1. TAMBAYA
HUKUNCIN DAURA LAYA DA GURU!
Assalam Alaikum.
Malam, menene hukuncin amfani da “LAYA
KO GURU a musulunci?”
Allah yasa mu dace.
Amsa
Wa alaikum assalam,
To dan'uwa Layu da guru sun kasu kashi
biyu:
1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur'ani ba, wannnan malamai sun cimma daidaito game da haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna Adda'imah 2/212 saboda fadin Annabi S.A.W. (LAYU da kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi S.A.W. yake cewa: (Wanda ya rataya laya to ya yi shirka, shima
wannnan hadisin Albani ya inganta shi a Silsila Sahiha.Hadisan da suka gabata suna nuna
haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana
fitar da mutum daga musulunci.
2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani
ko hadisai ingantattu, wadannan na'u'i malamai sun yi sabani akansu:
A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan
Allah da kuma karatun alqur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya
dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga
cikin magabata.
B. Ba su halatta ba saboda Ba'a samu
Annabi S.A.W. ya yi ba, da hakan sharia ne da an gan shi ya yi ko da sau daya
ne a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da Alqur'ani zai jawo a
wulakanta su tun da za'a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bukata,
kiyaye hakan kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin
amfani da Layun da suke daga Alqur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya
ga manzon Allah S.A.W, sannan shariar musulunci ta halatta mana addu'o'i da
yawa na neman kariya wadanda suka wadatar da mu daga layu.
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba: Taisirul
Azizil Hamid shafi na : (136) da kuma Ma'arijul Kabul 2/510
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
4/10/2017
2. TAMBAYA
ABUBUWAN DA YA KAMATA MACE MAI YARON
CIKI TA KULA DA Su!
Assalamu alaikum
Don Allah Malam wata tambaya aka yi
min, shi ne na ke son a taimaka min wajan ba da amsa, tambayar ita ce: me ya
kamata mai yaron ciki ta kula da shi?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To malama akwai abubuwan da ya kamata
mace ta kula da su, lokacin da take da ciki, ga wasu daga ciki :
1. Ki yi kokari, ki dinga cin halal,
saboda lokacin da yaro yake ciki, na daga cikin lokutan da yaro yake ginuwa,
don haka, idan kina cin haramun, yaron zai ginu da ita, sai Allah ya fara
cirewa gabobinsa son alkhairi, tun yana yaro, domin duk jikin da ya ginu da
haramun zai zama mai kasala wajan aikata abin da Allah yake so, kamar yadda
malamai suka yi bayani.
2. Wasu malaman suna cewa : yawan
saduwa yana karfafa yaro a ciki, saboda Annabi s.a.w ya kamanta ciki da shuka,
kamar yadda ya zo a hadisin Abu dawud, mai lamba ta : 1847, kuma shuka tana kara karfi duk lokacin
da aka bata ruwa.
3. Neman masa tsari daga shaidan,
kamar yadda mahaifiyar nana Maryam ta nemarwa 'yarta tsari, lokacin da ta haife
ta.
4. Nisantar duk wani abu da zai cutar
da shi, saboda musulunci ya yi umarni da kula da rai, don haka zai yi kyau a
matsayinki na sabon aure, ki nemi shawarar magabata da kuma likitoci, saboda ki
gujewa abin da zai cutar da yaronki.
5. Zuwa asibiti, lokaci-lokaci don
tabbatar da lafiyar yaron.
ALLAH SHI NE MAFI SANI.
Dr. Jamilu Zarewa
16\6\2014
3. TAMBAYA
NA SAMU RAKA'A BIYU TARE DA LIMAN A
SALLAR ISHA'I, YA ZAN CIKA SALLATA?
