GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.TAMBAYADAAMSA.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA FATAWOHI DA AMSOSHIN SU WADAN DA AKA YIWA WASU DAGA CIKIN MALAMAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{tambayadaamsa@gmail.com]

Monday, 23 December 2013

TAMBAYA TA DARI BIYU DA SITTIN DA DAYA (261) ZUWA TA DARI BIYU DA TAMANIN (280)

261. TAMBAYA

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA Mijina  BA LAFIYA?

 

Assalamu Alaikum, Dr macece mijinta

ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya

zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani

dogon tunani na sha’awaba, ya matsayin

ibadarta yake ?

Amsa

Wa'alaikumus salam.

To gaskiya abin da yake dai-dai shi ne :

 ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, kadange ma’aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar. Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa

ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin ? ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

21/12/2016

 

262. TAMBAYA

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA Mijina  BA LAFIYA?

 

Assalamu Alaikum, Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana