaar minal
Mu'umineena wal Muslimeena, wa innaa insha Allahu La laahiquuna, as'alullaha
lanaa wa lakumul 'aafiyah, Muslim a hadisi mai lamba ta : 2302.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr.
JAMILU YUSUF ZAREWA
(04/11/2015)
37. TAMBAYA
SIFFOFIN ABOKI NAGARI!
Assslamu alaikum Malam ina da abokai
da yawa, amma ina so ka ba ni shawara?
Amsa
Wa alaikum assalamTo dan'uwa Aboki
yana da mutukar mahimmanci a rayuwar mutum, idan ya zama abokinka mutum ne mai
himma, sai kai ma ka samu himma kamar yadda ake cewa zama da madaukin kanwa
yana kawo farin kai, haka nan idan ya zama mutumin banza sai ya yi maka tasiri,
Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga Annabi ((s.aw.)) yana cewa (misalin
aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai daukar turare ne da mai hura
zuga-zugi, mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa
ko kuma ka ji kamshi mai dadi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona
maka kaya ko ka ji wari a wurinsa) Bukhari ne ya rawaito
Kuma wani malami yana cewa:
• idan ka kasance a cikin mutane, to
ka yi abota da zababbensu, kada ka yi abota da halakakke saiku halaka tare.
• Idan kana so ka san waye mutum, to
ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi .
Wani kuma yana cewa:
• Kar ka aboci malalaci a kowanne
hali, da yawa mutumin kirki yana lalacewa ne idan ya hadu da mara kirki.
• Dakiki yana saurin tasiri akan mai
kokari, ba ka ganin garwashe idan aka saka shi a toka shi ma sai ya zama toka.
Da fatan za ka kula da abin da ya
gabata.
Allah na mafi sani
Amsawa
Dr. JAMILY YUSUF ZAREWA
11/11/2017
38. TAMBAYA
ZAN IYA RANTSUWA DA AL-QUR'ANI?*
Salamun alaikum Dr. Don Allah mene ne
hukuncin rantsuwa da Al-Qur'ani?, kamar ka ce: Alquran.
Allah Ya kara ma Dr. Lafiya Amin.
AMSA
Wa alaukum assalam, Ya halatta mana
tun da qur'ani sifa ne daga cikin sifofin Allah .
Annabi S.A.W. Yana cewa: "Duk
wanda zai yi rantsuwa, to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru" kamar
yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (6270).
Rantsuwa da Allah ya kunshi rantsewa
da daya daga cikin sunayanSa ko daya daga cikin sifofinSa, kamar yadda malamai
suka yi bayani.
kasancewar daga cikin sifofin Allah akwai
zance, kuma Al-Qur'ani maganar Allah ce
ba halittarsa ba, hakan sai ya halatta rantsuwa da shi.
Allah mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
09/11/2017.
39. TAMBAYA
BANA SHA’AWAR MATA SAI MAZA
IRINA,MENENE MAFITA ?
Assalamu Alaikum.
Mallam inada tambaya kuma zan ji
dadi idan za’a iya amsa mun. Mallam
mutun ne
balagagge namiji, tun lokacin da ya
malliki
hankalin shi yasan cewa yana cikin
matsala,
amma ya rasa inda zai danganta
matsalan…sabode ya daure masa kai. Bai
taba
kawo son mace a zuciyan shi ba ko sau
daya,
baya taba sha’awar mace illa namiji
kamar
shi…wannan ba sabode yana kallon batsa
bane
ko kuma yana tare da marasa imanin
mutane
ba…a’a tun yana karami ake fada masa,
cewa
yakan daukan dankwali ya daura,
yanayin sa ma
kamar mace yake yi…muryan shi ma idan
ba
kasan shi sosai ba sai ka dauka mace
ce
magana, abun yana damun sa sosai, ya
kai ga
idan yayi barci yayi mafarki da maza
yake yi
wato saduwa har maniyyi ya fita. Toh
mallam
yanzu ya rasa yadda zai sa
kanshi..wannan
wace irin matsala ce? Kuma wani hanya
za a bi
wajen samun shifa’a?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To dan’uwa tabbas ka hadu da babbar
musiba, sai dai akwai shawarwari da nasihu kamar haka :
1. Ka rinka
yawaita istigfari, saboda yana warware
matsaloli,
sannan sha’awar maza tana kaiwa zuwa
ga
luwadi, Allah ya hallakar da al’uma
kacokan
saboda suna aikata luwadi.
2. Ka dinga yawaita addu’a a lokutan
da ake amsar roko, kamar cikin
sujjada da karshen dare, saboda Allah
zai iya
karbar kukanka, ya kare ka daga wannan
fitinar.
3. Duk lokacin da tunanin namiji ya zo
maka a
zuciya ka yi kokari wajan kautar da
tunanin
zuwa wani abu daban mai amfani.
4.Shagaltuwa da ayyukan alkairi na
taimakawa
wajan kaucewa Alfasha.
5. Tuna azabar Allah da
girmansa, suna taimakawa wajan barin
sabo.
6.Kada ka dinga kwanciya bacci, sai
lokacin da ka
tabbatar kana jin bacci, saboda
tunane-tunane
suna yawan zuwa a wannan lokacin.
7. Nisantar
abokan banza yana gyara halaye.
8. Nisantar
cakuduwa da maza zai taimaka maka
wajan
rashin sanya su a rai.
9. Yawaita karatun
Alqur’ani na nisanta mutum daga
shaidanu,
wadanda suke juya dabi’ar mutum.
10. Zai yi
kyau in yana da hali ya je wajan
kwararrun
llikitoci, saboda za su iya ba shi
gudunmawa.
Tare da cewa akwai mutanen da Allah
yake
halitta suna da siffofin mata saidai
ya wajaba ka
yi iya bakin kokarinka wajan nisantar
kamanceceniya da mata, saboda Annabi
s.a.w.
ya la’anci namijin da yake
kamanceceniya da
mata, a hadisi mai lamba ta :5546 a
Sahihul
Bukhari, sifar da ka yi iya bakin
kokarinka ta ki
canzuwa, to Allah ba ya dorawa rai
sama da
abin da za ta iya, kamar yadda aya ta
karshe a
suratu Bakara take nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
18/12/2016
40. TAMBAYA
NA GA WANDONA A JIKE BAYAN NA KAMMALA
SALLAH?
Aslamualaikum MALAM na tashi da janaba nayi
salar asuba da azahar da kuma laasar, duk nayi sallah sai bayen naje wanka da
yemma naga wando na da alamun manniyi shin ya ingancin sallolina na baya ?
nagode
Amsa
Wa alaikum assalam, mutukar ka
tabbatar a baccin asuba maniyyin ya fito, to ya wajaba ka sake asuba da azahar
da la'asar din.
In har ka yi wani baccin bayan azahar
to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin karshe da ka yi, ta yadda sallar da
ka yi bayan baccin karshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu Malik ya rawaito a
Muwadda daga Sayyady Umar.
Allah ne mafi sani
Amsawa:
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
13/11/2017
No comments:
Post a Comment