Assalamu Alaikum
malam AWAL ga tambayata kamar haka minene
hukuncin wanda yatararda liman Acikin sallar Isha sai yasami raka biyu nakarshe idan zaikawo cikon raka
watarana yakan bayyana karatun fatiha da sura batareda yayi Ba,adiyaba ko
Qabliyya shima yaya hukuncinsa yake?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Wato an samu sabani ne tsakanin
malamai wajen wanda ya samu raka'o'i biyun karshe tare da liman, shin sune na
farkon sa ko kuwa sune na karshen sa shima, wadan da sukace abinda ya samu sune
na farkon sa kaga kenan zai ciko biyun karshe a yadda suke wato fatiha kawai
kuma a asirce, amma wadan da suka ce abinda ya samu sune na karshen sa toh kaga
zai rama biyun da suka wuce shi kenan, a yadda suka wuce shi wato fatiha da
sura kuma a bayyane dukkan ma'abota wadannan maganganun suna da madogara daga
abinda suka fahimta na hadisan manzon Allah, amma abinda yafi rijaye wajen
malamai shine maganar farko wato abinda ya samu sune na farkon sa don haka zai
cika abinda ya rage masa, wato zai karanta fatiha kawai a boye a duk raka'o'in
biyu.
Wannan shiyafi dacewa da fadar manzon
Allah...
ما أدركتم فصلوا وما فاتكم فأتموا...
Duk abinda kuka riska ku sallata kuma
Abinda ya wuce ku sai ku ciko..
Wallahu A'alam.
Amsawar:
Malam NURUDDEEN MUHAMMAD(MUJAHEED)
26/09/2017
4. TAMBAYA
HUKUNCIN YIN AZUMIN TASU'A RANAR
ASABAR
Assalamu alaikoum malam muna so a fidda mu cikin shakku. Manzon Allah SAW ya hana ayi azumin nafila a ranar Asabar toh yaya zamuyi? ayi mana bayyani game da azumin assabar na tasu'a
Za mû yi shi ko kuma tsallakeshi za mû
yi saï mû azumci ranar ashura lahdi?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Babu komai zaku iya yin azumin ku,
hanin dake cikin Hadisin Abdullahi bin Busrin al'maziny na kada ayi azumi ranar
asabar malamai sun kebance shi da halaccin yi saboda hadisai masu yawa daga
cikin su akwai hadisin Abu Huraira wanda ke cikin Bukhari ( kada kuyi azumi
ranar Jumma'a saifa in kun hada da na yinin kafin Jumma'a din (wato alhamis
kenan) ko yinin bayan Jumma'a din (wato asabar kenan)
Da kuma hadisin Juwairiyya, wanda
manzon Allah ya shigo wurin ta ranar Jumma'a sai ya tarar tana azumi sai ya
tambaye ta kinyi na jiya tace a'a sai yace zakiyi na gobe sai tace a'a sai yace
to in haka ne ki karya azumin ki...
Da ire iren wadannan hadisan malamai
suka ce hanin ya shafi kebance ranar asabar din ne ita kadai.
Amma idan za'a hada da wata rana toh
babu laifi,
Imam Ibn Kudaama a cikin littafin sa
Al'mugni yace makaruhi ne kebance ranan asabar da zumi amma in za'a hada da
wata ranar toh babu karhanci.
Wallahu A'alam
Amsawar:
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
26/09/2017
5. TAMBAYA
MIJINTA YA SAKE TA SAI YA RASU BAYAN
SATI 2, YA BATUN TAKABA?
Assalamu alaikum.
Shin idan miji ya saki matarsa sai
bayan mako biyu Allah ya yi masa rasuwa zatayi takaba?
Amsa
Wa'alaykumussalam
Macen da mijinta ya sake ta kafin ta
kammala idda sai mijin ta ya rasu, malamai sunyi maganganu uku:-
(1) ya zamanto sakin akwai kome a
cikin sa wato saki daya ko biyu, toh malamai sunyi ittifaqi zata fita daga idda
ta koma takaba kuma tana da gado, domin mace matukar tana cikin idda bata fita
daga hurumin mijinta ba don haka ma yana da ikon dawo da ita ba tare da andaura
aure ba, don bata halatta ga wani sai bayan idda.
(2) ya zamanto sakin babu kome a cikin
sa kamar saki uku kuma mijin yayi sakin a lokacin yana lafiya lau, toh a wannan
hali ba zata ci gado ba bisa ijma'in malamai sunce domin alaqar dake tsakanin
su ta yanke.
