GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Sunday, 4 September 2022

TAMBAYA TA DARI UKU DA ASHRIN DA DAYA (321) ZUWA TA DARI UKU DA ARBA'IN (340)

321. TAMBAYA

MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?

 

Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka. Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid?

 

Amsa

Wa alaikum assalam,

 Bai  halatta ga mai takaba ba ta  fita zuwa Idi, saboda Hadisin  Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031)  inda Annabi SAW yake cewa da  Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna a cikin  gidan da  kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki kammala iddarki"

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba

Sunday, 24 July 2022

TAMBAYA TA DARI UKU DA DAYA (301) ZUWA TA DARI UKU DA ASHIRIN (320)

 301. TAMBAYA


 AZUMI NAWA AKE YI A WATAN MUHARRAM?


Assalamu Alaikum Malam Don Allah malam azumi nawa akeyi a wannan watan ?


Amsa

Wa Alaikum Assalam To 'yar'uwa ana so mutum ya zage dantse wajan yin Azumi a wannan watan, saboda fadin Annabi (SAW) : "Mafificin Azumi bayan Ramadhana shi ne Azumi  a watan Muharram" kamar yadda Muslim ya rawaito.

Amma Wanda ya fi muhimmanci shi ne na ranar goma ga wata, sai kuma na ranar tara, Annabi S.A.W yana cewa: "Azumin ranar goma ga wata yana kankakare zunubin shekara daya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1162), sannan yana cewa: "Idan na rayu zuwa badi zan azumci ranar ranar tara ga MUHARRAM".

 Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA


31/08/2019.



302. TAMBAYA

TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE ?

 

Assalamu alaikum malam Mace taba da jikinta ga mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa.

 

Amsa :

Wa alaikum assalam

To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game

Saturday, 23 July 2022

TAMBAYA TA DARI BIYU DA TAMANIN DA DAYA (281) ZUWA TA DARI UKU (300)

 

281. TAMBAYA

WANDA YA SAKI MATARSA A ZUCI BA TA SAKU  BA!

Assalamu Alaikum,

Don Allah Malam, idan mutum da dare ya qudurta zai saki matarsa zuwa safe, amma bai furta ba zuwa safiyar kuma sai ya canza shawara. Shin yaya matsayin auren yake?

Allah Ya taimaka.

AMSA:

Wa alaikumus assalam, Mutukar bai furta ba kuma bai rubuta ba to Ba ta saku ba, saboda Allah ba Ya kama Al'ummar Annabi Muhammad S. A. W.  da zancen zuci kamar yadda hadisi ingantacce ya tabbatar.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

01/08/2017.

 

282. TAMBAYA

WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI, BAI TUBA BA?

 

Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah mene ne Hukuncin Mai shan taba (sigari), har ya