(3) ya zaman toh sakin babu kome a
cikin sa wato saki uku amma a lokacin sakin mijin yana kwance ba lafiya/yana
jinya (ciwon ajali) ya zamanto nufin mijin shine haramta wa matar cin gado toh
a irin wannan matsalar malamai sunyi sabani:
* Mazhabar imam A shafi'i sunce ba
tada gado / ba zatayi takaba ba.
* Mazhabar Abu hanifa sunce tana da
gado/takaba matukar tana cikin idda hakan ta faru.
* Mazhab na Imam Ahmad bin hambal suce
za taci gado/takaba matukar ba ta auri wani mijin na daban bane.
Aduba littafin (Al'mugni 9/194-196)
Da yawa daga cikin malaman wannan
zamann sun tafi akan ra'ayin mazhabar iman Ahmad kamar irin su Sheikh Bin Bazz
da Sheikh Ibn Usaimeen da Sheikh Swaleh fauzan da sauran su...
A duba ( Fawa'idul Jaleelah Fil
mabaahithul Fadiyya na Sheikh bin bazz Shafi na 6) da (tahkikatul Fardiyya Fi
mabaahithul fardiyya na Sheikh swaleh fauzan shafi na 33- 36).
Wallahu A'alam
Amsawa:
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
28/09/2017
6. TAMBAYA
ZAN IYA HALARTAR DAURIN AURAN CRISTER?
Assalamu Alaikum, mutum musulmi zai
iya shiga chikin church domin halartar aure na aboki ko abokiyar karatun sa?
Amsa
Wa alaikum assalam
Yawanci auran Crista a wannan zamanin
ba ya rabuwa da kade-kade da raye-raye, da roko da Neman albarka a wajan Jesus
a matsayinsa na Allah a Wajansu, da Addu'o'i Wadanda suka sabawa koyarwar
addininmu.
Wannan ya sa barin halartar ya fi
dacewa da sharia.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
05/10/2017
7. TAMBAYA
JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA
KAI WATA HUDU?
Assalamu Alaikum Dr. dan Allah inada
tambaya akan matar da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata
daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu yakan iya dawowa ko bayan
wasu awoye shin ya hukuncin sallar ta? xata jinkirta sallah sai jinin ya dauke
ko xata rika yin wanka duk sanda ya dauke tayi rankon sallolin baya ne.
Nagode
Amsa:
Wa alaikum assalam To 'yar'uwa mutukar
cikin ya kai wata hudu kuma jinin da yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to
ya zama jinin biki, kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to
mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama haila, tun da a
zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.
In ya fita daga wadannan biyun zai
zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake
fita, za ki iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallaolin da
aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki, babu
kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi
bayanin haka.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa
Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA
03/02/2016
8. TAMBAYA
NAWA NE ZAKKAR MILIYAN DAYA?
Assalamu Alaikum
Tambaya daga jahar Taraba Suna so Dr ya amsa
musu a wannan zaure mai albarka.
Wata ce take da Miliyan daya tana so
tafir da zakka nawa ne ya kamata ta fitar dashi?
Allah ya tsare mana Dr ya yi mashi
sakamako da gidan aljannah fiddaus.
AMSA
Wa alaikum assalam,
Idan ta mallaki miliyan daya (1,00000), kuma
su ka yi shekara daya a wajanta, to za ta fitar da dubu ashirin da biyar
(25,000), wato daya cikin arba'in din abin da ya mallaka.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
10/10/2017.
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
9. TAMBAYA
TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA !
Assalamu alaikum, Mallam Na kasance
ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin
mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba
matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga
cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin
musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila,
ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana
likitanci suna bada shawarar cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a
tsotsa, saboda neman kariya
Allah madaukakin sarki a cikin suratul
Bakara aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna
dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura
wacce nassi ya togace.
Allah ne mafi sani.
Duba : Mawahibul-jalil sharhin
Muktasarul Khalil 3\406,
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
20/12/2014
10. TAMBAYA
IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR
BAKWAI, MENENE MAFITA?
Assalamu alaikum.
yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala
ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata
hudu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi?
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi
cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu
malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin
bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.
Duk wanda bai samu damar yiwa dansa
Akika ba a kwanakin da aka ambata a sama, to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi duk lokacin da ya samu dama.
AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya
yiwa dansa a lokacin da Annabi S. a. w
ya ambata, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba: Daka'iku
Ulin Nuha 1/615.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/08/2017
11. TAMBAYA
YA KAI WANI GIDAN BOKA BAI SANI BA ?
Assalamu Alaikum
Dr, nine wani ya faka a motor dinshi
sai ya tambaye ne shin nasan gdan wani mutumi sai nayi mishi kwatance sai daga
baya natuna gdan boka zaije
Amma sai daga baya natuna meye hukunci
wanda ya bada amsa ne?
Allah ya sakawa malan da gdan aljannah
fiddausi
Amsa
Wa alaikum assalam,
Mutukar ba da saninsa ba ya nuna masa, Allah
ba zai kama shi da laifin hakan ba, saboda Allah ya yiwa al'umar Annabi
Muhammad S.a.w. afuwa cikin abin da suka aikata da kuskure ko mantuwa kamar
yadda ayar karshe a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr. Jamilu Zarewa
11/10/2017
12. TAMBAYA
YA SAUKE AL-QUR'ANI, BAI SAN FASSARAR
SHI BA , YA YI LAIFI?
Assalamu alaikum. Malam ina da tambaya
na sauke Qurani amman ban san fassaransa ba, kuma ina yawan tulawa. To ya
matsayin karatunnawa ?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To 'yar'uwa karatunki ya yi, mutukar
kina yinsa ta tajwidi, ba wajibi ba ne sai kin hada haddar qur'ani da sanin fassarar
shi, domin akwai daga cikin sahabbai wadanda fassarar wasu daga cikin ayoyin da
suka haddace ta shigewa duhu, amma in hakan ta samu zai fi kyau, saboda hakan
ita ce hanyar wasu daga cikin sahabban Annabi s.a.w, An rawaito wasu daga cikin
magabata sun haddace qur'ani tun suna shekaru bakwai da haihuwa, zai yi wuya
ace hade da fassarar suka haddace a irin wannan shekarun.
Sayyadina Umar ya karanta Aya a
suratul A'amah a cikin hudubarsa an tambaye shi fassararta bai sani ba, hakan
sai ya nuna yin hakan ba wajibi ba ne, amma kuma shi ne ya fi.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
13\10\2015
13. TAMBAYA
MAHAIFIYATA TA RASU ANA BIN TA AZUMI!
Assalamu alaikum malam dan Allah ina
da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah,
rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah
yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya
saka da hairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To malam mutukar rashin lafiyar ta
zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba
sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki
: "Kuma duk wanda yake mara
lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta : 185,
wato bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka
ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama
ba, don haka sai ya saraya akan shi . .
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata,
saboda fadin Annabi s.a.w. : "Duk
wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa" .
kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1851.
Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta :
247.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamil Zarewa
1/11/2014
14. TAMBAYA
HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA DON
GIRMAMAWA
Assalamau alaikum Malam. Ina teaching
practice ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa damin gaishe ni, mal.
na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai
malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai kuma wadanda
suka haramta, akwai wadanda kuma suka halatta.
Saidai maganar da ta fi ita ce bai
hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. " Duk
wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta" kamar
yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755,
Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahihah lamba ta : 5957.
Amma idan aka mikewa malami ba tare da
ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi,
domin ya zo a hadisi cewa : Annabi s.a.w. ya nemi mutanen Madina su mikewa Sa'ad, lokacin da ya gabato" kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai
lamba ta :2878, wannan sai yake nuna halaccin mikewa ga mutane masu falala
kamar malamai da manyan mutane, lokacin da suka gabato .
Don neman karin bayani, duba : Alminhaj na
Nawawy 12/440, da Mirkataul mafaatiih sharhu mishkatil-masaabiih shafi na :
2972 BABU ALKIYAM . .
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
24\11\2014
15. TAMBAYA
FATAWAR NAN AKWAI GYARA!
Malam fatawarka da ka yi akan mijin da
matarsa ta neme shi da jima'i, bai amsa mata ba, ba shi da laifi, mun watsa ta
a group da yawa, kuma ta hadu da kalubale, ga abin da wata take cewa :
Nake ganin idan har aka ce namiji
kawai ne zai iya kusantar matarsa duk lokacin da ya so ko tana so ko ba ta so,
ita mace idan ta nemi hakan ko bai biya ma ta buqatarta ba sai lokacin da ya
so,Anya akwai adalci a hakan.!???., Idan akwai istidlali naqli a taimakamin da
su ba aqali ba. Na ga istidlal din na aqali aka kawo a rubutun.Ya za'ayi mace
ta nemi mijinta ya qi amince ma ta, duk da kasancewar mace tana da kunya. Amma
har ta iya nemansa ka ga kuwa akwai dalilin da ya sa ta neme shi. Ai shi ma
namiji ko da bai da sha'awa da an taba shi sha'awarshi za ta motsa.Kenan hakan
ba zai zamo dalili da zai sa don mace ta nemi mijinta ba ya ki amincewa da
dalilin wai baya da sha'awa.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To abin da zan iya cewa shi ne:
saduwar da muke magana akanta ibada ce, ibada kuma tana bukatar dalili kafin a
tabbatar da ita, babu wani dalili Wanda ya wajabtawa miji amsa kiran matarsa
duk lokacin da ta neme shi, sannan yanayi da al'ada ya tabbatar da cewa namiji
ba zai iya saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, saboda Namiji yana
bukatar nashadi kafin saduwa, sabanin mace, wacce take a matsayin katifa,
wannan yasa malamai da yawa na sharia suka tafi akan cewa ba'a yiwa namiji
fyade, tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba, mace kuwa an
cimma daidaito za'a iya mata fyade saboda kamar tirmi take, in har an samu
tabarya shike nan, wannan yasa za'a iya saduwa da mace tana bacci sabanin
namiji.
Kasancewar an ce babu la'anta akansa
idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake
da nishadi.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
14/10/2015
16. TAMBAYA
YAUSHE ZA KA IYA ZAMA MUFTY?
Imamu Ahmad yana cewa bai kamata mutum
ya zama mai fatawa ba, har sai an samu siffofi guda biyar tare da shi :
1. Ya zama mai tsarkakakkiyar niyya,
domin in ba shi da tsarkakakkiyar niyya to ba za'a samu haske a tare da shi ba,
kamar yadda ba za'a ga haske a zancensa ba.
2. Ya zama yana da ilimi da juriya da
nutsuwa.
3. Ya zama ya san abin da zai yi
fatawa akai yadda ya kamata.
4. Ya zama yana da rufin asiri, in ba
haka ba mutane za su taune shi.
5. Ya zama ya san mutane yadda ya
kamata.
Ibnul kayyim yana cewa : wannan yana
nuni zuwa girman Imamu Ahmad, da kuma matsayinsa wajan ilimi, saboda wadannan
abubuwan guda biyar su ne turakun fatawa, duk abin da ya samu nakasu a cikinsu
to hakan zai haifar da nakasu a fatawa.
Dr. Jamiilu Zarewa
16/10/2012
17. TAMBAYA
ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE,
YAYA BATUN GADO DA TAKABA ?
Assalam Alaikum, Dr. an daura auren
wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon
rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi?
Amsa
Wa'alaykumussalam
To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an
daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba,
kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi S.a.w. ya yi hukunci da hakan
ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai
lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
1/05/2016
18. TAMBAYA
NA TSINCI NAIRA #5,00 , KO ZAN IYA
AMFANIDA ITA BA TARE DA CIGIYA BA ?*
Assalamu alaikum, malam wani bawan
Allah ne ya tsinci Naira: #500#, a wurin
kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya
ba… Ya
ya kamata yayi da kudin tsintuwar ?,
suna ajiye
yanzu haka kusan wata daya.
Amsa
Wa'alaykumussalam
To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa
ya wajaba
a gare shi ya yi cigiya har tsawon
shekara guda,
idan bai samu mai ita ba, daga nan zai
iya
amfani da ita, amma in mai ita ya zo
daga baya
zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya
rawaito a
hadisi mai lamba ta: 5761. Amma idan
abinda
ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa,
to ya
halatta ya yi amfani da shi ko da bai
yi cigiya
ba, saboda abin da aka rawaito cewa :
Annabi
s.a.w. ya ga wani dabino akan hanya,
sai ya ce:
In ban da ına tsoron na sadaka ne da
na ci.
Muslim ya rawaito a lamba ta:2527, sai
hadişin
ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar
cigiya.
Malamai şun yi sabani wajan iyakance
tsintuwar
da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce
za’a koma
al’adar mutane, duk abin da mutane
şuke
ganinsa ba a bakin komai ba, to in an
tsince shi
ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya
hakaito
daga Imamu Malik cewa: bai wajaba
mutum ya
yi cigiyar abin da bai Kai a yanke
hannu saboda
shi ba, wato daya bisa hudun dinari,
haka nan
sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya
ya yi
amfani da ita ba tare da yayi cigiya
ba. Abin da
ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba
ka
samu mai Naira (5,00) din da ka tsinta
ba a
kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani
da ita ba
tare da cigiya ba, tun ba kudi ne mai
yawa ba,
kuma mai ita ba zai kwallafa rai
Akanta ba.
Don neman karin bayani duba : Al-mugni
6/351.
Allah ne mafi Sani
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa
16/12/2016
19. TAMBAYA
DUK MINTI BIYU SAI NA YI TUSA, YAYA
SALLATA ?
AsSalamun'alaikum.
Malam Wai akwai sallah ga wanda in
yana sallah sai ya fitar da iskar tusa kuma duk sallah yake hakan koda ace yayi
kashi kafin yayi sallahr,amma inhar yazo sallah saita futo koda ace zayyi
alwala sama da 10,
Amsa
Wa alaikum assalam,
Akwai sallah akan shi, ba za ta taba
faduwa ba akansa, ya wajaba a gare shi ya yi alwala yayin kowacce sallah, dağa
nan duk abin da ya fito yana sallah ba zai cutar da shi ba, tun da in aka ce ya
sake alwala yayin fitowar kowacce tusa ba zai iya ba, zai kuma shiga cikin
wahala, Sharia ba ta dorawa rai sai abin da za ta iya, kamar yadda ayoyi da
hadisai da yawa suka tabbatar da haka. Babu takurawa da kunci a cikin Addinin
musulunci kamar yadda ayar karshe a suratul Hajji ta tabbatar da hakan.
Don neman Karin bayani duba:
Alfawakihuddawany na Annafraawy 1\340.
Amma idan tusar ba'a mafi yawan lokuta
take fitowa ba ya wajaba ya sake alwala duk sanda ta fito, saboda sallah ba ta
ingantuwa saida alwala.
Kula da wasuwasin abu ne mai
muhimmancin gaske, saboda da yawa Shaidan yake busa a duburar dan'adam amma ba
tusa ba ce, wanda ya ji haka, to kar ya fita daga sallarsa, har sai ya ji iska
ko kara ta fita, kamar yada hadisin Bukhari ya tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
24\04/2016
20. TAMBAYA
MIJINA YANA CHARTING DA TSOHUWAR
BUDUWARSA, BAYAN TA YI AURE
Assalamu alaikum.
Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat da
wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya sama da shekara 20 da wani
abu ta yi aure, suna turawa juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata na yi masa?
Sabo da kubutar da su ga fada wa
halaka.
Allah ya taimaki mallam ya kara
fahimta.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ki yi masa nasiha da tsoran Allah,
sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so ayi irin wannan mua'malar da ita ba.
Yin charting irin wannan da matar aure
yana iya kaiwa zuwa zina, musamman da alama har yanzu kuna son juna, Allah ya
hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra'a'i.
Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi
kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai.
Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi,
wanda ya saba masa zai hadu da Shi a madakata.
Dayanku ba zai yi cikakken imani ba
har sai ya sowa dan'uwansa abin da yake soma kansa.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
DR.Jamilu Yusuf Zarewa
No comments:
Post a Comment